← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 66

Sashe 59

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yau tunda suka tashi doctor yazo ɗan ganin ya yanayin condition din Mr azaad yake saboda yanzu ne yacika wata uku da sati biyu inhar de be samu lafiya a wannan lokacin ba to fa sede afara mishi shirye shiryen treatment din wata shida, yaseer da Fawwaz suna zaune akan kujera suna ganin yanda doctor din yake kokarin yin conversation da Mr azaad amma yakiyin magana ,yau haka suka tashi dashi ko irin dan sambatun da yake yi ma beyi ba yana zaune yabasu baya yana kallon waje daya, doctor Shankhar ya ce " Mr azaad don't you want to speak to me today?" Ko kallon inda yake Mr azaad beyiba doctor Shankhar yasake cewa " alright is okay, but do you know that you're a father now ?" kamar daga sama batare da sun taba tsammanin hakan ba kokuma tunanin haka ze faru ba , sukaji Mr azaad yabawa doctor Shankhar amsa da" Yes i know " shikanshi doctor Shankhar seda yaji kamar kunnen shine ya mishi gizo yasashi sake cewa " okay do you know you're a father right?" murya adaƙile kamar wanda ake takurawa cikin rashin sonyin magana ya ce" Yes i know and please don't disturb me " atare Fawwaz da yaseer suka ɗaga hannu sama suna godewa Allah matsanancin farin ciki suka shiga wanda baƙi baze iya faɗa ba zama sukayi kusa da Mr azaad fuskokinsu dana doctor duk na dauke da murmushi, congratulations doctor yayi musu sannan ya ce nanda One week za'a sallameshi , kafin doctor Shankhar ya rufe baki Mr azaad ya ce ko kwana ɗaya baze ƙara a asibitin ba , yanayin yanda yake magana kaɗai ma mutum yaji yasan ya canza sosai domin inyana magana ko ɗago kai ba yayi balle ya kalli me mishi magana miskilanci yaƙaru fiye da na da . Sallama doctor yayi musu yafita, yaseer ya ce " dude nayi farin ciki sosai da Allah yabaka lafiya" banza yayi dashi kamar be jishi ba se bayan minti goma ya ce " ina twinkle?" Fawwaz ya ce " an karbota a asibiti,gobe za'ayi sunanta" tundaga nan besake ce musu komai ba ya mike yashiga toilet bin bayanshi sukayi da kallo , ganin a ƙashi ɗari na halinshi nada yanzu ƙashi 90% yadawo, saboda dama shigowar fanan rayuwarsa ne yasa yarage amma yanzu sundawo fiye dana da dinma , suna magana yafito daure da towel a kugunshi kallonsu yayi be ce musu komai ba dan maganar ma wahala yake bashi , fahimtar abinda yake nufi da sukayi ne yasa Fawwaz mikewa yabude wardrobe a bangaren da kayanshi yaje ya fito mishi da jallabiya fa ra , karba yayi ya koma toilet din yasaka yafito fuskan nan adaure kamar wanda besan menene kalmar dariya ba arayuwarsa.
Sude se aikin binshi da sukeyi da ido , Dan sunsan ko sunyi mishi magana ma ba kulasu zeyi ba hakan yasa suka zuba mishi ido kawai, kira ne yashigo wayar yaseer number Abba ne dagawa yayi suka gaisa sannan ya tambaye shi Mr azaad , girgiza mishi kai Mr azaad yayi alamar kar ya ce musu komai. Kamar yanda ya buƙata haka yaseer yayi yace mishi yana nan lafiya haka suka gama magana sannan ya katse kiran.

" Fawwaz kayi mana booking flight ayau din nan zamu koma Nigeria". " okay " Fawwaz ya amsa sannan yayi musu booking flight s online karfe 6:00mp jirginsu ze tashi.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
( Yar lelen Jarumai)

*🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚*

⚜️📚J. A. W🖋️📚

THE END .

*Wato Hausawa sunyi gaskiya dasukace komai yayi farko zeyi karshe haka zalika laifin daɗi karewa,ya Allah ka yafemin kura kuran da nayi acikin wannan littafin😭🙏 duk wanda na batawa rai yayimin afuwa ya yafemin dan ɗan Adam ajizine . Masu min addu'a da fatan alkhari ina godiya bazan taba mantawa daku ba, masu karfafamin guiwa Kuma ina godiya bazan taba mantawa daku ba domin kun ban babban gudunmawa nagode sosai Allah yabar zumunci*

PAGE 6️⃣3️⃣

Batare da yan Nigeria sun san da zuwan nasu ba karfe shida nayi suka wuce airport jirginsu yatashi zuwa gida Nigeria, karfe hudu na asuba jirginsu yayi landing a gombe lawanti international airport, taxi suka shiga zuwa gida tunda suka taho a cikin jirgin babu wanda Mr azaad yayiwa magana acikin su har suka shiga taxi zuwa gida se hiransu sukeyi uffan be ce musu ba daga karshema surutun nasu ma ya fara damunshi yaja dogon tsaki suna jin haka sukayi shuru da bakinsu .

*Horn me taxi yayi , fitowa baba me gadi yayi dan ganin su waye , ganin Mr azaad ne dasu Fawwaz yasa ya wangale musu gate yaname murnan ganin Mr azaad*

Fitowa yayi yabarsu suna sallamar me taxi , shigowa cikin part din yayi jin motsi a kitchen yasashi ya tsaya daga bakin kofa ya ce " ƴata na wajen waye ?" Dasauri abu ta juyo jin muryan da batayi zato ba , cikin farin ciki ta washe baƙi " yallabai Azaad kaine alhamdulillah sannu da hanya , tunkwal na wajan ummi" yar harara ya watsa mata jin yanda takira sunan twinkle da tunkwal barin kitchen din yayi ya shige part din ummi dake bathroom taje dauro alwala zatayi nafila. Hawa kan gadon yayi yadauki twinkle dake baccinta peacefully yana kallon fuskanta da bashida maraba dana fanan yanajin tsananin kaunar twinkle aranshi ,ahankali yafurta " sleeping beauty" ya mannata ajikinshi tashi yayi dauke da ita ahannunshi yafice a bedroom din ummi ya nufi nashi bedroom din, kwantar da ita yayi akan makeken gadonshi yasake rufeta da blanket sannan ya shiga toilet yayi wanka da alwala yazo yafara nafilfilu yana addu'a Allah ya kare mishi fanan yakuma sa tadawo rayuwarsu be tashi na har seda aka kira asuba yayi Sallah sannan yahau gadon yashiga blanket din yajawo jaririyar shi kusa da shi yana kallon fuskanta,ahaka bacci yayi awon gaba da shi .
Chapter 59 · 0% Book details