← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu jibga_jingar motoci guda hudu sukazo daukar Mr azaad and Mrs azaad kuma dukkansu turawa ne sanye da bakaken suits , har suka sauko daga jirgin fanan bata sani ba hankalinta na kan airport dan ya burgeta sosai , cikin girmamawa turawan nan suke gaishesu beko kallesu ba daya daga cikinsu yabude musu murfin motar tsakiya Mr azaad yashiga dauke da fanan a hannunshi kwantar da ita yayi akan seat yadaura kanta akan cinyar shi shafa fuskanta yayi ya ce " sannu ko wifey munkusa isa gida " da muryanta da baya fita ta ce " to habiby" tafiya sukeyi akan titi slowly kamar wayanda suka dauko sarki ko shugaban kasa har suka iso wani hadedden waje me matukar girman gaske wani katon sign bot kamar tv yana fitar da rubutu da colors kala_kala yana rubuta ' welcome to las Vegas ' babban birnin las Vegas kenan dake cikin kasar america .

Horn sukayi a tangamemen gida masu gadi suka bude aljannar duniyar gidan daya kasance daya daga cikin manyan gidaje a las Vegas komai na more rayuwa akwaishi awannan gidan akashe masa daula iya daula,gidan da ya yakasance mallakin Mr azaad, bude musu gate akayi suka shiga fanan kamar bakauyiya haka takoma domin gidansu Mr azaad na Nigeria bekai wannan kyau ba dukda cewa shima dankararriyar gida amma wannan ya hadu iya haduwa aikunsan banbancin gidajen turai dana gida Najeriya, tsayawa fada muku kyaun gidan ɓa ta ɓaki ne buɗe musu motar akayi yafito dauke da ita ahannunshi, turawa dake aiki a gidan se ɗiban gaisuwa sukeyi haka yashiga da ita cikin gidan kai tsaye wani ƙayitatciyar bedroom yashiga ya kwantar da ita akan makeken gado, luf tayi tana kallonshi daga mata gira yayi alamar tambaya girgiza kai tayi , dukunkune jikinta tayi waje daya saboda sanyi da takeji ganin haka yasa Mr azaad kashe ac sannan ya rufa mata bargo , kayan jikinshi ya cire yashiga toilet yayi wanka da alwala,yafito yasamu harta fara bacci batare da yasa kaya ba yana ɗaure da towel yahau kan makekiyar gadon , yaye bargon yayi yaɗagota yafara cire mata kayan jikinta , bacci ne a idonta duk abinda yakeyi tanajinshi amma takasa koda bude idonta ne haka yadauketa yashiga toilet da ita yamata wanka da ruwan zafi tayi alwala sannan yanaɗota a towel yakwantar da ita akan gadon sosai taji dadin jikinta.

Kitchen din dake cikin part din yashiga ya haɗa mata cornflakes yakawo mata hartayi nisa abacci babu yanda ya iya dole seya tasheta tasa wani abu acikinta baze barta ta kwanta haka ba zama yayi agefenta ya ce " wifey kitashi kisha cornflakes seki koma baccin " tana jinshi sama_sama hakan yasa ta make kafada tare da turo mishi dan karamin baƙinta , murmushi yayi yasa hannu yadagota zama tayi tana marairaicewa kamar wacce tasha maganin bacci dakyar ta iya cewa " habiiiiibyyyyy kabarrrrni inyiiiiiii bacciiiii " yanda take jan maganar nata seda yaji tsigan jikinshi yatashi musamman yanda takira shi se dayaji har cikin ranshi , fa ra bata yayi abaki harta shanye duka batama san tashanye ba kwanciya take kokarin yi yarikota ya ce " ki bari muyi sallah seki kwanta" dressing room yashiga yadauko mata wandon da riga na bacci masu kauri se katon jacket din rigar sanyi domin ana sanyi sosai bude trolley dinta yayi yafito mata da hijab , shima jallabiya yasaka , sannan yadawo bedroom din, sa mata kayan yayi ya shimfida musu sallaya jansu yayi sukayi sallolin da ake binsu bayan sun idar tayi addu'a ta haye gado ta kwanta se bacci murmushi kawai Mr azaad yayi shima agajiyen yake hakan yasa yakashe wutar dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo hade da musu addu'a bacci .

To sekuma gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya .

Waiting for your comments and share fisabilillahi 🙏.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
( Yar lelen Jarumai)

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚

⚜️📚 J. W. A 📚🖋️

Gargadi....
Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin kuma yabimin hakkina.

PAGE 6️⃣0️⃣

NIGERIA

Adamawa Yola

Shigowa lukman yayi yadawo daga office yasamu nusaiba zaune tana chatting dinta hankali kwance tanajin shigowar shi amma ko dago kai batayi ta kalleshi ba balle yasa ran zatace mishi sannu da dawuwa girgiza kai yayi kawai yana mata fatan shiriya domin tunda akayi aurensu yake fuskantar bacin rai daga wajan nusaiba betaba ce mata uffan ba balle yabiye mata haka zata tsaya ta mishi rashin kunya iya isarta ko kadan bata ganin girmanshi ta renashi ga tsanar datayi mishi tunda akayi auren wani abu be taba shiga tsakaninsu ba a matsayin miji da mata , bata daga tsinke bata da aikinyi se chatting da kawayenta ko girki bata tabayi mishi ba kullum a restaurant yakecin abinci duk da akwai me aiki agidan amma nusaiba tahanata shiga mata kitchen bakomai ne yayi tasiri awajan nusaiba ba fa ce huɗubar da mahaifiyarta madina tayi mata.

wanka yayi yafito yazauna afalon har lokacin tana nan a inda yabarta bata motsa ba se hira takeyi da kawayenta a whatsApp, zuba mata ido yayi yana kallonta kamar wani me nazarin wani abu wata uwar harara nusaiba ta watsa mishi lokacin da ta ankara yana kallonta sannan ta ce " meye haka ? Kazo kawani sani agaba kana kallo mtsssw " ta gama maganar hade da jan doguwar tsaki kamar wacce take magana da sa'anta, ran lukman yabaci sosai da tsakin dataja mishi ya ce " nusaiba ni kika jawa tsaki?" Kallon tara saura takwas tayi mishi tana ƙaɗa kafa ta ce" ehh kai nayiwa wannan tsakin lukman! nace kai nayiwa kadau mataki , inka isa cikekken namiji ka sakeni mara zuciya kawai " murmushi me ciwo lukman yayi kafin ya ce" nusaiba kenan kice gaba da barin duniya tana ruɗarki da kuma hure miki kunne duk abinda zakiyi sede kiyi amma bazan taba sakin kiba wannan alkawarine nadaukawa kawu , amma kisani nikaina bawai kaunarki nakeyi ba kawai de so ne na yan uwantaka bayanshi babu komai araina , tun yanzu Yakamata kizubar da mukaman yakinki ki karbi wannan auren namu hannu bibbiyu tun kafin lokaci yakure miki " duk maganar dayakeyi mata nan cikin sanyin murya yakeyinsa dukda kuwa ranshi abace yake lukman yana da sanyin hali sosai , haka yatashi yabarta a falon tana cika tana batsewa , gani takeyi babu wanda aka cuta sama da ita za'a aura mata lukman ita ai ba sanshi takeyi ba kuma dole taci gaba da yi mishi abinda Madina take fada mata domin ta wannan Hanyar ce kadai zasu samu ya saketa.

Yau de Allah yayi dare gari ya waye se yau Mr azaad yabawa su spider umarnin ƙyale alh Ibrahim tijjani su da kansu suka fitar dashi wajan gari suka hankaɗoshi waje yafadi aƙasa timm kamar wani kayan wanki, duk yabi ya yamutse yafita a hayyacinshi ya canza kamanin wannan tumbin nan nashi duk seda ya sa ce dan baƙar azaban dayasha tabbas yaji jiki bana wasa ba, dede da yatsun hannunshi dakyar yake iya dagawa fuskan nan ya kumbura sumtum ya tara jini musamman idonshi , yana yashe akan hanya motar ambulance yazo suka dauke shi suka wuce asibiti dashi .

_____ jikinta na matukar rawa take magana tana nunashi da yar yatsa ta ce " bazeyuba ! baze taba yiwuwa ba ka cuceni ! in kyaleka? baka isaba kayi kadan amjad" wanda takira da suna amjad yana zaune yazuba mata ido hankalinshi kwance ya ce " keee aneesa karki yarda kice zaki nunamin akuyanci koɗan kinga nayi shuru na ƙyaleki ne ? Ni bance kin cuceni ba se kece zakice na cuceki" aneesa dake tsaye a kanshi tana huce idonta yayi ja sosai duk alamu sun nuna kuka tasha ta koshi ta nunashi da yatsa tana fadin " kayi kaɗan ka shafamin cuta sannan ka hanani magana HIV positive fah nagani toma dakake cewa bakai ka shafamin ba agidan ubanwa nasamu to? iyeeh nace agidan ubanwa nasamu inbakai kasamun ba?" murmushi yayi irin nasu na gogaggun yan duniya yabata amsa da " ai badani kadai kike yawon tazubar ɗinki ba , waye besan ke karuwa bace zaki zo ki dameni kina cemin nina shafa miki HIV kije can kinemo sauran abokan holewarki " kukan kura aneesa tayi ta cukumi kwalar rigar amjad afusace ta ce " amjad nikake fadawa haka halaccin dazakamin kenan , kaine na mijin daya fara amfani dani a matsayin virgin , kyautar budurcina fah nayi maka amma yau kaine kake cewa wai ai bakai kadai kake amfani dani ba , to naji bakai kadai bane amma ai kasani kai da ya ne kake sex dani batare da condom ba kaga kuwa dole kaine ka shafamin HIV " fincike hannunta daga kan rigarshi yayi ya ce " karamar yar iska kema yanzu da kanki kinfada ai bani daya kike sex ba to wallahi nasakejin kince nine nashafa miki HIV ranki se yayi mugun ɓaci "
Azafafe tadau handbag dinta da wayoyinta tafita a hotel room din tana me danasanin sanin amjad a rayuwar ta.

SATANIC
Chapter 44 · 0% Book details