Sashe 58
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Video ne da CCTV Camera yadauketa na duka asibitocin da taje ta taimaka musu da kuma short video lokacin da suka rungume juna itada Mr azaad ga kuma twinkle dake hannun Mr azaad, se playing din videos din akeyi again and again aƙasa a rubuta 'the warrior ' wani journalist yafara kwararo bayanai " wannan dakuke gani ita ce Jarumar da ta cece rayuka bila adadi, kwana biyu dasuka wuce wanda a wannan ranar ne muka tashi da tashin hankali mara misiltuwa , kamar yanda kuka gani a wannan dauka na CCTv camera ita ce ta cece jarirai da ake kokarin kashewa da kuma mata masu ciki da masu jego, dama ako ina Allah baya taba goyon bayan zalunci shisa yaturo mana da wannan baiwar Allah. Allah yashiga tsakanin mu da mugaye azzalumai yayi mana tsari dasu itakuma Allah yabiya mata bukatunta na alheri yabata Sa'a akan abinda tasa gaba, ya Allah ya kare ta aduk inda take , ƙasa Nijeriya dakuma ƙetare we're very proud of her she's our superstar warrior. Yanzu zakuji daga bakin wa'yanda suka kasance sheda na gani da ido, sune wa'yanda suke cikin asibiti abin yafaru " magana wani magidanci yafara " sunana Abubakar lawan . wato abinda yafaru shekaranjiya tabbas ni ganau ne ba jiyau ba domin nakai matata haihuwa ne wannan lamarin ya rufta damu a asibitin wannan baiwar Allah ita ta cece jaririnmu dakuma matata bazan taba mantawa da ita ba kuma , itadin matace ga azaad the billionaire sannan sirka ga ahalin mainasara, yanda ta taimaka mana Allah ya taimaka mata ya shige mata gaba aduk lamuranta " haka sauran da aka gayyato suka dinga fadar irin aiyukan da fanan tayi da taimakonsu datayi, haka aka dinga hasko hotunan fanan ta ko Ina yazamana labarinta akeyi , ko ina aka waiga jama'a se addu'a sukeyiwa fanan manya da yara, kowa se bashi dama akeyi yana fadan ra'ayinsa dangane da fanan kowa alkharinta kawai suke magana .
Duk jikinsu yayi sanyi ganin irin yanda al'umma tun yanzu sunfara alfahari da fanan ko ina yabonta akeyi , guntun hawayen da yazubowa ummi ne tasa hannu ta share , Abba ya ce " Allah mungode maka " tashi yake kokarin yi idonshi yasauka akan video fanan da ake nunawa a tv asukwane yakarasa tashi yanufi tv da gudu yasa hannu yana shafa " wifey kalleni , ki kalleni wifey kizo mu tafi gida kinji " dasauri suka bi bayanshi zuwa wajan tv ganin yanason birkicewa lokaci daya, dukan tv yakeyi da iya karfinshi wai anashi tunanin yanason yafito da fanan din ne dake cikin tv ,dunkule hannunshi yayi ya bugawa tv wanda seda yayi sanadiyar wargajewarsa raga_raga rikoshi Abba da Fawwaz sukayi yanata sambatu yana kiran sunan fanan, su biyu suke rike dashi amma sun gagara mishi rikon da baze kubce ba ,fisgewa yayi yahaura upstairs da gudu yashiga part dinshi yarufe yasa key .
Yaseer ko magana ya kasayi yana zaune yayi tagumi abin duniya yadameshi ganin yanda babban amininsa da bayida kamarshi yana cikin wani hali, hawaye yataru a idonshi. Ummi kam izuwa yanzu bata iya controlling din hawayenta idonta sunyi ja sosai, daga ranar da fanan ta tafi izuwa yanzu kullum a cikin kuka suke da damuwa.
Haka abangaren su mama duk suna kallon labarai da suke yawo a gidajen rediyo da kuma social media, murmushin takaici kawai mama tayi aranta tanayiwa fanan addu'a.
Yau Flight dinsu Mr azaad yatashi zuwa kaishi India suka sauka a asibitin Narayana superspeciality hospital babban asibitine a India da babu kamarshi komai nasu na musamman ne , babban part aka bawa Mr azaad acikin asibitin aranar da sukazo a ranar doctor Shankhar yafara dubashi .
Bayan kwana uku Abba ya koma Nigeria, Fawwaz da yaseer ne zasu zauna tare dashi.
Acikin wata daya duk sun rame amma damuwar dasuke ciki yadan ragu dukda bawai yafita azuciyoyinsu bane kawai suna dannewa ne domin sunyi tawakƙali. Duk bayan sati daya se sunkaiwa little twinkle visit a asibiti suna kallonta acikin kwalba haka ma suna kaiwa Mr azaad visit duk sanda sukaje sesunyi kuka , acikin dakin dayake ko ina yayi bi bangon yazana hoton fuskan fanan da yana kallo shi kadai za'a ga yana magana, amma yanzu abun da sauki.
NASMINAYA.
Tafiya takeyi cikin izza da mulki hade da jarumta, tana sanye da doguwar riga yellow color kanta dauke da crown ( hular sarauta) din sarauta, rigar yanaja abaya kuƴangu suna rike mata da bayan rigar domin yana da tsayi sosai , jikinta tako ina tasha ado da zinari, fatar jikinta se yalki yakeyi da idanunta , gashin kanta yana abaje shima an mishi kwalliya da gold sosai tayi kyau , fuskanta babu ko da alamar murmushi. Tunda suka nufo hanyar fa da ake mata bushen sarewa duk inda ta wuce se an sunkuya an gaisheta sannan bazasu tashi ba seta wuce tukun zasu iya mikewa , tana shigowa fa da duk suka zube akan guiwowinsu suna ɗiɓan gaisuwa agun babban sarauniya, zama tayi akan kujeran mulkin da aka ƙawa tashi da lu'ulu'u ta ɗaura ƙafarta daya kan daya daga musu hannu tayi alamar ta karbi gaisuwar sannan suka koma suka zauna , manyan sarakunan aljanu ne takowa ni bangare sunzo ne domin yi mata barka da zuwa , agefenta kuwa akwai kujeran gimbiya afroza da na yarima ahil se kuma na manya masu muƙami a nasminaya irinsu galadima abdud Shakur da jakadiya da sauransu , tashi sukayi suna gabatar mata da kansu , haka ranar sukayi shagali sosai domin farin cikin dawuwar sarauniyarsu abin sonsu.
AFTER THREE MONTHS
Gangarowa zeenat tayi daga upstairs tadan rame ga cikinta da yafara fitowa tana " ya areef wai kai da Hafiz baku gama bane nifa nashirya dan Allah kuzo mu tafi kunga su Abba sun riga da sun tafi " tayi maganar tana saukowa daga staircase din , areef ya ce " muje mungama muma" fitowa sukayi zuwa packing lot suka shiga motar areef yayi driving dinsu zuwa medical center. Ciki suka shiga ɗan karasawa inda su ummi suke , samunsu sukayi suna rike da baby a hannunsu se wasa sukeyi mata tasha hadaddun kayan baby Pink color , suna cikin farin ciki da sauri zeenat ta isa inda suke tsaye din ta ba ta fuska ta ce " amma ai bahaka mukayi ba , Ni ce fa nace aduk sanda akazo daukan twinkle I will be the first person to carry her amma yanzu kun bata min Abinda nake matukar jira" du ka dariya sukayi jin maganar da zeenat tayi Abba ya ce " to zee yanzu ma ai gata nan " miƙa mata twinkle ummi tayi ta karbeta tana washe fuska se kallonta takeyi, fuskar fanan sakk take gani ana twinkle tsabar yanda kamanninsu yaɓaci sede fatar Mr azaad ne da ita , idonta arufe hannunta na cikin bakinta tana tsotsa hawayen da yazubo daga idon zeenat ne yasauka akan kumatun twinkle mutsu_mutsu tafarayi kamar zatayi kuka taname bude idonta kadan sannan ta rufe , zaro ido waje zeenat tayi lokacin dataga kalar idon twinkle da karfi ta ce " laaah kuga ikon Allah idonta brown color ne irin na kaka me martaba " zubawa twinkle ido sukayi suna jiran suga ta bude idon nata aikuwa tasake budesu , tabbas idonta iri daya dana me martaba shi ta gado a kwayar halittar ido kenan sannan natama yafi nashi nata brown ne sosai , haka suka koma gida cike da farin ciki bayan awa daya zuwa biyu su suhaima sukazo ganin baby amma banda mama da baba .
Baby girl gata nan yar lukuta da ita ga farin fata se karbanta sukeyi suna santin jaririyar sunayi mata photos suna turawa Fawwaz da yaseer da suke India su kansu sunyi farin ciki , adaren ranar me martaba da Fulani sukazo ganin jaririya aka tsayar da ranar suna nan da sati daya.
Tun bayan tafiyar fanan basu sake tsinkayar kansu acikin farin ciki ba se zuwan twinkle ita kadaima insuka gani ransu nayi musu sanyi domin suna kallon fanan atattare da ita, har yau daya kasance gobe suna baba da mama basu sa twinkle a ido ba sede a hoto ne suhaima da ya usman suke nuna musu ita , su umma rahina da amira da ya al ameen sunzo saboda suna da za'ayi.
INDIA
NARAYANA SUPERSPECIALITY HOSPITAL