← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 66

Sashe 53

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari doctors din ganin jikin fanan da sauki sosai yasa ya rubuta mata sallama , sungama kimtsawa mazan suke jira su shigo su tafi wa'yanda suka kwana da fanan ummi ce se anty shayida , su mama tun jiya bayan mangrib suka koma gida zeenat kuma Abba ne yacewa Mr azaad da fawwaz su maida su gida , Mr azaad da yaseer suka shigo cikin asibitin ga securites suna binsu abayana rike da manyan kwalaye yaɗuwa yayi da doctor din yabashi result din fanan, shiga cikin resting room din sukayi suka bar securites din suna rabawa majinyata da kuma nurses din asibitin kudi kamar yanda Mr azaad ya sanar da su , duk wani wanda yake cikin asibitin seda yasamu dubu dari dari , haka suka dinga kwararowa Mr azaad da family shi adduo'i , saboda awannan lokacin kafi karfin abinda zakaci arana daya ma ka godewa Allah gashi yau sun samu wani bawan Allah yaraba musu kyautar dubu ɗari _ɗari babu abinda zasu gode masa dashi sama da addu'a.

Tana zaune akan gadon ta sanya doguwar rigar atamfa kanta ba dankwali saboda bandejin dake kanta ummi ce tahaɗe mata gashin tadaure mata da ribbon zama yayi akusa da ita yasa hannu yana ɗan taba kan nata kaɗan gaisheshi tayi shida yaseer, amsawa yaseer yayi sannan yamata yajiki , Mr azaad be amsa mata gaisuwar da ta mishi ba ya ce " wifey ya jikin naki " kallon ummi tayi taga hankalinta ba'a kansu yake ba tana magana ne da yaseer, ta ce " jiki alhamdulillah" tashi sukayi da niyyar tafiya rike hannunta yayi ya mikar da ita tsaye sannan yadau gyalen da ya gani akan gadon ya rufe mata ajikinta, gaba su ummi sukayi shikuma yana rike da ita suna baya , duk inda suka wuce se jama'ar asibitin sun mishi godiya tare da sa mishi albarka haka suka shiga motoci suka dau hanyar gida , bayan sun isa ne , duk afalo suka samu su zeenat suna zaune suna zaman jiransu tashi sunayiwa fanan ya jiki ta amsa musu fuska asake wucewa da ita Mr azaad yayi zuwa part dinshi basu tsaya a ko ina ba se a bedroom dinshi zaunar da ita yayi akan gadon ya zauna akusa da kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana shaƙar kamshin turarensa , " habiby inasanka sosai" kallonta yayi da sexy eyes dinshi yace " wifey! inasanki bantaba tunanin aduniyar nan akwai macen da zanso har inyi rayuwar aure da ita ba se akanki Allah yadoramin sanki banajin zan iya rayuwa batare dake ba, inasonki sosai da ke dakuma unborn baby mu " dagowa tayi dasauri ta kalleshi da alamar tambaya ta ce" habiby bangane abin kake son fadamin ba ! what do you mean by our unborn baby?" daura hannunshi yayi akan shamulallen cikinta da babu alamun akwai ɗa aciki ya ce" yes up course baby kina dauke da ciki , kinadauke da jinina acikin ki munkusa zama parents, bazan iya misalta irin farin ciki da nake ciki ba " hawaye ne yafara wanke mata fuska da mamaki yake kallonta ganin daga fada mata tana dauke da ciki tafara hawaye gabanshi ne yafadi tsoronshi daya kar fanan ta ce batason cikin dake jikinta, riko hannayen ta yayi suna fuskantar juna ya ce" baby why are you crying?" rungumeshi tayi gam cikin muryan kuka ta ce" habiby kukan farin ciki nakeyi , nima yau ina dauke da baby acikina alhamdulillah zanji abinda iyaye sukeji insuna da juna biyu. habiby babban farin cikina shine zantafi in bar muku abinda zaku kalla kuji sanyi aranku , ko bayan raina nasan nabar iri aɗoron ƙasa " shi yanzu babu abinda ya tsana sama da yadinga jin maganar tafiyanta hakan daga mishi hankali yakeyi se yaji kamar shima yabita kome ze faru ya faru shafa bayanta yakeyi ya ce" kidena fadar haka ko so kike kidinga dagamin hankaline , yanzu lokacin farin ciki ne ba lokacin bakin ciki ba Please ki bari " raba jikinta da nashi tayi ta aro murmushi ta yaɓa wa fuskanta ta ce" am sorry my love bazan sake ba , yanzu fadamin wata nawa ne babyn ?" fito da result din da doctor yabashi yayi ya bude duk sun nutsu shida ita suna karantawa sosai sukayi mamaki ganin cikin wata hudu ne dede, su duk tunanin su karamin cikine da be wuce one month ba ganin yanda cikin nata yake a shamule babu alamar akwai ɗa acikinsa " laah habiby cikin wai wata hudu amma kalli cikina " tafada tana daukan hannunshi ta daura cikinta shafa cikin yayi yaduƙo da kanshi dede cikin ya mannawa cikin nata kiss shafa kanshi tayi tana murmushi ta ce " father to be " yar dariya yayi ya ce " yes yakamata ko da yaushe mahaifi yadinga jin lafiyar ɗan sa " cike da so da kaunar juna suke ta hira .

Bayan kwana biyar da sallamota anty amina ta kawo me gyaran amaren part din mommy da ba kowa aciki aka gyara aka fitar da kayan tsafinta aka konasu, aka bar musu part din anan zasuyi komai dinsu aciki zeenat ce ta fara dawuwa aka fara mata ta , anty amina tace fanan ma itama amaryace harda ita tare aka fara musu ita da zeenat.

Suhaima tadawo gombe saboda baba ne ze aurar da ita , anty amina ce tazo har gidan ta roƙi alfarma awajen mama akan ta bata aron suhaima da hairah tadauko me gyaran da zata yiwa du ka amaren gyara , dakyar mama tayarda ita gani takeyi za'a daura musu dawainiya ahaka anty amina ta lallabata ta ɗauki suhaima da hairah daga nan bayan sun fito tashiga gidansu Amira ta taroki hajiyar Amira itama duka direct part din mommy tashiga dasu . Suna ganin juna sukasa ihu suna murna harda tsalle girgiza kai anty amina tayi ta ce " yaran nan Allah yashiryeku , my feena dan Allah kidena biye musu kinga ke bake kadai bace" " tom anty amina" cewar fanan. gyara akeyi musu na gani na fada lokaci daya suka canza acikin sati biyu sunyi kyau sosai fatar su ta kara glowing se sheƙi yayi luwai_luwai, fatar su kamar ataba jini ya fito bugu da kari ga shi ba shiga rana sukeyi basa fita ko nan da kofar falo duk abinsu acikin part din sukeyi ga kamshin da jikinsu yakeyi duk inda suka zauna sesun bar kamshin su awajan . ga tsumin da ake basu suke sha , burin zeenat de yashika abin nema yasamu ci da kaza da take magana akai ,yanzu itama lokacinta yazo tanaci.

Abun duniya ya dami Mr azaad shi gani yakeyi baayi mishi adalci ba ace sati biyu cur ahanashi ganin matarshi dakuma jin ɗuminta dana ɗanshi. Duk laifin anty amina yafi gani taya zata daukar mishi mata bayan tasan yana bukatar matarshi akusa dashi, rabon da yasata a ido tun ranar da tazo tadauketa da sunan za'a musu gyaran jiki , haka yayi hakuri ya kyalesu amma kullum suna manne awaya arana zasuyi waya sau uku sau hudu harda video call.

Haka bangaren sauran angwayen ma suma basu sake saka amaren a idonsu ba sede suyita waya.

Ana daurin aure saura kwana uku , Yan beauty saloon's sukazo domin yi ma amare lallai da wankin kai , lalle da dayis akayi musu me rai da lafiya ja da baƙi hannu da ƙafa sannan aka yi musu saloon duk kansu kitso akayi musu amma banda fanan da ta ce ita kawai a gyara mata kan . sun sha gyara kam na fitan hankali .

Washe gari ana jibi daurin aure Hajiya ta turo da motar yadau Amira da suhaima dakuma hairah .
Masha Allah abangaren gidajen amare da angwayen komai yayi ready ranar daurin aure kawai ake jira domin abba da baba sunce bazaayi wata bidi'a ba saboda albarkan aure ake nema . Yan uwa na nesa da na kusa duk sun samu hallara yan Dubai sun iso haka su umma rahina da uncle kabir duk sunzo .

gidan da komai seda aka canza mishi komai sabo , babu abinda ba'a canza yazama sabo ba anyi ƙayitatciyar decorations, part din Mr azaad anzuba sabbin furniture haka part din fawwaz da areef ma anzuba furniture da duk wani abinda ake bukata, areef da Hafiz kuma sundawo part din downstairs na karban ba ki . Shirye shiryen biki akeyi ba kama hannun yaro duk sun shiga busy , anty amina da anty shayida da anty zainab sune gaba akan komai .

Safiyar jumma'at ranar daurin aure, da safe anty amina tashigo da masu aiki rike da kayayyakin da zeenat da fanan zasu saka.

misalin ƙarfe sha biyu , wanka aka sasu sukayi da ruwan madara dake dauke da sinadaren kamshi, sannan aka sake hada musu ruwan wanka da ruwan turare sukayi bayan sun fito ne aka basu kayan atamfa riga da zani rigar ɗinkin bubu ba'a musu kwalliya ba babu abinda aka shafa musu dangi nata shigowa cikin part din suna kallon amare ana jiran lokacin daurin aure , haka aka ta daukansu hotuna , ga fans din NIDA PATIENT DINA duk sun samu hallara se daukan hoto da fanan sukeyi saboda kowannesu yasamu nayin posting a status , karfe daya kuma aka sake sasu sukayi sabon wanka aka shirya su cikin hadaddun dogayen riguna na amare ,na fanan milk color na zeenat kuma white color aka musu make up sannan aka daura musu dankwali , sunyi masifar kyau .

Bangaren amare suhaima da hairah kuwa suma misalin ƙarfe sha biyu atamfa suka saka akayi ta musu hotona karfe daya aka sasu sukayi sabon wanka aka shirya su cikin breathing taking gown masu masifar kyau ga shi sun sha make up kyau kam ba'a magana kusan amare babu wanda yake kaisu kyau.
Chapter 53 · 0% Book details