← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 66

Sashe 31

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari shida kanshi yakaita toilet ya gasa mata jiki tayi alwala yadawo da ita, ta gabatar da sallah shima yafita zuwa masallaci yau duk wanda yaga Mr azaad yasan yana cikin matsanancin farin ciki fuskanshi ma kadai ya isa ya nuna hakan dan yau fuskar asake yake bakamar kullum ba . Suna dawuwa daga masallaci yashiga wajan ummi , tana kwance alamun ba ta dade da idar da sallah ba ta kwanta hannunta rike da carbi , zama yayi yadaura kafafunta akan cinyarshi yafara mata tausa , ummi tunda taji hakan tasan wayene bude ido tayi akan Mr azaad ta ce " son!" Ya ce " barka da safiya farin ciki na " dariya ummi tayi ta ce " katashi lfy , yau kazo yiwa umminka tausa kenan dama ka dade bakamin ba " murmushi kawai yayi bece mata komai ba yaci gaba da yi mata tausan . " Ummi ! jibi zanyi tafiya inada meeting a USA kuma zan iya kaiwa wata daya ko biyu " jin haka yasa ummi cewa " tom amma kasan auren fawwaz da zeenat saura wata biyu de ko? " ya ce " nasani ummi zandawo kafin lokacin " ci gaba da magana ummi tayi" tom yanzu feena fah yakamata kutafi tare saboda inason kutsaya a dubai kuyi ko da one week ne , kaga basu san ta ba , itama ba ta san su ba! ko jiya da nayi waya da abbu seda yamin maganar. kasamu kuje " motsa leben bakinshi yayi kawai ba dan tana kallon fuskanshi ba bazatayi tunanin ya amsa ba , haka yadinga mata tausa har bakwai nasafe kafin yakoma part din su , tana kwance tana bacci tarufe duk ilahirin jikinta da blanket iya cute face dinta ne a waje , Kiran layin masu aikin gidan yayi yasanar a zo part dinshi agyara dan dama tunda fanan ta dakatar dasu take gyarawa da kanta bata sake barin sunzo mata gyara ba komai ita takeyi , shigowa wata mata tayi ta gyara ko ina fess ta tafi har time din baccinta takeyi , ganin tara yakusa ne yasa ya kwabe kayan jikinshi yarage daga shi se singlet da boxers farare , murdaddiyar jikinshi nan awaje masha Allah ga gashin jikinshi sun sake qa'wata jikin , kitchen yashiga yarike kugu yanabin ko ina da kallo yama rasa mezeyi kusan 10mint yana tsaye be gama yanke abinda ze mata na breakfast ba,wani tunani yayi yasa ya dauko frypan yadibo kwai ya kada yasa albasa da maggi kadan ya soya kwan , yasashi acikin plate ya hada mata tea me kauri da kuma slice bread din white light. Ya hada komai akan tray madedeci yafito a kitchen din se zufa yakeyi idon nan yayi jawur saboda yankan albasar da yayi yanada zafi , ajiye tray din yayi akan table sannan yahau gadon yaje dede kunnenta cikin rada ya ce " baby ki tashi kiyi breakfast na miki da kaina " tanajinshi amma baccin be sake taba yasa ta ki tashi , dagata yayi yazaunar da ita a tsakiyar gadon , kukan shagwaba tasa mishi tana dukan kirjinshi hade da turo baki rike hannayenta yayi yasa idonshi cikin nata ya ce " muje kiyi brush " daukan yar baby yamata ya sabà ta a kafadarshi sukayi bathroom, can suka fito nanma yana dauke da ita , zaunar da ita yayi akan bed ya dauko tray breakfast din ya ajiye akan bed . Kallonshi takeyi ba ko kyaftawa mamaki da tausayinshi ne yakamata ganin yanda idonshi yayi jawur tasan wannan aikin albasa ne , tayi mamaki jin shi ya mata breakfast lallai arayuwan nan nothing is permanent komai me wucewa ne in bahaka ba wai yau ita ce Mr azaad yayiwa breakfast mutumin da ko magana ma wahala yake bashi , lura da mamaki takeyi yasa ya ce " baby bari kiji ko nima na iya girkin " ya fa da yana yanko hadaddiyar kwai din yasa akan sliced bread din yakai mata baki, gutsura tayi ta ci , ba yabo ba fallasa kwai din yayi dadi balaifi, babban yatsanta tadaga alamar jinjina sannan ta ce " wow ! habiby aina ka koyi girki ?" Ya ce " zan fada miki amma ba yanzu ba" haka yadinga bata egg and bread da tea harta koshi shima yaci yakai tray din kitchen. Yadawo yana mustsuka ido kamar zeyi kuka dan seyanzu ne yakejin zafi a idonshi, kwantar da kanshi yayi akan cinyarta yana ci gaba da murza idon , ganin haka ne yasa fanan sa kyawawan hannunta akan fuskanshi ta bude dara_daran sexy eyes dinshi ta matso da bakinta setin idon tafara wura mishi iska me dadi kusan minti biyar sannan ta tsaya
Ta ce " yanzu ya denayi ko yanayi ?"

Gyara kwanciyarshi yayi kanshi na kan cinyar nata ya ce " yadena ! and na manta ban fada miki ba ,jibi zamu tafi USA daga nan kuma zamuje dubai " shafa lallausan sumar kanshi tayi tana murmushi ta ce " Allah yakaimu".

daga waya yayi yasa akunne yafara magana " okay ganin zuwa " daga kanshi yayi a cinyarta ya ce " baby inazuwa " gyada mishi kai tayi yafice yabar mata wayarshi tana buga game.

tana kwance tana game yashigo bedroom din hannunshi da wata yar siririyar qyalle fari me kyau daga dan bakin kofa yatsaya ya ce " baby zaki iya tafiya ?" ajiye wayar tayi ta sauko akan gadon , dagashi har ita basuyi tsammanin zata iya taka kafar ba saboda jiya har kuka tayi mishi kafarta yarike bazata iya tafiya ba amma yau da ikon Allah taji yasake , ahankali take tafiya jikinta sanye da jallabiyarsa daya mata tsayi da girma sosai kanta kuma da pink din gyale ta daurashi , ta iso gabanshi murmushi yayi yasa wannan yar qyallen ya daure mata ido dashi sannan ya dafa kafadarta suna tafiya ahankali hankali suna zuwa wajan staircase yadagata har suka sauko main falo areef ne da zeenat kawai suke zaune sukaga fitowarsu , direta yayi akan kafafunta acikin falon sukaci gaba da tafiya suna tunkarar kofan barin part din.

_______ ta ce " wayyo habiby bamu iso ba har yanzu ?" ya ce " yes saura kadan " haka har suka iso cikin compound din, sa hannunshi yayi acikin aljihu yafito da wata hadaddiyar car key yadamka mata a hannunta rikesu tayi dukda batasan meye bane idonta arufe , warware mata dauren qyallen yayi daga idonta ya koma gefe yatsaya ya harde hannunshi ya ce " surprise" Slowly tabude manyan idonta tafara ganin dishi_dishi sauke idonta tayi akan . Brand_new Range Rover SV version white color wanda kudinshi yakai kimanin $234,000 dollars akudin Nigeria kuwa yakai kimanin naira million dari biyu da hamsin ( 250 million) , motar ce da ta amsa sunanta se wanda ya isa manyan masu kudine kawai suke iya hawar wannar motar, jikin motar an mata kwalliya da jan balloons( balon balon) da flowers jajaye , kallon motar takeyi ba qaqqautawa sannan ta kalli car key hannunta.
kallonshi tayi tana neman karin bayani juyawa tayi tana kallonshi murya na rawa ta ce " habiby....." girgiza mata kai yayi alamun kartace komai yana me nuna mata jikin motar da akabar envelope me kyau sosai kamar IV , dasauri ta isa jikin motar ta sa hannu ta ciro envelope din hannunta har rawa yakeyi wajan bude wa paper ne ajiki anyi rubutu da jan alkalami an rubuta " MY FEELINGS FOR YOU ARE VERY STRONG! YOU HOLD A SPECIAL PLACE IN MY HEART BABY, I love you so much . Here is a small gift for you, hope you liked it "
Chapter 31 · 0% Book details