← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 66

Sashe 60

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fitowar ummi daga toilet tadauro alwala kenan ta kalli kan gadonta fuskantar dauke da murmushi, gabanta ne yafadi lokacin dataga babu twinkle akai dasauri ta karasa izuwa gadon kamar wasa bataga twinkle ba hankalinta yayi matuƙar tashi ba shiri ta fice a part dinta saukowa downstairs tayi taga abu , abirkice ta ce " abu dan Allah akwai wanda kika gani yashiga part dina ne?" Murmushi abu tayi ta ce " eh ummi! Yallabai Azaad ne yashiga kuma naga fitowar shi da tunkwal a hannu " shuru ummi tayi jin abu ta ambaci sunan Mr azaad tunani tafara yaushe suka dawo to kenan hakan na nufin yasamu lafiya murna ne yakamata da sauri_sauri ta nufi part din nashi, bedroom tasamesu suna bacci zama tayi akan gadon tana shafa kanshi tanajin matsanancin farin ciki yana ratsata , ahankali yafurta " ummiii" batare da yabude idanunsa ba , " na'am son , fatan kundawo lafiya ?" tashi yayi yazauna ya ce " uhmmm" tundaga jin amsar daya bata ummi tasan he has changed completely ganin gaba daya fuskar shi ba walwala, riko hannunshi tayi ta ce " son kaga our little feena ko , babu abinda yarabasu da my feena, aduk sanda na kalli fuskar ta inaga ganin my feena atattare da ita, son yakamata yanzu kayi move on ko dan amanar twinkle da feena tabaka kazama uba na kwarai inkana cikin wannan yanayin taya ne zaka kula da twinkle? Hakuri shine Yakamata muyi ,mudauki dangana da juriyar rashin feena nasan is not easy for you my son, but you have to for the seak of twinkle ka ji " gyada mata kai yayi kawai batare da ya iya cewa komai ba yaname kwantar da kanshi akan kafadarta slowly ya ce" thanks ummi " ummi ta ce " son yaune sunan twinkle wani suna Yakamata asa mata " ajiyar zuciya Mr azaad yayi ya ce " Fatima za'a samata sunan wifey tun ranar da aka haifeta nayi mata huduba da Fatima " murmushi kawai ummi tayi tanajin dadi aranta a part din tayi Sallah. Karfe 7:00am aka raɗawa twinkle suna da sunan mahaifiyarta fanan, kafin gari yagama wayewa duk family kowa yasan Mr azaad yadawo cikin koshin lafiya , anty shayida tazo da yaranta yan biyu mata ta haihu satin da yawuce sukayi arba'in sunansu adeema da adeena ,haka anty zainab tazo tare da yaronta daya dawo daga egypt ya kammala karatu , yan uwa duk anzo suna su hairah da auta da amira tun karfe 8 suka zo gidan , haka mahaifiyar yaseer ma tazo , shigowa gidan baba da Abba sukayi suna part din Abba da wasu abokan abba suna hira Mr azaad yashigo da twinkle ahannunshi tana sanye da kayan jarirai me matukar tsada , zama yayi akan kujera rike da ita ya gaidasu suka amsa fuska asake Abba ne ya ce " to kabamu ita mu ganta mana" kamar baze bada twinkle din ba se kuma ya miƙawa baba ita , murmushi baba yayi yace " Fatima na biyu kenan , Allahu Akbar Fatima ta tafi Fatima ta dawo Allah yarayaki ya albarkaci rayuwarki" haka baba yadinga mata addu'a sannan yamikawa Abba ita shima karbanta yayi yana yi mata addu'a, yana zaune yana jiran su gama su bashi yarshi yayi tafiyarsa , karbanta yayi a hannun Abba . yafice abinshi ya nufi part dinshi afalo ya tsaya yana kallon katon hoton enlargement din hotonshi shi da fanan fuskantar dauke da ƙayitatciyar murmushi ta riƙe hannunshi tana kallon fuskanshi , shikuma yazagayo da hannunshi yana rike da kugunta fuskanshi asake dayan hannun kuma yakama kumatunta . Murmushi yayi lokacin daya tuna sanda akayi hoton , ranar da suka dawo daga shopping ne suka tsaya a garden suna hiransu gwanin sha'awa tashi sukayi zasu tafi yajawota jikinshi yayi yadaura hannunshi akan waist dinta dayan kuma kuma yariƙe kumatunta itakuma tana sakar mishi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau , suna ahaka basu sani ba Fawwaz dabesan suna cikin garden din ba yashigo burgeshi sukayi sosai yasa yafito da wayarshi yafara daukansu hotuna,yayi musu hoto yafi guda goma ankara dashi Mr azaad yayi yagalla mishi harara ganin inda yake kallo ne yasa fanan juyawa tana ganin Fawwaz ne awajen dasauri taraba jikinta da na Mr azaad cike da jin kunya tabar garden din da gudu, da karfi Fawwaz ya ce " haba antynmu kiyi hakuri kidawo bari in baku guri " damkar kunnenshi Mr azaad yayi ya ce " wato labe kakeyi mana nida matata ko ? " Kara Fawwaz yasa yana " sorry Babban ya'ya wallahi kun burgeni ne yasa nake muku hoto" hararanshi Mr azaad yayi ya ce " kafin awa daya kazo min da enlargement din hoton in kuma beyi kyau ba zakayi bayani " yasakeshi yabi bayan fanan. Dariya fawwaz yayi ya ce " salon soyayyar ku na daban ne ya azaad da anty fanan Allah yabarku tare " ya ida maganar yaciro waya yakira layin wani photographer yatura mishi hotunan ya ce yanaso ya mishi katon enlargement nan da anjuma akawo. Haka yazauna a garden har aka kawo enlargement din da akayi rapping dinshi shiga part din Mr azaad sukayi da shi basa falo suna cikin bedroom dinshi , manna enlargement din akayi ajikin bangon falo yazauna sosai yanda suka fito sukayi kyau ajikin hoton Kamar a kirasu su amsa. Fitowa Mr azaad yayi yaga harsun manna enlargement din ya ce " Allah yataimake ka " murmushi Fawwaz yayi suka fita shida wanda yakawo hoton , jin sunfice ne yasa ta fito " habiby kazo ka nunamin wanne zansa" tayi maganar batare da ta lura da enlargement din jikin bangon ba , nuna mata yayi da hannu zaro manyan fararen idonta waje tayi sosai ta rufe baƙinta ta karaso gaban hoton tasa hannu ta shafa ta ce " yaushe akayi wannan hoton , wallahi yayi matukar kyau sosai" tafada tana rungumeshi.

Murmushi yayi bayan ya gama tunawa yasa hannu yashafa hoton dede fuskar ta ya ce " i missed you so much baby rayuwa yamin zafi sosai da babuke aciki, ki kalli our little twinkle , na miki takwara sunanta Fatima ina fatan itama tazama jajirtacciya irinki me kyawawan halaye. Bazan taba cire rai da dawuwar ki ba ina nan ina zaman jiranki "
Kuka twinkle tafarayi jijjigata yayi yana murmushi ya ce" karfa kidauko min rigimar mommynki " kamar tasan me yafada tayi shuru yana tsaye agaban hotonsu zeenat tashigo kallo daya tayiwa hoton bata sake kallo ba saboda tasan intaci gaba da kallo tasan yanzu zata fara kuka ɗan ji takeyi tafi kowa missing din fanan " ya azaad ummi ta ce kabada twinkle " ya ce" kifice ki bani waje bazan bada ita din ba" da sauri tafita mishi a part din shi tsaki yaja yashiga bedroom yazauna abakin gado har time din yana rike da ita, fadawa ummi yanda sukayi da Mr azaad zeenat tayi,ummi dama tasan zaarina mikewa tayi dakanta ta tafi part din nashi tace yabata twinkle be mu sa ba ya mika mata ita takoma falo tabawa umma rahina da sukazo da mama, mama ta dade bata shiga farin ciki irin na yau ba jitakeyi kamar tana rike da fanan ne , haka akayi suna nagani nafada baby twinkle tasamu kyaututtuka me tarin yawa ,an yanka manyan shanaye guda biyar da raguna anyi sadaka dasu komai anyi awadace karfe hudu na yamma aka watse kowa ya koma gidajensu, dare yayi yagama komai yazo ze kwanta zasuyi bacci twinkle tafara kuka rarrashin duniya yayi mata amma takiyin shuru daukarta yayi yanufi part din ummi tunkafin ya karaso ummi tajiyo kukan twinkle dama abinda take jira kenan saboda bataci abincin dare ba haɗa mata madaranta tayi a feda yana shigowa ta ce " dama nasan zaku dawo ai ta fada tana karban ta tafara bata madaran shuru tayi tanasha , gama sha tayi yakarbeta sannan yasa hannu ya kwashi kayan madaran nata ummi de binshi da ido tayi harya fice .
Chapter 60 · 0% Book details