Sashe 61
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda twinkle tayi arba'in yafara fita da ita duk inda zashi yana rike da ita ummi da Abba sunyi mishi magana harsun gaji akan yadena fita da twinkle amma hakan be hanashi daukar yarshi ba duk inda zashi a gida ma sosai twinkle take samun kulawa kullum tana tare da ummi ko Abba ko suhaima da sauran yan gidan haka zeenat da yaseer suma suke zuwa gida akai_akai ɗan ganin twinkle haka su ya usman ma suna zuwa , haka duk sanda Mr azaad yatashi daga office yana biyawa gida da twinkle yakaiwa su mama ziyara .
irin kulawar da take samu awajen familyn ta guda biyu na musamman ne takara girma kowa sonta yakeyi duk abinda suka gani na jarirai zasu siya mata shi musamman me gayya me aiki daddynta duk sati se yayi mata shopping din lafiyayyun kayan madaranta da kayan sawa daduk wani abinda yaro yake bukata ga dakin da aka ware mata anzuba mata kayayyakin wasa aciki , sau daya twinkle takesa kaya bata sake maimaitawa duk kayan data saka baa kara samata shi komai nata special ne kuma masu mugun tsada ,hatta kayan da zatasaka komai dinta. gata iya gata twinkle na ganinshi .
Sosai ummi tayiwa Mr azaad fada kafin nan suka samu yadena fita tare da twinkle, tana da wayo sosai gashi bata da ƙiwiya saboda kowa tasan fuskarsu musamman yanzu da tafara zama daga zaran taga daddynta yadawo zata fara bude baki tana dariya hade da miko hannu yadauketa haka zedauketa yana dariya haka take tabasu nishadi agidan , safiyar yau zeenat ta tashi da naƙuda aka kaita asibiti ta haifi namiji kyakkyawa me kama da babanshi yaseer, seda suka dawo gida tukun suka kira family suka sanar dasu aikuwa sunyi farin ciki da jin labarin haka sukaje yi mata barka , bayan sati daya akayi suna aka yiwa baban yaseer takwara yakubu suka mishi inkiya da ashraff.
bayan ta haihu da sati biyu hairah ta haihu amma bata iya haihuwa da kanta ba seda aka mata operation ta haifi ya mace taci sunan mama wato sumayya akayi mata inkiya da samha gida aka dawo da hairah saboda kulawa da ita kuma mama na iya kokarinta wajen kulawa da ita yanda Yakamata su ya usman anzama baba , Amira ce take ta ja da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe , suhaima haryanzu shuru kuma daga ita har Fawwaz din hakan be damesu ba .
Duk sanda Mr azaad yatafi da twinkle Company ma'aikata sun dinga yi mata wasa kenan saboda tana da farin jini ga rashin ƙiwiya , duk da Mr azaad baya basu ita saboda be yarda da kowa ba se Faisal, shi kadai ne duk sanda Mr azaad yazo da ita suke tare dama tun faɗan da ummi tayi mishi akan fita da ita yadena se de duk ranar Friday yana fita da ita .
Amira ma ta haihu ta haifi na miji anyiwa baba takwara suna ce mishi musin duk anje suna Bauchi bayan angama suna kuma suka dawo .
haka rayuwa yaci gaba da tafiya abubuwa nata faruwa aciki me dadi da akasin haka Mr azaad de yana bawa twinkle datayi wayo sosai kulawa shida yan gidan suna nuna mata gata , areef yafara zuwa aiki a kamfanin Abba , hafiz kuma ya zana papper anfara nema mishi addimission a gombe state University , kuma yasamu yafara zuwa.
Allah yayiwa Alh Ibrahim tijjani rasuwa kuma yayi ta tonawa kanshi asiri daga karshe ya haukace sannan ya mutu , ga aneesa da ciwo yafara cin jikinta tadawo gida ta nutsu duk irin rashin kunya da wulakancin data dingayiwa mahaifiyarta Hajiya Zainab daga karshe ita ce, take kula da ita saboda uwa ce ita bazata iya kauda kai akan yarta ba dukda kuwa abubuwan datayi mata haka taci gaba da kulawa da ita sukaje asibiti aka daurata akan magani , alhamdulillah maganin yanadanyi mata aiki amma ba sosai ba saboda HIV yarigada yayi tsanani ajikinta yafara kashe duk wani garkuwar jikinta.
Abangaren nusaiba da lukman suma suna nan suna rayuwar farin ciki da yaronsu namiji da ta haifa wata biyu dasuka wuce .
__________________________________________
NASMINAYA.
" Sarauniya kar muce zamu biyewa zuciya, kar ayi wannan yakin yanzu koda kuwa za'ayi muma mu rama irin abinda sukayi mana mu farmakesu a lokacin da basu sani ba nan ne zamu iyacin galaba akansu amma wannan sakon dasuka turo yanuna kancewa sun rigada sun shiryawa yakin kafin suka turo mana da saƙo" cewar wazirin nasminaya .daka mishi razanannen tsawa sarauniya tayi, a harzuke ta ce " yanda suka bukaci ayi wannan yakin dole za'ayi shi mudin ba matsorata bane , ai wannan nuna tsorone bamu cika ainihin jarumai ba inhar de bamu taresu gaba da gaba ba dole ne ayi kare jini biri jini , amma maganar kai musu hari batare da sun sani ba duk shirme ne "tafada tana kallon fuskokin ko wannensu kafin taci gaba da fadin " muma zamu nuna musu mudin masu nasara ne , hankalina baze taba kwanciya ba senaga bayan wa'yannan azzaluman dan haka kufara shirin yaƙi, sannan ku maida musu da saƙon cewa na amince da wannan gwabzawar da za'ayi , abashiyya ke kuma kitafi masarautar kusfah ki fadawa sarki habar muna bukatar dakaru saboda yaƙin dazamuyi . Dole wannan ƙaron ayi dayan biyu ko mu ko su " gimbiya afroza ce ta ce " yake sarauniyata tabbas iname goyon bayanki dari bisa dari amma muna bukatar dakaru masu matukar yawa, saboda wa'yanda zamu fuskanta kungiyoyi biyu ne kuma shu'umai ne marasa tsoron Allah " yarima ahil yace " nayarda da Maganar ki gimbiya amma fa kisani, masarautar nasminaya yafi karfin duk wasu kungiyoyi munada karfi dakuma kwarjini , kar ɗan sun kasance kungiya biyu ne su daga mana hankali da yardar Ubangiji munfi karfinsu" murmushi sarauniya tayi wanda tunda tazo masarautar ba ta tabayi ba ta ce " wannan gaskiya ne yarima ahil " suna cikin wannan tattaunawa wani tsohon dattijo yashigo fa da hannunshi rike da wasu abubuwa masu tsayi yarufesu da farin tufafi , dakatar da shi fadawa sukayi suka hanashi shiga yayi yayi subarshi domin yanada magana da sarauniya amma suka hanashi da karfi yayi magana " yake shugaba me adalci zasu kibawa wannan bawan naki daman yin muhimmiyar magana dake dan Allah dan Annabi" daga musu hannu sarauniya tayi suka barshi yashigo nuna mishi wajan zama jakadiya tayi , yazauna ya ce " shugabata zanso abamu waje" kallon su tayi suka ɓace yarage daga ita se gimbiya afroza da yarima ahil se jakadiya, galadima abdud Shakur,se waziri iya sune sukayi saura a fa da. Sarauniya ta ce " dattijo zanso kafadamin dalilin dayasa kakeson yin magana dani" mikewa dattijon yayi ya ajiye abun hannun nashi akasa yabude tufafin da ya rufe su dashi nan take wukake guda biyu suka bayyana, wukane da akayi domin yaƙi anyi shine da baƙin narƙekken dalma se yalki da daukar ido sukeyi, duk kallonshi sukeyi suna jiran ƙarin bayani daga wajan shi .
" Ya shugabana wannan wukar ni na hadashi da hannuna domin bada nawa gudunmawan , a iya karfafa bincike na danayi shubumbum da tanzarzar zallar wuka babu abinda zeyi musu , shisa naje har birnin sin wajan uban gidana shine yafadamin abinda ze kashesu , bayan nadawo ne nahada wa'yannan makaman domin baki su nasan ze taimaka dan Allah shugabata ki karbi nawa gudunmawan " yafada yana zubewa akan guiwansa jinjina kai sarauniya tayi itada su jakadiya ta ce" na karbi wannan kyautar taka amma kafadamin amfaninsa me kyau , saura mara kyau din " zama yayi ya ce" shugaba ko min yaya kar ki bari wannan wukar ya yankeki domin yanda zeyi miki illa haka suma zeyi musu illa " murmushi tayi ta ce" Masha Allah " galadima abdud Shakur ya ce" tabbas sarauniya da yan fa da sunyi matukar godiya da kuma jinjinawa wannan gudunmawan naka " sosai dattijon yayi murna yayi musu sallama yatafi.
Sarki habar yaturo musu da dakaru masu matukar yawan gaske haka masarautar nasminaya sungama shirya duk dakarun su domin fita yaƙi, masu kai saƙo wa kungiyar SATANIC da BAPHOMET duk sunje sunkai.
Fitowa sarauniya tayi cikin azabebben shiga na yaƙi ga khairaty na hannun daman ta dakuma dakaru mata dasuke biye da ita, haka gimbiya afroza tafito itama cikin shigar yaki da yarima ahil ga shufan da shufaina yaran jakadiya da ita kanta jakadiyar duk sunyi shiga cikin kayan yaƙi. tsofaffi dakuma yara na masarautar sunatayi musu adduo'in samun nasara dakuma dawuwa lafiya .
Hawa kan dawakai sukayi suka fara firewa akan dokunansu har suka dira a babban filin dazaa gabatar da yaƙin .