← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 66

Sashe 15

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Haka tanaji tana gani tayiwa su mama sallama, suka fito ita da suhaima tana rike da hannun auta ajikin motar suka samu Mr azaad da ya al ameen suna tattaunawa game da yanda zaa shawo lamarin ya usman bude motar yayi ya dauko fashion bag dake cike da chocolate kala_kala yaba auta karba tayi tana fadin " thank you yaya balarabe god bless you" murmushi kawai yayi azuciya ya amsa da Ameen motar suka shiga fanan na musu bye-bye.

Sun danyi nisa da tafiya se taga yacanza hanya kallonshi tayi tace " Mr azaad ina zamuje naga nan de ba hanyar gida bane" batare da ya kalleta ba yace " namanta ban fada miki ba dazun nagama cinikin kanki to yanzu zamuje a fille ne" iya tsorata fanan ta tsorata saboda ko kadan bataga alamar wasa a fuskanshi ba he sounds very serious mazgewa tayi tana turo baki tace " da ka siyawa kanka rashin kwanciyar hankali dan wallahi nadinga maka fatalwa kenan" tuntsirewa yayi da dariya tare da taka birki motar gudun kar asamu matsala sosai yake dariya kamar ba Mr azaad ba, ya salam wani irin kyau yakara da yake dariyar kyawawan fararen hakoranshi su kansu abin kallo ne zuba mishi ido kawai fanan tayi yayi masifar mata kyau tun daga saninta dashi izuwa yanzu bata taba ganin yayi dariya irin haka ba se yau seta ga ma dariyar yafi mishi kyau ,koda shekara dari zasukai ahaka da wannan dariyar dauke akan fuskanshi bazata taba gajiya da kallonshi ba. hura mata iska yayi a fuska sauke idonta kasa tayi tana wasa da yatsunta jan motar yayi sukaci gaba da tafiya beyi packing a ko ina ba se a ice cream planet zallan ice cream ake siyarwa awajen wajan ya hadu sosai kaff gombe inde wajan da ake siyar da ice cream ne to yafisu kyau da tsaruwa, se fitar da hasken wuta kala_kala yakeyi tunda suka iso gun wajan yadauki hankalin fanan se kallon wajan takeyi tana sakin lallausan murmushi, " muje " kawai yace mata ya bude motar ya fito fitowa itama tayi suka shiga ciki , ice cream yazaba yafi kala biyar masu tsada mika mata ledar yayi yabada atm card suka cire kudinsu motar suka koma tun kafin yatada motar fanan tabude roba daya tafara sha se lashe baki takeyi ice cream din yamata dadi bata taba shan ice cream me dadi irin wannan ba , ahaka harta sha roba uku ta bude na hudu kenan zata fara sha yayi karaf yarike hannunta yakarbe ya ajiye kafin yace " yanzu ke in anbarki se ki tazubasu a cikin ki ko ? Keda yakamata ki hana wani shine ke kikeyi to wayan nan se gobe" yatsina fuska tayi idon nan nata dasuke manya dasu yayi rau_rau kamar me shirin kuka tace " ayyah Mr azaad kabarni in shanye Allah yanzu in bansha ba kwadayina ze tashi " kallonta yayi ta gefen ido yaga yanda takoma abin tausayi aranshi yace " wani abu se yarinta in bahaka ba mutum yata durawa cikin shi sanyi" afili Kuma yace " idan kwadayin yatashi inada abinda zan bashi " ganin ya manna mata hauka ne yasa tayi shuru tana bin ledar ice cream din da ido ahaka har suka iso gida.

Gyara packing yakeyi ta faki idonshi tadau roba daya tasa a hijab dinta tafito daga motar da gudu tayi ciki , murmushi kawai yayi dan yaga abinda tayi wato shi zatayiwa wayo , bin bayanta yayi yanda tasamu falon ba kowa shima haka yasamu duk sunshiga sun kwanta dakinshi yashiga yayi wanka ya sauya kaya izuwa sleeping dress ya kwanta.

Tana zaune a tsakiyar titi misalin karfe 2 nadare kafa yadauke babu kowa ba alamar koda kafar mutum se haushin karnukan dake tashi , zaman yan bori tayi gashi duk yarufe mata fuska ga mutum kwance agabanta cikin jini dake malala ajikinshi sanadiyar yaga cikinshi datayi kayan cikin duk suna waje itakuma se aikin cin namanshi takeyi zaro dogon hanji tayi tasa abakinta dake dauke da dogayen hakwara duk sun rine da jini , tana janshi kamar yanda akecin indomie harta gama cinyewa tass bata kyaleshi ba seda ta cinye duk wani nama ajikinshi yarage qashi bakinta ta kafa adede wuyanshi tana zuqan jini seda ta tsotse jinin kaff kafin ta dago kanta bakinta yayi dama_dama da jini zaro dogon harshenta tayi ta sude baki hade dayin gyatsa mikewa tayi tsaye tamaida gashinta baya nan take fuskanta ya bayyana ba kowa bace face zeenat Muhammad mainasara......

Kuyi hakuri da yanayin read more din yau wallahi yau nidince se a slow.

~Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏~

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Page 4️⃣6️⃣ & 4️⃣7️⃣

Duk abinda takeyi suna kallonta a madubin tsafi sun san yanzu zasu samu abinda sukeso tunda yar family sunsamu sun jawota cikin kungiyarsu bako wani kungiya bane wannan da yawuce vampires union, kungiya ce da suke shan jini da kuma cin naman mutane da dabbobi sunada matukar hadari Kuma sun bawa zeenat maita ne dan su rama abinda mommy ta aikata musu.

Taya akayi zeenat tazama daya daga cikin kungiyar vampires union, yau fitansu da safe ita da ya fawwaz and areef zasuje gidan anty amina daga nesa ta hango wata yarinya na tallan guiva setaji ya shiga ranta magana tayiwa fawwaz yatsayar da motar tasiya tafara sha acikine tasha maitar batare data sani ba .

Bayan sunzo gidan anty amina ne tafara jin wani irin sauyi ajikinta setaji kamar abu na mata tafiya hade da magana akunne. dakin su aslam da islam tashiga tadan kwanta ciwon Kai ne yafara damunta shisa dasu fawwaz sukace zasu tafi tace suje kawai ita se gobe zata dawo aikuwa tafiyar sukayi abinsu, anty amina data lura da yanayinta kamar bata da lafiya yasa ta tambayeta amma se kawai tace mata bakomai.

Around 10 duk sun kwanta ita kam takasa bacci wani azabebben yunwa ne yafara ciyota ,kitchen tashiga har lokacin ciwon Kai din besauka ba bude food flask din tayi dan ta dibi abinci toshe hanci tayi jin abincin namata wari kamshin danyen nama ne yadaki hancinta bin direction din da takejin kamshin tayi har izuwa fridge dauko namar tayi duka tana kallon shi , tunani" tafara taya zanci danyen nama " jitayi andaka mata tsawa akunne cike da umarni taji murya nafadi " ki tabbatar da kincinye naman nan " tun kafin yagama magana tahau cin naman haka tacinye namar da yafi kilo goma , wani sabon yunwa tafaraji jitayi naman dataci yatayar mata da kwadayi kamar wata mahaukaciya haka ta birkita kitchen din tana neman nama amma babu daki takoma kamshin su aslam da islam ne yacika mata hanci shinshinasu tayi tana ajiyar zuciya tasamu nama hankali kwance bude baki tayi nan take dogayen hakwara suka fito , jitayi namar aslam yayi tauri sosai kamar dutse haka ma Islam duk yanda takai da son cinyesu to abin yagagara badan komai ba sedan adduah da mamansu da babansu sukeyi musu afusace ta tashi tabar dakin jikin bango ta shige fitowa tayi abakin titi kwance taga mutum da sauri ta karasa wajan ta farka cikinshi tafara cin naman dama su suka ajiye mata ganin abin yafara aiki ajikinta yasa sukayi murna sunada ya kinin se ta cinye yan gidansu kaff.

Washe gari.
Chapter 15 · 0% Book details