← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 66

Sashe 56

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe sha biyun dare fanan na bacci ajikin Mr azaad naƙuda yatashi mata ranga_ranga hankali atashe yatashi yaje ya bugawa ummi yasanar da ita abinda ke faruwa dasauri tabiyo bayanshi aikuwa tana duba fanan taga naƙuda ne jinjina ikon Allah tayi wato bakwaini itama zata haifa , ita bakwaini sannan zata haifi bakwaini , tasanar da Mr azaad haihuwa ne,dauko motar yayi yazo yadauketa Fawwaz jin an tada motar ne cikin dare yasashi lekawa ta window yaga Mr azaad dauke da fanan dake murkususun azabar naƙuda ga ummi da ta fito da kayan haihuwa acikin jaka suka shiga motar aka bude musu gate , da sauri Fawwaz ya tashi suhaima ta shirya suka bi bayansu suma , da gaggawa aka karbi fanan aka shiga da ita labour room tare suka shiga da Mr azaad yana rike da hannunta se faman nishi takeyi ga gumin datakeyi , Mr azaad is very speechless ganin irin azaban da mata suke sha wajan haihuwa jiyayi kamar yamayar da ciwon kanshi tana kuka hade da addu'a shima yana hawaye tun sha biyu ake fama amma har karfe hudu na asuba bata haihu ba har karfinta ya kare tama gagara yin nishin se wasiyya take barwa Mr azaad sosai yake kuka gani yakeyi kamar tafiya zatayi tabarshi , su ummi duk suna waje suna mata addu'ar sauka lafiya duk yan uwan sun hallara a asibitin harta su mama sunzo da abba su ya usman duka sunzo . duk se safa da marwa sukeyi abakin dakin labour din ganin har shida tayi babu labarin ta haihu.

Yau garin Gombe an tashi da munanan labarai na kashe kashen da akayi kuma ake kanyi ansa tsaro ba shiga ba fita sojoji da polisawa se dirƙa sukeyi acikin duk wani asibitin dake jahar gombe saboda kisan gilan da akeyiwa masu ciki da yara jarirai ankashe mutane sun fi ɗari lamarin ba kyan gani kowa a tsorace suke ko ina labaren ne ke tashi , gashi masu aikata kisan ba'a ganinsu , wannan shine tashin hankalin da aka wayi gari dashi a jahar gombe kenan.

Shigowa sukayi cikin asibitin medical center suka fara ɓarna sunshiga dakin da ake ajiye jarirai suka fara kashe su .

Shirye shiryen yiwa fanan operation sukeyi saboda ta ƙasa haihuwa da kanta har Mr azaad da baba sunyi sign za'a shiga da ita , karfinta yadawo tafara nishi da karfi ahaka harta haihu . Ta haifi ya mace kyakkyawar gaske me matukar kama da ita kamar tayi kaki ta tofar sede farin fatan Mr azaad tadauko fara ce sol gyarasu akayi ita da babyn sannan aka bata ita tana kallonta tana murmushi hade da hawaye manna mata kiss tayi ta ce " am sorry my angel zaki taso bazakiga mahaifiyarki akusa dake ba Allah ya miki albarka nasan babanki ze kula dake sosai " sude doctors binta suke
da kallo dukda basu san ina zancen nata ya dosa ba amma tabasu tausayi , bude kofar labour room din sukayi suka fito hannunsu nadauke da baby girl din dasauri suka taso suna alhamdulillah mikawa mr azaad jaririyar sukayi karbanta yayi , nan take yaji wasu irin zafafan hawaye sun sauko daga idanunshi jiyayi kamar ayau din nan ze rasa wani barin bangare na jikinshi mannata yayi ajikinshi ya manna mata kiss a goshi, yayi mata huduba a kunne, karbanta doctor yayi yace " congratulations Mr azaad tasauka lafiya kuma itama Madam na lafiya yanzu ita babyn zamu sa ta acikin kwalba ne" sunaji suna gani aka tafi da ita suna jira suga an fito da fanan kenan sukaji ihun jama'a a asibitin suna neman taimako , mutane mata da maza se guduwa sukeyi suna ɓuya sude suna zaune kansu yadaure basu san abinda yake faruwa ba , ganin fanan sukayi tafito da gudu daga ita se rigar asibiti hannunta na zubar da jini saboda fincike calular da tayi , dasauri Mr azaad yarikota ganin bata cikin hankalinta yarikota ya na " wifey meyafaru Ina zakije ?" abirkice ta ce " yata zasu kashemin yata habiby " duk ta rudar dasu suna kokarin yin magana sukaga doctor dayatafi da babyn ya shawo kwana da mugun gudu hannunshi dauke da jaririyar gudu yakeyi kamar ranshi zefita ga jikinshi dake zubda jini duk anji mishi rauni , dasauri Mr azaad yasake fanan anty amina tariketa yaje yakarbi jaririyar ahannun doctor din yana tambayar shi meyake faruwa , doctor dake kokarin mutuwa ya ce" wasu azzalumai ne suka shigo wannan asibitin suna kashe mana mutane daga mata masu ciki zuwa kan jarirai dakuma masu shayarwa " yana gama fadin haka yafadi awajan rai yayi halinshi .

Iya tashin hankali sun shiga sunma rasa ɓuya zasuyi ne kokuma komawa gida zasuyi ga shi jama'a ne shaƙee abakin gate din asibitin jami'an tsaron sun hana kowa fita , suma da sauri suka fito compound din asibitin Mr azaad na rike da jaririyar Anty amina tarike fanan baba nadauke da auta akan kafadarshi haka Abba ma yadauki aslam, Fawwaz narike da hannun suhaima da Islam, babu yanda basuyi ba amma jami'an tsaron sunce bazeyu subar kowa yafita ba saboda awajenma ana fuskantar tashin hankalin da yafi na cikin asibitin ko ina se zubar da jini akeyi.

Kuka takeyi kamar ranta ze fita se kallon ahalin nata takeyi ita tasan yau ne ranar tafiyarta domin ayanzu ne zata fara tunkaran wa'yannan azzaluman , Mr azaad ya ce " kuzo muje mu ɓuya awani awajan" dugunzuma sukayi suka fara binshi juyawa yayi yaga fanan na tsaye , abayan su batako daga ƙafarta ba dakatawa yayi ya ce "wifey kizo muje hurry up" duk juyowa sukayi suna kallon fanan da itama su take kallo tana kuka , Abba ma sake mata magana yayi girgiza musu kai tayi tana kuka me tsuma zuciya ta ce " am sorry amma bazan biku ba ni yau ne ranar tawa tafiyar " duk jan burki sukayi lokaci daya zuciyoyinsu yafara bugawa da karfin gaske musamman ma Mr azaad da mama , se yanzu suka tuna da cewa akwai wani babban zaluncin da za'ayi da aranar fanan zata tafi , da gudu Mr azaad yaje gabanta yatsaya ya ce " common on wifey don't be so childish kizo mutafi kinji " girgiza mishi kai tayi ta ce " am sorry habiby amma yau bazaku koma gida tare dani ba " da karfi Mr azaad ya ce " noooo! hakan bazeyuba baby please karki min haka dan Allah karki tafi look at our daughter please kitsaya mu kula da ita tare dan Allah rayuwa zatayi mana zafi dani da ita in bake " yagama magana yana zubewa akan guiwansa agabanta yana kuka ga baby a hannunshi " riko hannunshi tayi ta mikar dashi ta ce" habiby inada full confidence akanka nasan zaka bawa twinkle dinmu dukkan kulawa daya kamata kayafemin inna tabayi maka wani abu sannan in twinkle ta girma ka ce mata ta yafewa mommynta, ta dinga min addu'a" girgiza kai Mr azaad kawai yake yi yana kuka shida ita ta rungume shi.

Kuka su mama sukeyi mama ji tayi zuciyarta na mata zafi sosai kamar ze fito waje ummi na kuka kowa na wajen kuka yakeyi musamman suhaima da zeenat Anty amina mazan ne kawai sukayi dauriya suna me matukar tausayawa Mr azaad, baba kam idonshi yayi ja yakasa cewa komai domin shi kullum dama da haka yake kwana aranshi saboda yasan ko ba jima ko ba ɗa ɗi yasan wannan lokacin na zuwa , Abba hawaye yataru a idonshi.

Fuskantar su fanan tayi tana share hawaye tayi folding hannayenta waje daya ta ce " mamana inasonki sosai amma haka zan tafi in barki kiyafemin sannan kitamin addu'a zantafi yaƙin da bazan dawo ba har abada , baba dan Allah kaima ka yafemin inasanka sosai, ummi kiyafemin kinji ? Abba ka yafemin zanyi kewar kyakkyawar ahalinku kudinga sani a addu'a, ya usman kaima kayafemin zeenat forgive, suhaima kiyafemin sannan ga twinkle nan karki barta tayi kukan maraicin uwa , Anty amina nagode sosai, " haka tadinga bin su tana nemar yafiyar su sannan ta koma kan yaseer ta ce" ya yaseer dan Allah karka bar habiby yashiga wani hali dan Allah ku kulamin dashi sosai karku barshi yayi kewa na sannan ku aura mishi mace ta gari wacce zata mayar mishi da gurbina sannan tazamowa twinkle uwa " dakyar take iya magana saboda kukan da yaci karfinta, sukkansu yanzu mazan sun kasa jurewa kuka kawai suke yi hatta jama'ar cikin asibitin da suka fito domin ceton rayuwarsu hankalinsu yakoma kansu sosai suka basu tausayi .

Mr azaad da ido kawai yake binta ji yayi dama Allah yadauki ranshi ayanzu ko zefi ji raradin dayakeji ya ragu .
Chapter 56 · 0% Book details