← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 66

Sashe 36

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

barin part din Mr azaad yayi yasa securities su tsaya akanta kar subarta tayi koda motsine dukda adaure take
. yakoma garden yazauna yana kada kafa har asuba , yayi alwala duk a garden din yanufi hanyar fita a gidan dan zuwa masallaci yaga su fawwaz da areef sunfito su ma. jerawa sukayi sukaje suka gabatar da sallah suka dawo be fadawa kowa abinda ke faruwa ba haka zalika be fada musu abba yataso ba yawuce part dinshi samun fanan yayi tana zaune tana azkar zama yayi akan kujera yana facing dinta harta idar ya ce " morning wifey" ta ce " habiby katashi lafiya ?" ya lumshe idanu kawai. ta ce " habiby ina kaje daren jiya natashi naga baka nan amma naganka amarfakina a part din mommy" " eh naje part dinta ne " daga haka yakawar da zancen ta hanyan dauko wata maganar daban ya ce " gobe zamu tafi yau zankaiki kije kiyiwa su mama sallama yau " cike da murna taji zataje gida ya ce " to Allah yakaimu" bata koma bacci ba ta cire babban hijab din jikinta yarage daga ita se wandon falazo da vest ajikinta tafara gyaran part dinsu tayata shima yayi suka gama , atare suka shiga kitchen sukayi breakfast dan wake tamusu tunda tafara kwaba dan waken da digawa Mr azaad yaketa yamutsa fuska yana " nide bazanci wannan abun ba abu kamar wani kwallo_kwallo " dariya tayi tasan be taba ci ba gashi itakuma shi takeson ci yau din nan gama danwaken tayi ta dafa kwai ta baresu sannan tayanka vegetables salad , tomato, ta yanyanka kwai din a bowl daban taki saka albasa aciki saboda yanzu seyasa bakin mutum yafara warin albasa, plate ta dauko tazuba danwaken dayawa sannan tasaka mai din data soya yaji albasa ta zambada yaji zaro ido waje Mr azaad yayi ya ce " yanzu da wannan pepper zakici baby" murmushi tayi ta ce " kadingayin jam'i zamuci zakace yau zan koya maka yanda akecin danwake" haka taci gaba da saka salad da tomato din da ta yanka tasa kwai din. ( bakaramin daukan hankalina danwaken nan yayi ba lokaci daya naji yawuna ya tsinke, kunsan ni , akwai ni akwai kaunar dan wake sosai. gashi ban Isa ince zanci ba yanzu se Mr azaad yayi kasa_kasa dani ) haka ta dauko plate din taje tsakiyar falo ta ajiyeshi akan carpet takoma taje tadauko bottle water da glass cup ta ajiye ta zauna zama shima yayi dan yaga yau tayi niyar kumburar mishi da ciki ne . sa hannunta tayi tafaraci tana santi babu yanda ya iya haka shima yasa hannu yayi yanda tayi yakai baki, ai ba arziki yafurzar dashi waje idonshi harseda ya kadà murya na rawa ya ce " is to spicy kiban ruwa " zuba ruwa tayi a glass cup ta mika mishi yasha yanata shishitan yaji, sannu tamishi sannan tasa hannu dede ta gabanshi ta kwashe yajin yarage dan kadan takara maggi ta gauraya mishi ta ce " to nacire yajin kaci ka ji " make kafada yayi kamar yanda take mishi a shagwabe ya ce " nide bazan iya cin wannan abun ba is to spicy" dariya tayi ganin yanda yake mata shagwaba hakan ya kayatar . diba tayi ta bashi abaki dakyar ya iya cinyewa dukda babu yajin sosai wannan karan, haka suka cinye danwaken tas daga ya ce yakoshi setace ah ah yakara kadan de haka ta mishi wayo tadinga feeding dinshi harsuka cinye ,sunaci suna shishitan yaji kamar wayanda akama dole, sukasha ruwa hancinshi har wani ja yayi dan wahala gaba daya yazama wani kala dukda yaji dadin danwaken amma ya ji ya azabtar dashi .

Karfe 10:00am dede abba yashigo gombe yasauka agida part dinshi yayi , wanka yayi ya kimtsa babu wanda yasan da zuwanshi saboda babu wanda yasani se Mr azaad . Kiran yayanshi yayi awaya yasanar musu yanason ganinsu yanzu yanzu batare da bata lokaci ba , wannan kiran gaggawan da abba yamusu ya tayar musu da hankali yasa babu wacce tabata lokaci kowa suka hallara a main falo harta su Mr azaad da fanan duk babu wanda bezo ba duk suna zaune ,m afalo sukaji sallamarshi , zama yayi akan kujera fuska babu yabo ba fallasa. shan jinin jikinsu sukayi kowa yasake shiga rigar nutsuwa, suka fara gaisheshi.

bude taro yayi da adduah sannan yafara magana " na taraku anan ne bandan komai ba sedan fayyace muku gaskiya" zuba mishi ido sukayi sunason suji meye ze fada , bin kowannesu yayi da kallo.
Chapter 36 · 0% Book details