Sashe 18
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tashi tayi ta zauna tana murza idonta kallonta tayi a dakin Mr azaad kuma babu shi aciki tuna abinda yafaru tayi danna wayarshi da ta gani a kasan pillow tayi karfe 5:40am ta gani batayi mamakin ganin haka ba tashi tayi tashiga toilet tayi wanka da alwala dressing room dinshi ta shiga bangaren jallabiya taje ta dau arche color tasaka yawa yamata ganin hijab dinta tayi akan kujera dauka tayi, tayi sallah tana zaune tana azkar ya shigo ya zauna akan kujera yazuba mata ido harta idar, juyawa tayi ta kalleshi kafin tace " Ina kwana Mr azaad" batayi tsammanin ze amsa ba taji yace " lafiya ! tashi kizo" tashi tayi taje ta tsaya a jikin kujeran da yake zaune , " malama ki zauna mana kin tsaya min akai" zama tayi dan tasan halinshi yanzu se ya fara , bayan ta zauna ne yake tambayarta " ko zan iya sanin fa'idan shan jininki da kika bar zeenat tayi?" bashi amsa tayi da " Mr azaad ka rigada kasan nidin wacece , dakuma abinda nake dauke dashi ina da ya kinin shan jinina da tayi ze iya fitar da maitar ajikinta" cike da gamsuwa da maganarta hadi da kaunarta yace " Allah yasa " ta amsa mishi da " ameen " satan kallonshi tayi suka hada ido itama ita yake kallo gyara zama yayi yace" to miye na kallon kuma " girgiza kai tayi . Kwantar da kanta tayi a kafadarshi ta lumshe ido kamar tana bacci tana shakar daddadar kamshin turarenshi , " fanannnn!" batare da ta Bude ido ko ta tashi ba tace " naam" shafa kumatunta yayi ya dan jashi kadan runtse ido tayi saboda yamata zafi ," fanannnn meyasa kike boyemin abinda ke ranki ?" cewar Mr azaad da har lokacin yana shafa mata kumatu , tashi tayi daga jikinshi ta zauna suna kallon juna tace " Mr azaad miye nake boyewa din ?" kwantar da kanshi yayi a jikin kujeran be sake ce mata komai ba ganin haka yasa fanan mikewa zata tafi bedroom dinta rike hannunta yayi yace " karki tafi please" kaman wani bako haka take kallonshi wai yau Mr azaad ne yake ce mata please anya ba mafarki takeyi ba kuwa, janyo hannunta yayi tafado jikinshi sunfi 5mint kafin ya sauke ajiyar zuciya yace " fanannnn am sorry for all mistakes nasan na miki Abubuwa da dama kiyi hakuri na miki alkawari hakan baze sake faruwa ba " sosai idonta ke fitar da ruwan hawaye tun tana hawaye harta fara shesheka azuciyarta tana godewa Allah da yasa Mr azaad ya gane abinda yake mata ba dede bane dukda bata taba rikeshi arai ba son da take mishi yasa bata ganin laifinshi . rungumota yayi ajikinshi yana rarrashinta dede kunnenta yakawo pink libs dinshi wura mata iska yayi acikin kunne da yasa taji tsigan jikinta ya tashi kafin ahankali cikin rada yace " baby be with me for the rest of my life! I love you " cak duk wata ma gudanar jinin jikinta seda yatsaya yadena aiki na wasu lokuta jin abinda ko da amafarkin wasa bata taba tsammanin ji ba hawayen farin ciki ne yafara saukowa daga idonta runtse idon tayi sosai tana rokon Allah yasa koda a mafarki nake Allah karkasa in tashi , haka ya dinga fada mata daddan kalamai dashi kanshi besan ya akayi ya iya su ba kawai abinda yasani duk abinda yafada mata daga cikin zuciyarshi yafito, rungumeshi tayi gam muryanta na shake tana kuka hade da dariya tace " I love you too Mr azaad inasanka sosai" raba jikinsu yayi ya manna mata kiss a goshi tare da fadin " Allah ya miki albarka my wifey" kallon cikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hawaye me zafine ya gangaro kuncinta hannu yasa ya share matashi yana girgiza mata kai sannan yace" hawaye bashida gurbi a cikin rayuwarki har inde ina tare dake ! adah nabari kinyi amma banda yanzu domin kuwa inya sake saukowa zan hukuntashi " dariya tayi tana kwanciya ajikinshi tayi lamo .
______ bacci suka koma se 11 suka tashi komawa bedroom dinta tayi sakeyin wanka tayi ta shirya cikin atampa super Holland me purple color se touch din maroon da fari, dinkin doguwar rigace pencil gown me dogon hannu kasan hannun an mishi play wuyan rigar kuma adan bude yake batayi kwalliya sosai ba kawai powder tashafa se kwalli da libstick , dankunne da sarka tasa na gold tayi dauri me v feshe jikinta tayi da turarurruka masu dadi dakuma sanyayyar kamshi hills tasaka a kafarta maroon sak tafito a amarya tayi kyau sosai kamar wacce zataje gasar kyau gashi kayan sun matseta nafitan hankali duk wani shape dinta seda yafito fili . yau fess takejin ranta ji takeyi babu wanda yakaita farin ciki a irin wannar rana saboda wanda take matukar so shima yana santa, kallon kanta tayi a mirror ta kashe ido daya tare da fadin " excellent" knocking tayi yabata izinin shigowa, samunshi tayi yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya three quarter dark blue yasa da kuma riga armless baka waya yakeyi da yaseer dake tambayar shi jikin zeenat kamshin turarenta ne ya sanar dashi isowarta kallonta yayi da narkakkun idonshi kasa magana yayi kawai yayi hanging din kiran murmushi dauke a fuskanta, tafiya takeyi ahankali kamar wata me tausayin kasan, har izuwa lokacin be kawar da idonshi akanta ba cike da kissa ta zauna agefenshi ta shagwabe fuska tace " Mr azaad wannan kallon fah?" cize libs dinshi yayi kafin yace " to laifine dan na kalli matata?" rufe fuskanta tayi ajikinshi tana dariya dagota yayi yatsurawa libs dinta ido dayasha man baki matso da fuskanshi yayi daff danata ahankali ta lumshe manyan idanunta,hade bakinsu yayi waje daya yasakar mata hot kiss sannan yadago yana kallonta yace " baby kinyi kyau sosai" dadi ne taji yarufeta jin yabon daya mata tana kokarin yin magana sukaji anyi knocking tare da fadin " sir your food is ready" beyi magana ba sukaji alamar wanda yakawo abinci ya fita tashi sukayi sukaje falon sukayi breakfast.