← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 66

Sashe 27

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

suna can duniyar su shugabansu daya kansance katon bakin aljani mara imani me mugun halitta mara kyaun gani rabinshi mutum rabinshi dabba kuma wata halitta daban ga katon qaho akanshi, yana zaune akan kujeran mulkinsa suna tattaunawa da wasu mugayen halittu marasa kyaun fasali inda sukema kadai duk bil adaman daya shiga inde yaje tofa fitowa se wani iKon Allah, wata bakar mujiyace daga zama tafado kasa kamar wanda aka wurgo tana fadowa gabansu takoma rabinta mutum rabinta mujiya tsirara ba kaya ajikinta duk jikinta gashi gashi ga qaho agaban goshinta, afusace shugaban nasu da murya me amo mara dadinji yace " keeeeeeeee! Abinda yafi miki sauki shine ki sanar dani abinda naturaki kinemo min domin shi kadaine ze taimaka mana wajan mallakar sarauniyar nasminaya" muryanta kamar yanda kukan mujiya yake fita haka yake tace " yakai shugabana SHUBUMBUM na samoshi ! shidin cikekken dan baiwane dayazo duniya besan shiwaye bane kuma babu wanda yasan da hakan se wata halitta kwali daya dake tare dashi wato tsuntsun arnass , shidin yakasance dan babban gida acikin bil adama shidin babban dan kasuwane da akeji dashi" murmushi kawai shubumbum yakeyi jin bayanan da aka kawo mishi duba madubin tsafi yayi ko ze ganshi domin yanzu shi kadaine ze iya sasu suyi nasara akan kungiyar satanic kuma harsuci galaba akan sarauniyar nasminaya, wasu surkullenshi yayi a hannu sannan ya watsawa madubin tsafin, hoton kafanshine yafara bayyana nan take kuma madubin tsafin yatarwatse kaca_kaca yana fitar da hayaki, seda suka ja baya suna jinjina karfin baiwan da yake tare dashi......

Tom duka duka anan nakawo karshen rubutun yau se mun hade tomorrow in sha Allah.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&rehttps://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
Wannan labarin qageggen labarine ban yarda wata ko wani yajuyamin labari ta kowani tsiga ba , bana bukatar ajuyamin labari ko ayi wani Abu batare da izinina ba😐🤔

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

( J. W. A 📚📚📚)

PAGE 5️⃣4️⃣

Hajiyarsu amira ce zaune afalo tagama list din abubuwan da zata aiki amira kasuwa , fitowa amira tayi daga dakinta sanye da riga da wando ta daura after dress baki akai tayi rolling din gyale akanta tayi kyau sosai,se turo baki takeyi, kama baki hajiya tayi tana kallon amira dake turo baki gaba tace " to ba baki za ki turo ba ! Ko wuya zaki turo sekinje kasuwar nan yauwa" kamar amira zatayi kuka tace " hajiya yanzu da yamman nan zakice min inje kasuwa kibari gobe da safe" " to ban bari ba ga kudin nan da list, in kin gadama kije " cewar hajiya . Daukar kudin tayi tasaka ajaka da paper tafito , tana tsaye abakin titi tana jiran masu napep se ga motar ya al ameen ya tsaya agabanta yasauke glass , kallonta yayi yace" yar kanwa ina zuwa haka ?" turo baki tayi tace" hajiya ce ta aikeni kasuwa " ganin yanda take ta babbata rai ne ya bashi dariya yace mata " shigo muje " bude murfin motar tayi ta shiga tace " ya al ameen ina wuni ?" amsawa yayi da fara'a akan fuskarshi yace " wata kasuwa kenan ?" " Main market " okay yabata amsa kafin yace" nikam yar kanwa yaushe ne zamusha bikinki ne ?" dariya tayi sosai dan tambayar yabata dariya tukun tace " ya al ameen Allah kaban dariya ! Tom ba yanzu ba tukun dan yaron abokin daddy da muke soyayya dashi mun rabo dan bashida dabi'a me kyau , shisa ni yanzu bazan sake bawa ko wani na miji dama ba tukun gudun kar abatamin lokaci , se na gama karatu tukun " jinjina kai kawai ya al ameen yakeyi dan ya gamsu da maganar ta yace " tofa yar kanwa kina nufin bazaki bawa ko wani namiji dama ba kenan harda yayanki da ya dade da dakon sonki aranshi ? " Kamar saukar aradu haka taji maganarshi cak taji ruwan jikinta ya shanye ta gagara ko da kwakkwaran motsi , tabbas ya shammaceta batayi tunanin haka ze fada mata ba kunya ne yarufeta, nunawa tayi kamar bata gane me yake nufi ba tace " ya al ameen wani yayana din kenan?" Murmushi ya al ameen yayi yace " yayanki da kuke tare acikin motar yanzu kuna tafiya zuwa kasuwa " yabata amsa cike da barkwanci , sa gyale tayi ta rufe fuskanta takasa magana har suka isa main market yayi packing , Bude motar tayi tasa kafafunta waje sannan tace " se anjuma ya al ameen nagode" " noo my mirah baki ban amsa ba za ki tafi?" daburcewa tayi dan tarasa amsar da zata bashi yasa tace " ayyah ya al ameen mu karisa magana a waya " ta fada tana shagwaba fuska . gyada mata kai yayi tafice ko juyawa batayi ba taci gaba da tafiya amma tanaso tajuya ta sake kallonshi ko da sau daya ne, juyowa tayi suka hada ido yana tsaye ajikin motar yazuba mata manyan idonshi irin na fanan , seda taji meyasa tajuyo gudu_gudu , sauri_sauri takeyi saboda ta bacewa ganin shi seda ya tabbatar da tashiga kasuwar sannan yashiga motar , yana murmushin nasara dan yadade yanason amira kawai be taba fada mata bane .

Bayan sati biyu soyayya ya kankama sosai tsakanin ya al ameen da amira kuma har manya sunshiga ciki an yanke zaa hada rana daya dana fawwaz,ya al ameen sekuma na yaseer da zeenat dasuma yanzu suke shan soyayya ruwa_ruwa, ya usman kuwa yanzu ne suka fara shakuwa da hairah ahankali yake samata sonshi a zuciyarta duk da she's just 16yrs , kuma an komar da ita school tana jss 1 haka hafiz ma an sashi a school yana ss 1 , suna samun gata sosai kamar yan gida sun saki jiki gashi alhamdulillah suna fahimta a makarantan dan brain dinsu naja.

Nusaiba anyi aurenta da yayanta lukman dukda madina takawo tashin hankali sosai amma hakan be hana auren ba saboda alh me ruwa ya sanar mata muddin ta hana auren a bakin aurenta shisa ta zubar da makaman yakinta bawai dan tanason auren ba.

Yau ne su suhaima da ya al ameen suka fara shiryawa domin komawa bauchi state gobe zasu wuce da sassafe zasu dau hanya shiryawa suhaima da auta sukayi ya al ameen ze kaisu gidansu Mr azaad suyiwa fanan sallama , sun fito har sun shiga motar amira tazo itama zata bisu komawa baya zeenat tayi tazauna tabata front site hakan kuwa yayiwa ya al ameen dadi, haka suke tafiya suna hira shida mirah shi .
bayan isarsu gidan duk afalo suka samesu suna zaune banda Mr azaad da fawwaz da suka fita office, anty amina tun sati daya da ya wuce takoma, fanan ta warke sumul tana tafiyanta dede kamar da, takara fresh da kyau sosai suna falo ita da ummi da zeenat,areef . shigowa falon sukayi suka zauna suna gaida ummi . Amsawa tayi fuskanta cike da farin cikin ganin su , auta kuwa rungume fanan tayi tana dariya tayi luf ajikinta , zeenat ce tace" ohhh su auta akwai son jiki kamar mage " dago kai auta tayi tace" ummi ina wuni ? Anty zeenat Ina wuni? Anty fanan ina wuni" ya alif Ina wuni ?" Amsawa sukayi suna dariya jin bata iya kiran sunan areef ba sede tace alif, areef ne yace" baby auta dan Allah kibarni karki batamin suna " dariya sukayi dan auta da areef insun hadu haka zasuta drama yana biye mata.
gaida ya al ameen zeenat da fanan, areef sukayi ya amsa yana tambayar areef " Ina fawwaz?" " Fawwaz ya fita office" cewar areef gyada kai ya al ameen yayi .
Shigowa abu me aiki tayi da su drinks da fruits hade da snacks ta ajiye musu.

Amira ce tace " besty kinji suhaima ko? wai gobe zasu koma bauchi " da sauri fanan ta kalli ya al ameen tace " ya al ameen wai dagaske dama tafiyar taku gobe na nan ?" kafin ya al ameen yabude baki yayi magana suhaima ta rigashi da " ahhh lallai matar nan da kin dauka wasa ne ko yanzu ma sallama mukazo miki " har ran fanan taji ba dadi tafiyarsu da zasuyi dan tunda suke basu taba zuwa sun dade sosai ba irin wannan setaji dama kar su tafi dukda ma suhaima kam gombe zata dawo kuma a gidan amma taji ba dadi , kwabe fuska tayi tace" ayyah sweet sis karki tafi kinji ? , Ya al ameen ku kara wata 1 " dariya taso bawa ummi ganin yanda lokaci daya walwalarta ya dauke yasa tace " karki damu feena kafin lokacin bikin ai zakije in kun dawo daga dubai zaku tsaya acan kinji ?" " tom ummina " fanan tafada tana kwantar da kanta akan cinyar ummin . yanda ummi take da fanan kamar ita ta haifeta ,matar batada matsala ko kadan hakan ya faranta ran ya al ameen da suhaima hatta amira taji sun burgeta adduah takeyi Allah yasa itama nata surkan suzama haka dukda bata san cikekken halin umma rahina ba , dan duk zuwan da sukeyi gaisawa ne kamai yake hada su.
Chapter 27 · 0% Book details