← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 66

Sashe 16

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mr azaad ! bansan meke faruwa ba amma yau natashi da faduwar gaba Allah shine masanin dede" cewar fanan dago Kai Mr azaad yayi yadan kalleta shikanshi inya tuna zata tafi seyaji wani irin aranshi amma babu yanda suka iya, kwantar da kanta yayi a cinyarshi sannan yace " inkin ji faduwar gaba kidinga karanta innalillahi wainna ilaijiraji unnn in sha Allah ze dena, " murmushi tayi ta sakeyin lamo ajikinshi , tunda sukayi breakfast suke zaune afalo yana duba wasu files, yaseer ne ya kirashi awaya ya sanar mai yana falon ummi okay kawai yace mishi kallon fanan yayi yace " dauko hijab dinki muje falon ummi" tashi tayi dan ta dauko hijab din jikinta na sanye da Riga da skirt na kanti ,fitowa tayi tasamu ita yake jira rike hannunta yayi suka nufa falon ummi, duk suna zaune afalon banda abba da ya fita meetings ummi, yaseer, fawwaz,areef tsungunawa tayi ta gaidasu sannan ta zauna , yaseer ne kasa_kasa kamar wani munafiki yace " dude two days kayi wuyan gani ina kashiga " hararanshi Mr azaad yayi shida yadena nemanshi tun zuwan dayayi last harsuka so yin fada akan fanan amma yanzu yana ce mai ya buya , dariya yayi da yaga hararanshi kawai Mr azaad yayi bece mai komai ba , sallamar zeenat ne yasasu kallon bakin kofar tun kafin ta iso cike da tsokana yaseer yace " yanzu haka ake bakunta zeenat daga zuwa kin kwana shine za ki dawo da sassafe kamar wacce aka koro " turo baki tayi tace" ya yaseer kaiko ni nayi missing din ummina ne shisa na dawo " itade ummi batace musu komai ba suna yar hira da fanan da gudu zeenat tafada jikin fanan tana rungumeta, ummi ne tace " nikam zee kina da hankali kuwa karyata zakiyi" kafin takarasa maganar sukaga fanan tasa iya karfinta ta ture zeenat ajikinta seda ta kusa faduwa yaseer yariko ta dukkansu kallon mamaki suke binta dashi meye dalilin dazesa tayiwa zeenat haka ganin yanda suke shiri sosai kuma ko fada sukayi fanan bazata mata haka ba.
Tashi fanan tayi taje har gaban zeenat dake wur_wurga ido irin namasu rashin gaskiya bata taba tunanin fanan zata ganota ba .
Kamar wata tsohuwar mayya haka fanan take shinshina zeenat, Mr azaad dasu ummi sunzuba ido suna kallon ikon Allah,kallon cikin idon zeenat fanan tayi kafin tafara fadin " zeenat meyasa kike Karnin jini?" Inda_inda zeenat tafarayi tarasa karyan dazata mata daka mata tsawa fanan tayi tana " nace aina kika samo jini meye hadinki dashi karki bari in kara tambayarki zeenat" kansu yadaure sun rasa ina maganar fanan yadosa me take nufi da zeenat na karnin jini. Zazzare ido kawai zeenat takeyi can kuma tace " ayyah anty fanan dazun ne dazan dawo daga gidan anty amina se naga motar ya bige wata yarinya karama shine naje na dauketa jikinta duk jini to kuma dole jikina nima yabaci da jini, nakaita asibiti to kinji dalili" ajiyar zuciya duka sukayi harta Mr azaad danshi kanshi yafara zargin wani abu saboda yasan haka kurum fanan bazatayi irin wannan maganar ba,domin ita ba kamar sauran mutane bace shisa ita kadai taji karnin jinin su basu ji ba , ko kadan fanan bawai ta yarda da abinda zeenat tafada bane kawai ta kalleta ne dan tasan tabbas akwai wani bakon lamari adangane da ita , wucewa part dinsu tayi tabarsu agun dan har tsakiyar kanta takejin karnin jinin na damunta kallon zeenat ummi tayi tace " sekije kiyi wanka kinde ji abinda antyn ki tace " okay ummi itama tashige bedroom dinta wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tasamu tasha da kyar da asirinta yatonu magana ta fara hawaye nabin fuskanta " nashiga uku ni zeenat wannan wani irin mugun rayuwa na tsinci kaina bazeyu ba dole in fadawa anty fanan gaskiyar abinda ke faruwa nasan dole zata taimakamin" murya mara dadinji taji yana fadin " karki kuskura ki aikata aikin da nasani domin yin hakan dede yake da salwantar da rayuwar ahalinki in kunne yaji jiki ya tsira sannan adaren yau ki tabbatar da kin cinye yaron hafsat " cike da umarni ake mata magana babu abinda takeyi inbanda aikin girgiza kai.

Zaune suke a garden Mr azaad da yaseer , yaseer ne yake magana " mutumina naga kamar yanzu kadan fara saukowa " ajiye wayar da yake dannawa yayi sannan yace " dude bansan meyake faruwa dani ba yanzu kwata_ kwata bana iya mata abinda nake mata da and the worst thing shine komai tayi burgeni yakeyi haka kawai nakeson kasancewa da ita I don't know why" yaseer saboda farin ciki kamar yazuba ruwa akasa yasha haka yakeji yasan abokinshi yafada tarkon soyayya amma besani ba saboda be tabayin soyayya ba arayuwarshi yanzu bema san yana son fanan ba," dude inna fada maka wani abu zaka yarda?" Ya tambayeshi yana kallonshi gyada masa kai Mr azaad yayi cigaba da magana yaseer yayi " ka fara son fanan ne shisa ka kakejin wayan nan ba qin yanayin " sosai Mr azaad yake kallonshi dan san gasgata abinda yafada gaskiya ne ko karya tayama shi yafada soyayya batare da yasani ba. sassauta murya yayi yace " dude ba santa nakeyi ba kawai maybe kewanta nafara amma ka ajiye maganar soyayya agefe hakan baze faru ba" yar dariya yaseer yayi daya tuna wata magana da Mr azaad yataba gaya mishi " ina ruwana da tafiyanta" kafin yace " dude ba maganar kana kewanta da fa kafin kabara sonta ka tuna abinda kafadamin cewa fa kayi babu ruwanka da tafiyanta ko kamanta " shuru Mr azaad yayi. daurawa yaseer yayi da " kanason kasancewa da ita ko ?" gyada mishi kai Mr azaad yayi kamar karamin yaro yana son jin abinda yaseer ze fada. " dude wallahi kana sonta it will be better kayarda da hakan tun kafin time ya kure maka kafada mata kana sonta kaji dude" shikanshi yanzu ya yarda da tabbas yana sonta shafa lallausan sumar kanshi yayi yace" dude bazan iya fada mata ba saboda zata iya raina ni nikuma banason raini yashigo tsakanina da ita kasan mata haka suke " fashewa da dariya yaseer yayi Jin abinda Mr azaad yafada " haba dude wallahi fanan bahaka take ba duk wanda ya santa yasan bata da wannan rashin kunyar da kake magana akai mutumina kawai just go and confess to her shine kawai " murmushi ne ya subuce akan fuskar Mr azaad se yanzu ne yakejin sonta na kara shigewa zuciyarshi amma yana tsoron wani abu, yasan dole very soon zata tafi tabarshi karyazo yasabar wa kanshi da ita tazo tabarshi haka sukaci gaba da hira kafin suka bar gidan zuwa gidansu yaseer din afalo suka samu hajiyarsu yaseer tanawa kaninshi fada akan yawan yawon da yakeyi tunda suka shigo anwar yasha jinin jikinshi yasake nutsuwa ganin yaseer tare da Mr azaad dan yasan halinshi sarai hakuri yake bawa hajiyar gudun karta fada musu abinda ke faruwa watsa mishi harara Mr azaad yayi kafin yace " hajiyarmu meyayi " aikuwa kamar jira takeyi ya tambayeta tafara fada mishi, daura hannu akai anwar yayi aranshi yana fadin " nashiga uku hajiya ta kasheni wallahi yau nashiga hannun ya azaad nawa ta takare" pointing dinshi da hannu Mr azaad yayi akan yazo jikinshi duk yayi la'asar haka yazo wajanshi hannu Mr azaad yasa ya damki kunnen anwar da karfi ,kara anwar yasa yana yarfa hannu dan bakaramin damke kunnen yayi ba, magana Mr azaad yafara " wato ku yanzu kunyi girman da zaku dinga gantali ko ? Last time ya mukayi dakai ?" Kamar anwar zeyi kuka yace " alkawari namaka bazan kara ba ! dan Allah ya azaad kayi hakuri in sha Allah daga yau natuba wallahi bazan sake ba"
frog jump Mr azaad yasashi haka yafarayi yana zagaye falon, juyawa yayi yakalli hajiya ya gaisheta fuska asake ta amsa tana fadin " wato son se yau kayi niyar zuwa ko ? nadauka ma da matarka zakazo min " murmushin gefen baki yayi yace " kiyi hakuri hajiya in sha Allah zan kawo miki ita very soon" dariya tayi dan tasan halin Mr azaad yanzu setafi watanni ma bazata kara sashi a ido ba , part din yaseer suka shiga anwar de yana nan yana famanyin frog jump.

Haka yau fanan ta wuni wata sukuku da ita saboda lamarin zeenat ya tsaya mata arai dan tasan karya kawai zeenat tayi mata dan ta kaucewa zarginta , har tara Mr azaad be dawo daga gidansu yaseer ba abincinta taci tayi wanka tasa sleeping dress dinta ta kwanta.

Packing din motarshi yayi a packing lot tafiya yakeyi kawai yaga kamar gilmawar mutum wul ta gabanshi dakatawa yayi da tafiyar yana kallon the whole house, masu gadine kawai suke zaune suna jin radio sekuma securities da suma hiransu sukeyi , cigaba yayi da tafiyar harya shigo part dinshi har ze shiga bedroom dinshi se yajuya zuwa nata bedroom din wutan dakin a kashe flashlight din wayarshi ya kunna ya haskata akwance take tana bacci takawa yayi har izuwa bed dinta shafa cutie face dinta yayi daga bisani kuma ya manna mata kiss a forehead (goshi) komawa bedroom dinshi yayi shima wanka yayi ya kwanta. Sanyayyar murmushi fanan tasake lokacin da ya manna mata kiss tun shigowarshi ta tashi adduah takeyi aranta Allah yasa Mr azaad yafara sonta kamar yanda itama take sonshi.

To fa wato akace in zaka tona ramin mugunta ka tona dede kai yanzu de tsakanin mommy da zeenat nide narasa wazan kira mugu acikinsu.

Mommy tasamu lafiya sumul da ita tashirya fita dan taje itama tasamo yara 8 da suka rage zaayi sacrifice dinsu, itakuma zeenat tashiga part mommy har bedroom din Mansoor domin aiwatar da abinda a kasata ga shi dan banzan yunwa takeji tana bukatar jini ko nama kwance tasamu Mansoor yayi dai dai akan gado yana bacci bayan yagama shaye shayenshi dalewa kan gadon tayi tasa dogayen yatsunta tafara tsaga cikinshi , shuri daya Mansoor yayi rai yayi halinsa tass zeenat ta cinye namanshi da jininshi
Tana gamawa kuwa ta bace ta tafi dakinta tayi kwanciyarta cikinta a cike.
Chapter 16 · 0% Book details