← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa daga bedroom din ummi suka shiga na anty amina suka same anty amina da anty zainab suna hira sama_sama akan kujera anty shayida kuma tana kishingide akan gado ta rufe idonta kamar bacci takeyi amma idonta biyu takoma abin tausayi dan tagama waya da mijinta da baya Nigeria yatafi Egypt kenan ta kwanta tana jin duk hiran dasukeyi , gaishesu fanan tayi hade da musu taaziya zama tayi kusa da anty shayida datake jinsu hannunta fanan tarike murya asanyaye ta ce " anty shayida" bude idonta tayi akan fanan tayi mata murmushin yaqe ta ce " naam feena " gyara zama fanan tayi ta ce " anty shayida dan Allah kidena sawa kanki damuwa haka karki kamu da wata cutar daban tabbas abin da ciwo amma kiyi hakuri kimika lamarinki ga Allah komai zewuce in sha Allah mommy kuma muta binta da adduah" siraran hawaye ne yake fita daga idon anty shayida tasa hannu ta goge sosai kalaman fanan ya kwantar mata da hankali ta ce " nagode sosai feena samun yarinya me irin hankalinki awannan zamanin se antona! bawai nadamu da mutuwar mommy bane wallahi ah ah bandamu ba domin kuwa kowa ze mutu duk zamu koma ga ma haliccinmu amma ina tuna irin mugun tabon datamin wai ace mahaifiyata ce tamayar dani juya karfi da yaji , feena sau takwas fa inasamun ciki yanzu kila bazan taba samun wani cikin ba " duk ta kashe musu jiki mugun tausayinta ne ya kamasu mommy ba karamin illa tayiwa rayuwar anty shayida ba, anty amina da anty zainab duk idonsu ya taru da hawaye sun kuma ji dadin zuwan fanan domin kuwa yanzu anty shayida ta amayar da abinda yake damunta tunda akasa mata drip tayi bacci ta tashi babu wanda takeyiwa magana sede ta girgiza kai tsoro sukaji kar tashiga depression amma zuwan fanan yasa tayi magana ta amayar da abinda yake zuciyarta, mikewa Mr azaad yayi yazauna akusa dasu shima yarike dayan hannun anty shayida ya ce " meyasa zakice bazaki kara haihuwa ba ? baa cire rai daga rahamar Ubangiji kidena irin wannan maganar kinji komai yayi farko zeyi karshe " ajiyar zuciya tasauke tana fadin " nagode muku sosai kannena Allah yabarmu tare kuma in sha Allah zanyi amfani da abinda kuka fadamin " duk murmushi nadauke akan fuskansu ganin ta sa ki ranta har ana hira da ita mikewa fanan tayi tadauki kulansu ta ce " ga awara dazun nayi " jinjina mata sukayi suna yar dariya anty amina ta ce " ahh lallai feena sannunki da kokari da wannan daren yin awara kode munsamu karuwa ne ?" ta fada cike da zolaya kallon juna Mr azaad da fanan sukayi ya kashe mata ido daya itade kunya takeji se rufe ido takeyi tana buya ajikin anty shayida sosai anty shayida take dariyar fanan da take buya ajikinta dan anyi maganar ciki , bude kular anty amina tayi tana " wow irin wannan liyafar haka godiya muke " tunkafin takarasa abinda zata fada sukaga anty shayida ta toshe hancinta sannan daga baya ta tashi da gudu tafada toilet tana sheka amai kamar zata amayar da hanjin cikinta rufa mata baya sukayi banda Mr azaad daya fita a bedroom din yana kayittaciyar murmushi, taimaka mata sukayi ta gyara jikinta suka riketa suka fito aka zaunar da ita akan bed , muryanta kamar zatayi kuka ta ce " dan Allah ku rufe awaran nan please" rufewa sukayi sunayi mata sannu duk basuyi tunanin wani abu ba duk gani sukeyi kamar zazzabin da takeyi ne hakan yasa anty amina kara kiran layin doctor safiya ta sanar da ita abinda yafaru abangaren doctor safiya ta ce " Kinga dare yayi dana dawo amma yanzu kinsan me dazun nayi mantuwa adakinki kiduba zakiga handbag dina akwai PT aciki seku gwada fitsarinta " tunda doctor safiya tafara jawabi jikin anty amina yake tsuma jira kawai takeyi tagama jin abinda take fada ta aiwatar cikin sauri tadubo handbag din aikuwa taci karo da PT dauka tayi taje kusa da anty shayida ta ce " anty shayida tashi muje toilet mugwada yin abinda doctor tafada " batare da musu ba anty shayida ta mike anty Zainab ta kamata suka kaita toilet suka barta tayi fitsarin acikin wata yar container tabawa anty amina suka barta a toilet din tayi pt din bayan wasu mintuna baro_baro jan layi guda biyu suka bayyana da karfin gaske anty amina tafurta " alllahuuuuuuuu akhabarrrrrrr " dasauri tafito rike da PT strip din ahannunta, jin yanda taja kabbarah ne yasa suka taso zasu shiga toilet din sukaci karo abakin kofar toilet din sa hannu anty zainab tayi ta karba tana kallo farin ciki ne mara misiltuwa yakamata tafara " alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah ! Allah mungode maka daka nuna mana wannar rana me albarka tabbas wannan kalmar gaskiya ce da akace wani hanin ga Allah baiwa ne , Allah me yanda yaso , Allah mungode maka da sa muna cikin rayayyu dazamu sheda wannar rana me cike da albarka " rungume juna anty amina da anty zainab sukayi suna murna haka fanan ta rungumi anty amina da anty zainab, tayi matukar jin dadi sosai dakuma taya anty shayida murna .

Zuba musu ido kawai anty shayida tayi dan ita gani takeyi kamar mafarki takeyi jin wai ita akace take dauke da ciki acikin mahaifarta , hawaye masu zafine suke sauka akan kuncinta adduah takeyi Allah de yasa ba mafarki takeyi ba domin tasha yin ire_iren wayan nan mafarkan amma nayau kam fatan ta daya inma mafarkin ne Allah yasa karta tashi ta tabbata ahaka .

Rike kafadunta anty Zainab tayi itama tana hawaye ta na fadin " Allah ya amsa adduo'in mu shayida! Allah yadubeki da idon rahama bayan shekara goma sha takwas yau gashi kema kinadauke da da ajikinki kinkusa zama uwa alhamdulillah"

tabbas yanzu tasake tabbatarwa ba mafarki bane zahirine yasa ta rike hannun anty zainab da dan karfi kafin ta rungumeta sosai tana adduo'in acikin zuciyarta , raba jikinsu tayi , tayi sujjada taname godewa Allah daga hannunta sama tayi hawaye na kwarara a idonta ta ce " tabbas baa cire rai da rahamar Ubangiji, nadade da dena tunanin nima zanga jinina wacce na haifa banyi tsammanin bayan wayan nan shekarun zan zama uwa ba se yau Allah nagode maka, ya Allah ka karemin abinda ke cikina daga sharrin masu sharri kasa yafito lafiya " haka taci gaba da adduah suna amsa mata da Ameen lalubo wayarta tayi tana me dialing din number mijinta kusan missed call biyu tayi mishi be daga ba se daga baya yakirata hannunta na rawa tasa ta daga tana " alhaji albishirinka ?" yanayin yanda yaji muryanta adashe gakuma yaji ta ambaci albishir ne yasa ya ce " hajiyata meyake damunki naji muryarki haka ?" bata bashi amsar tambayar da ya mata ba tasake maimaita mishi " albishirinka?" amsawa yayi da " goro " dan yaga inbawai amsar tambayar yabata ba tofa shima bazata bashi tashi amsar ba cike da zumudi ta ce " Allah ya amsa kukanmu alhaji ni da kai nanda watanni tara masu zuwa inda rai da lafiya zamu zama iyaye " alhaji auwal aiki yakeyi a laptop yana shigar da wayansu bayanai jin wannan maganar da anty shayida ta furta mishi yasa ya tsayar da komai yaname cire wayar akunnenshi yakalli wayar dakyau sannan yamaidashi kunnenshi murya a sarkaqe ya ce " hajiyata banji me kikace ba ko Zaki iya maimaitamin ?" Duk murmushi sukayi na farin ciki sunajin abinda alhaji auwal yake fada saboda anty shayida tasa wayar a handsfree maimaita mishi tasakeyi kabbarah alh auwal yayi hade dayin sujjada yana mika godiyarshi ga Allah madaukakin sarki me kowa me komai meyin yanda yaso a lokacin da yaso . kasa magana ma yayi ji yayi yafi kowa murna awannan daren tunda ya karbi sako me matukar girma da daraja sosai sukayi waya dashi sannan yakashe .

daukan basket din duka biyu fanan tayi dan Mr azaad yatafi bedau dayan ba , taya anty shayida murna tayi sannan tayi musu seda safe ta tafi , har yanzu su fawwaz basu bar falon ba dan tun da ta tunkaro downstairs takeji muryansu suna musun ball hangota sukayi rike da basket har guda biyu tasowa areef yayi ya karbi dayar ya ajiye akan table zama tayi ta gaishesu suka amsa suma suka gaisheta kin amsawa tayi yaseer ne ya ce " antynmu barka da dare " kallon shi tayi batace komai ba dan tasan tsokana ne kawai can kuma ta ce " ayyah ya yaseer dan Allah kudena banaso " kwaikwayonta zeenat tayi tana " ayyah antynmu kema kidena kin amsawa " dariya sukayi harda ita fanan din tajefawa zeenat pillow tana " kekuma zanyi maganinki " fiitowa kowa kulan awaran shi tayi tabasu suka karba suna godiya Faisal kam ana bashi nashi ya ce " tom nikam natafi seda safenku madam nagode" yatafi . Fawwaz ne yabude nasu kulan yaga awara ne ya ce " yau akwai cin dadi irin wannan zazzafar liyafa haka antynmu" murmushi kawai tayi zeenat jin an ambaci sunan awara ne yasa tabude nata kulan ido biyu sukayi da awara ihu tayi " yessssssss wallahi awara ne" toshe kunne sukayi saboda ihun zeenat datakeyi na farin cikin ganin awara dan tunda suka dawo ta sallamar ba samu zatayi ba harta cireshi arai , kallon fanan tayi ta ce " gaskiya anty fanan kedin ta musamman ce wallahi Allah ya suburbuda miki albarka muah" takareshi tana yi mata blowing din kiss dariya kawai fanan tayi ta ce " tom yanzu de gaki ga awara amma kafin ki faraci tashi ki rakani wajan abba inkai mishi nashi " jikin zeenat har rawa yakeyi dan so takeyi sukaiwa abba sannan ta dawo tacinye nata takuma hada danasu ya fawwaz dan plan din data shirya kenan.

kallon areef fanan tayi ta ce " nikam ya areef hafiz ya farka ne ?" " Eh yatashi yayi sallah yasake komawa bacci bayan yaci abinci " areef ya sanar mata ta ce " tom ganashi nan inkun shiga ku bashi please". " to shikenan antynmu " tun kafin subar falon ma fawwaz da areef, yaseer sun faracin nasu se santin girkin sukeyi .
Chapter 42 · 0% Book details