Sashe 34
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata rana tanata shawaginta aduniyar bil adama tazo dede anguwar pantami kawai Allah ya nuna mata hairah da ta fito a firgice ko takalmi babu a kafanta tana rike da wata tsohuwar naira ashirin (20 naira) ta tsaya abakin kofar wani karamin chemist ta ce abata paracetamol mugun kaman da sukeyi ne yaba khairaty mamaki dayasa seda tasa hannunta ta shafa nata fuskan , karban maganin hairah tayi tashiga yar karamar gidansu da ginin yafara daddarewa , bakin randar kasa taje tadibi ruwa a kofi tashige daki bin bayanta khairaty tayi domin ganin ina zataje , acikin dakin kuwa tasamu hairah zaune da wani kyakyawan yayanta da suke matsanancin kama . barewa hafiz maganin tayi tabashi hade da ruwa ya karba yasha yakwanta ta lulubeshi da tsohuwar bargo da taji jiki, wani tunani ne yafado ran khairaty yasa taje tadaura hannunta akan goshin hafiz nan take jikinshi yayi zafi yafara rawan sanyi tsorata hairah tayi nan take tafashe da kuka tafita a gidan da gudu inda tasan zata samu me gidan hafiz da yake hayan bairon dayakeyin dako tayi , aikuwa tayi saa ta sameshi a bakin kasuwar waya ta badaru , suna zaune acikin majalisa tazo tana kuka take fadamishi yayanta ba lafiya yataimaka ya kaishi asibiti, me gidan hafiz kuwa ganin idon mutane akanshi ne kowa najiran yaji mezece yasa badan, yayi niya ba yace muje gidan naku , ya tari napep suka shiga gidan aka dauki hafiz zuwa asibitin medical center zuwansu yayi dede da kawo ya usman da akayi yana aman jini , gado akabawa hafiz aka rubuta musu magani na kusan dubu bakwai me gidan yatafi da sunan siyan maganin daga nan ya gudu, har gari ya waye babu wani likitan dayazo kan hafiz da sunan dubashi hakan yasa hairah fitowa tana kuka ga tashin hankali ga yunwa , office din likita take nema , shafe duk wasu kofofi khairaty tayi yarage hairah kofa daya kawai tagani inda ya usman yake kwance kenan , tashiga dakin domin yin magana da likita anan ne ya usman yaganta dakowa dake wajan . Hakan yasanya khairaty farin ciki sosai saboda bataso ace saboda ita wani ya cutu nan take ta bace. Wannan kenan.
9:40pm hafiz suka dawo gida bayan driver yayi packing yafita yana kokarin shiga part dinsu kawai ya hango matashin saurayi sanye da fararen kaya har daukan ido sukeyi yana tsaye daga dan nesa yana kallonshi , mamakine yakama hafiz yafara tunanin dama bayansu ya fawwaz da ya areef akwai wani na miji agidan ne betaba ganinshi ba kuwa , ko ajikinshi yakarasa inda fatalwar Mansoor yake tsaye yana kallonshi, mika mishi hannu yayi dan suyi musabaha, girgiza kai fatalwar Mansoor yayi ya ce " ni bakamar kowa bane hafiz ! nasan bakasanni ba sunana Mansoor yaron mommy kuma nima ada ni kanin su ya azaad ne " wasu maganganu dayakeyi ne ya daurewa hafiz kai dan maganar abaibai yayisu yakasa fahimta ya ce " ban gane me kake nufi da kai kanin su ya azaad bane ada ? to ayanzu kenan kai ba kanin su bane ? amma meyasa to? sannan ya akayi kasan sunana dan ni nasan bamu taba haduwa ba ? " ya jero mishi tambayoyi atare , girgiza kai kawai fatalwar yayi ya ce" bazaka gane ba hafiz se anjuma kacewa kowa ina gaishesu inka shiga ciki " yagama magana yajuya yafara tafiya , hafiz afili ya ce " to ai hikenan" yashiga falo duk suna zaune abinsu harta ummi da Mr azaad fanan ce kawai bata falon taje dakin ummi neman dabino, zama shima yayi kusa da areef ya gaishesu ummi ta ce " hafiz harka dawo kenan ni na daukama ai tare kuka tafi da areef ashe yana nan shi " ya ce " eh ummi nadawo ! nace mai ai yazo mutafi yacemin shi tsoron rigimar auta yakeyi yasa ya ki bina dan yasan haduwarsu " dariya ummi da zeenat da fawwaz sukayi zeenat ta ce " lallai ya areef wato kai karasa ma wacce zaka tsokano se auta rigima " nanma dariya sukayi , hafiz ya ce " ummi dazan shigo na hadu da wani wai yacemin sunanshi Mansoor sannan Kuma yacemin in gaisheku sosai , ashe shima kanin su ya fawwaz ne " duk dagowa sukayi har suna rige_rige wajan kallon hafiz dake magana yasa lamarin basu mamaki da daure musu kai dan kuwa sunsan de tabbas hafiz be san Mansoor ba balle yayi irin wannan maganar, jikin areef ne yadauki rawa ya mike yana kallon fawwaz ya ce " fawwaz bana fada maka ba wallahi Mansoor na gani dazun amma kacemin sam bashi bane to gashi hafiz ma yaganshi " riko areef Mr azaad yayi ya ce " calm down areef " zama sukayi amma har lokacin jikin areef be bar kerma dayakeyi ba. shiko hafiz mamaki ne yakamashi ganin yanda firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu lokaci daya dan kawai ya fada musu yanda sukayi shida Mansoor din . Mr azaad ne yakalli hafiz ya ce " hafiz aina ka kalli shi Mansoor din ?" fada mishi hafiz yayi sannan Mr azaad yasake maida kallonshi kan areef ya ce " ka kwantar da hankalinka kafadamin aina kaga Mansoor din ?" duk abinda yafaru a garden din areef ya fada mishi sannan yakara da " yayi tamin magana wanda nakasa gane me yake nufi amma naji yafadi wata kalma 'ku kare kanku daga sharrinta ' wannan kalmar ce kawai zan iyacewa naji "
zeenat kam uwar tsoro tunda taji aka ambaci sunan mansoor ta kankame fawwaz kam ta ki sakinshi. girgiza kai ummi tayi ta ce " karku daga hankulanku akan wannan mansoor yariga da ya mutu kawai sharrin shedanu ne da jinnu amma kun tabajin wanda ya mutu ya dawo ne " zaro ido hafiz yayi shima lokaci daya jikinshi yafara rawa jin wai Mansoor din da ya hadu dashi har sukayi magana wai matacce ne ya rigada ya mutu babban tashin hankalinshi shine inya tuna yar maganar da sukayi na wasu yan mintuna , da mugun karfi zuciyarshi yake bugawa sakamakon jin maganar yayi kamar saukar aradu hakan yasa yadafe kirjinshi da karfi sauka yayi akan kujera yaduqa kasa yana rike da setin zuciyarshi dagashi Mr azaad yayi yadan rungumeshi dan dama yasan hakan seya faru muddin hafiz yaji dan bakowane yake da wannan karfin guiwan tunkarar magana makamancin wannan ba ace kayi magana da wanda yarigada ya mutu baka sani ba daga baya inkaji hakan dole hankalinka yatashi , kokarin zaunar da hafiz Mr azaad yakeyi yaji yakara nauyi nan yagane suma yayi yasa ya kwantar dashi akan kujeran dauko ruwa fawwaz yayi yamikawa Mr azaad ya yayyafawa hafiz shuru be farfado ba , zama ummi tayi kusa dasu ta daura kan hafiz akan cinyar ta tarike hannunshi tana murzawa da dan karfi ko hakan ze temaka duk suna tsaye akanshi , saukowa fanan tayi tana murna tasamo dabinon dataje nema, ta samesu duk sunyi cirko_cirko sannan ga hafiz dake kwance dasauri takaraso falon , tambayar fawwaz tayi meyasa meshi karya yamata yafada mata kancewa sunga yarike kirjinshi ne daga bisani kuma yasuma zama tayi agefen kujeran ta rike hannunshi dede wajan pause dinshi taji yana harbawa da wuri tasake sa hannunta akan kirjinshi nan taji wani irin lugude da zuciyarsa yakeyi hakan ne ya tabbatar mata da tabbas wani abune yagani ya razanashi ko kuma wani abun yaji daya firgitashi kallon ummi tayi ta ce " yadan shigo yar doguwar suma amma zuwa nan da 4hours ze iya farfadowa amma kuma in muka bari ya farfado ahaka tabbas akwai matsala , ze iya samun matsalar brain kokuma yashiga firgici har nan da sati daya " tagama musu bayani tana karasawa kan center table tadauki pen and paper data gani ta rubuta allurai da magunguna ta mikawa fawwaz karba yayi yafice dasauri dukda darene zeyi wuya susamu pharmacy abude sede yadangana asibiti, duk suna zaune fanan ta kalli Mr azaad ta ce " Mr azaad meyasa meshi " bayason yafada mata yasa kawai ya ce mata " baby we don't know kawai ganinshi mukayi ahaka yarike kirjinshi" ta ce " Allah sarki inna mishi alluran nan in sha Allah zeji dama dama dan zesamu baccin 12 to 14 hours kuma baze tashi da wannan firgicin ba " jinjina kai yayi ummi ta ce "zeenat tashi kije ki kwanta dare yayi ko " make kafada tayi alamar ah ah dan duk atsorace take bazata iya kwana ita kadai ba , taso basu dariya areef kuwa shuru yayi yana binsu da ido , haka fawwaz ya dawo da allurai da magunguna , allurai fanan tayi mishi sannan Mr azaad yadaukeshi cak kamar wani yaro karami yayi part din su fawwaz dashi yakaishi dakinshi yakwantar dashi hade da rufeshi da blanket sukafito . Ummi tabasu umarni da kowa yaje ya kwanta haka suka shige part dinsu , Mr azaad maganar mansoor ya tsaya mishi arai amma zesan yanda ze bullowa lamarin .
Duk wannan wainar da ake toyawa mommy bata da masaniya akai tana nan tana neman hanyar da zata kashe kaf yan gidan hatta yayanta suma seta kashesu bazata bar kowa ba dan dukkansu ta tsanesu mansoor ne kadai takeso shikuma yarigada ya mutu, tamafi tsanan anty shayida shisa aduk sanda anty shayida tasamu karamin ciki , tunkafin sunsan da cikin mommy take cinye dan tun a mahaifa, kusan sau takwas anty shayida nasamun ciki mommy tana cinyewa tunkafin yazama hallita take cinyewa. Haka tasoyiwa anty zainab amma dake mijinta atsaye yake gashi babban dan siyasa kuma malami.
Bauchi state
Fitowa suhaima tayi daga bedroom dinta tana rike da waya tana video call da fawwaz har karfe 11:30 nadare ta farajin yunwa tafito tashiga kitchen din ta ajiye wayar yanda yana kallonta ta daura indomie akan wuta yadafu taje falo tazauna tanaci fawwaz ya ce " ba bismillah kenan? " Yar dariya suhaima tayi ta ce " hubby tom ai kona maka bismillah bazeyu kaci ba sede inci mana ka ji " tafada tana ci gaba da cin indomie fawwaz ya ce " to babynah kici mana din " haka suka dinga hira kafin ya kashe kiran dan dare yayi suka sauka a online din .