Sashe 41
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
zeenat ta ce " anty firdausi nide kibarmin junior dinkin nan wallahi kyau yakemin " hararanta fanan tayi ta ce " narigaki malama tun Yana ciki nace inaso " sa hannu zeenat tayi tadauki junior akan cinyar fanan tadaurashi akan nata cinyar ta ce " junior kace mata ni kakeso kaji" kamar wata me magana da babba , shide junior se dariya yake mata fanan ta ce " Allah yashiryeki zeenat yanzu junior kikewa magana?" gyada kai tayi dariya anty firdausi tayi ganin drama zeenat da fanan akan junior , kallon fanan anty firdausi tayi ta ce" muje zamuyi magana " tayi gaba fanan tabita abaya zama sukayi akan gadonta ta kalli fanan dakyau ta ce " fatan de yanzu komai normal keda mijinki babu wata damuwa ko?" ta ce " eh anty firdausi komai alhamdulillah " hakan yayiwa anty firdausi dadi , ta bata shawarwari da koya mata wasu abubuwan bude wata karamar wardrobe tayi tafito mata da magunguna dakuma mayukan gyaran jiki, dasu turarurruka masu yawa ta saka mata su a yar jaka me kyau sannan ta fada mata yanda zatayi amfani dasu godiya fanan tayi mata suna cikin hira taga Kiran Mr azaad dagawa tayi , ya ce" dare yayi kuzo mutafi " yana gama fadin haka yakatse kiran, fitowa sukayi tare ita da anty firdausi suka samesu a falo sundawo ga zeenat dake wasa da junior, mikawa anty firdausi junior tayi tana " senazo karbanshi ya yini awajena " daddyn junior ya ce " to shikenan sekinzo" haka suka rakasu packing space daddy junior nayi musu godiya sosai domin ya matukar jin dadin ziyarar da suka kawo mishi , sukayi musu adduah Allah yakiyaye hanya, suna tafiya akan hanya daga can nesa zeenat ta hango me soya awara murya asanyaye ta ce " ayyah ya azaad dan Allah katsaya agun me awaran can " juyowa yayi yawatsa mata banza kallo ya ce " wato harkin mata da abinda yafaru dake ko ? baki daddara bako ? kisakemin maganar wani abun akan titi kiga iKon Allah" yafada yana kara wurga mata harara shuru bata sake cewa komai ba jikinta yayi sanyi , amma harga Allah kwadayin awaran take , tunkafin zeenat tahango me tuyar awarar fanan ta ganta tana kokarin yi mishi magana se zeenat tarigata jin amsar dayabawa zeenat ne yasa tayi shuru takama bakinta amma ita yanzu hakama ji takeyi in bataci awara ba bazata iya bacci ba , haka suka wuce masu suyar awaran sunaji suna gani Mr azaad ya hanasu siya .
8:12pm dede suka shigo gida zeenat ce tafara fita a motar tashiga gida fita yayi harya fara tafiya yajuya ze riko hannunta yaga wayam batama fito ba tana cikin motar komawa yayi yabude mata murfin motar still bata fito ba kanta akasa tana wasa da yatsunta, sa hannu yayi yadago fuskanta zaro ido yayi ganin yanda fuskanta yayi jaga_jaga da hawaye , mamaki yafara meye aka mata take irin wannan kukan riko hannunta yayi ya ce " baby meyafaru kike irin wannan kukar" kamar wacce take jira yayi magana takara volume din kukanta harda shesheka, tsugunawa yayi agabanta yana rike da hannun nata yazubawa sarautar Allah ido kuka takeyi bil hakki kamar wacce akawa mutuwa tambayarta yayi ko wani abun akamata tayi mishi shuru lallashinta yakeyi Amma kamar zugata yakeyi, haryama rasa me zece mata kawai yazuba mata idanunshi, seda tayi kukanta son ranta sannan tayi shuru da kanta har lokacin Mr azaad yana tsugune agabanta rike da hannunta, ganin tayi shuru ne yasa ya ce " sorry wifey fadamin meye mekikeso " ajiyar zuciya tasauke tagoge fuskanta da hijab murya ashagwabe ta ce " bakai bane ba" nuna kanshi yayi da yatsa ya ce " nikuma menayi miki?" turo baki tayi ta ce " bakai bane ba kace bazaa siya awara ba bayan inason ci" sake hannunta yayi yadafe kanshi aranshi yana" ya salam yanzu dama akan wannan abun tatsaya tana kuka lallai mata rigimammune " tsaban yanda yake cike da mamaki hade da al ajabi gagara cewa komai yayi se binta da kallo dayakeyi sake fashewa da kuka tayi ganin yazuba mata ido kuma shi bece mata komai ba , zaro wayarsa yayi ya kira layin faisal bugu biyu yadaga abangaren faisal yagaishe shi be ko amsa gaisuwar ba ya ce " akwai wani abu ana siyarwa akan titi please kasiyowa wifey yanzu " daurewa faisal kai yayi domin shi besan tankamemen abinda zaa siyoba tunda bawai yafada mishi sunan abun bane ya ce " sir to meye sunan abinda zaa siyo din ?" shuru fanan tayi tana aika mishi da harara jin yatsaya yanawa faisal kwantancen abinda shikanshi be sani ba bekuma fadi sunan ba , yafi tsawon minti 10 yanawa faisal kwantancen amma be gane ba gashi Mr azaad ya manta sunan abun Kuma be tambayi fanan ba, iya cika fanan ta cika tazo har wuya takaici kamar ta tashi tabar mishi wajan shi besan abu ba Kuma baze tambaya afada mishi sunan ba gashi dare karayi yakeyi , sa hannunta tayi ta zare wayar akunnenshi tasa a handsfree, sallama tayi jin muryanta yasa faisal gaisheta, " faisal awara ne zaka siyo , amma danye wanda baa soya ba dan Allah" tafada tana murgudawa Mr azaad baki murmushi yayi dan yasan acike take jira takeyi yace wani abun ta taso mishi da sabon rigima . faisal ya ce " madam eh zaa samu dan kanwata ma tanayi na order yanzu haka bari in karbo miki " yafada yana kunshe dariya wato mace de babu yanda bata juya namiji gashi oganshi lokaci daya matarshi tajuya mishi lissafi mutumin da maganar mint 2 ma bayi yakeyi ba amma yau dake tanason abu yatsaya yana bayani kusan na 10mint mata mutanen mu. godiya tayi mishi takatse kiran tana mika mishi wayarshi karba yayi yana kallon fuskanta da ta daureshi ita dole fushi takeyi bata kalli inda yake ba tadauki jakar da mama tabata dana wanda anty firdausi tabata tayi gaba ta barshi abaya , tafiya takeyi batako juyo takalleshi ba balle tasan yana binta abaya hannu daya yasa yadagata sama kamar wata yar tsana , mutsu_mutsu tafarayi na sede ya ajiyeta akasa ta tafi da kafarta be saurareta ba seda suka kusan isowa falo sannan yasauketa yarike hannunta suka shiga falon ba kowa aciki, kowa na part dinshi , part dinsu suka shiga zama fanan tayi akan kujeran falo tana " washh nagaji " tafada tana bude fashion bag din da mama tabasu ciro hadaddiyar liffaya tayi me matukar kyau multi color jikin liffayan yasha manyan stones bakaramin kyau yayiwa Mr azaad ba, har imagine kayan yakeyi ajikin fanan intasa ,shafa liffayan yayi ya ce " wifey kayan nan zasuyi miki kyau sosai" har ranta taji dadi yanda ya yabi kayan dukda inde tayi kwalliya seya yabi kayan dakuma irin kyaun da tayi. maida kayan cikin gidanshi tayi ta ajiye agefe kallonta yayi ya ce " wifey amma ai nima zaa ban tsumin in sha ko ?" Kallonshi takeyi bako kyaftawar ido mamaki ne yakusa sumar da ita aina yaji maganar tsumi kuma saboda tasan itade bata mishi ba sannan bawai bude jakar da anty firdausi tabata tayi ba , cikin inda_inda ta ce " habiby tsumi kuma?" dariya taso bashi amma yafuske ya ce " yes up course tsumi kuma inzakisha kimin magana musha tare " kunya kamar fanan ta nutse kasa tama rasa mezatace mishi , dariya kasa_kasa Mr azaad yakeyi dan tun dawuwarsu daga masallaci suna kokarin shiga falon gidan anty firdausi yaji duk hiran da sukeyi murmushi yayi aranshi ya ce " Allah de ya biyaki maman junior" knocking sukaji Mr azaad yace ashigo Faisal ne yashigo hannunshi rike da food flask me girma ya gaishesu hade da ajiyewa akan table ya musu sallama ze tafi fanan ta ce " ah ah katsaya agama soya awaran " dadi sosai faisal yaji yana kara yabon matar oganshi nashi da irin kirkinta fita yayi zuwa main falo dan shigowarshi yabar zeenat da yaseer suna hira se fawwaz da areef sukuma suna kallon ball zama yayi ya jonasu shima. daukan kulan tayi zuwa kitchen taname jin dadin samun danyen awaran da akayi gyarashi tayi sosai ta soyashi sannan tayi sauce din hanta me dadin gaske, ta dafa kwai .
ba ita tagama ba se karfe tara saura kuloli madedeta ta dibo tasawa ummi nata tasawa abba nashi sannan se nata da Mr azaad, tasan su anty Amina suna tare dasu anty shayida tasa musu , se su fawwaz da areef da zeenat se kuma tasawa faisal dakuma hafiz nashi duk da haka awaran yarage nan ta sawa masu gadi da securities din gidan zuba kulolin tayi acikin basket taga basu shiga duka ba dauko wani basket din tayi tasa sauran kulan tafito rike da basket duka biyu a hannunta se nishi takeyi, tunda tafito daga kitchen Mr azaad yake kallonta yanayin ka zar _ ka zar dinta batada gandan aiki she's not that lazy yana burgeshi amma bayason tadinga shan wahala. tunkafin takaraso yamike yakarbi basket daya ahannunta ajiyar zuciya tayi saboda daukan basket din datayi setaji duk ta gaji sosai kamar wacce tadau buhun cement ta ce " thanks habiby dama downstairs zanyi amma mufara zuwa part din ummi " bece komai ba yariko hannunta dan yaga kamar agajiye take sunje sunyi ziyara sannan tana dawuwa tashiga kitchen yanzu kuma zata kai musu . tausayi tabashi dan seyanzu yake ganin laifin kanshi dan da tun farko ya tsaya an siya awaran da yanzu awuce layin amma shi yaji tsoron hakan ne saboda abinda yataba faruwa da zeenat, part din ummi suka shiga nan ma ba kowa bedroom dinta sukayi sallama ta amsa hade da cewa " ku shigo " shigowa sukayi har a lokacin hannunsu na sarke dana juna murmushi ummi tayi ganin sune zama sukayi akan kujera fanan ta gaisheta hade da mata taaziya amsawa ummi tayi ta ce " ya kika baro gidan naku fatan kowa lafiya? "
" lafiya lau ummi " fanan ta fada tana fito da food flask madedeci dake dauke da awara da sauce din hanta da dafaffen kwai ta ce " ummi ga awara " ta karishe maganar tana ajiyewa akan center table murmushi ummi tayi " ahh lallai my feena sannu da kokari yanzu awannan daren kika tsaya yin awara kindebo gajiya sannu ko kidena wahala kinji " ummi ta fada tana kallon fanan din da ta sunkuyar dakai kasa tana murmushi zatayi magana kenan Mr azaad yarigata da fadin " ai yau ita da zeenat sekinga yanda suka dameni akan awaran nikuma naki saya akan titi gudun abinda yafaru yasake faruwa amma wannan feenan naki wallahi sekinga kukan datakeyi min akai " yagama magana yana jan kumatun fanan dake muntsininshi , dariya sosai ummi tayi dantaga muntsin da fanan takeyiwa Mr azaad sake kallon fanan din tayi dakyau taga tayi fresh sosai tayi kiba tunani tafarayi kode fanan nada ciki saboda wasu sign din datagani amma bari zatayiwa Mr azaad magana yakaita asibiti agwada Allah yasa cikin ne dasunyi matukar murna , mikewa sukayi zasu tafi ummi ta ce " nagode miki sosai daughter dama nadade banci awara ba Allah yamiki albarka" amsawa fanan tayi da " ameen ameen ummina" suka tafi harsuka fita tana binsu da kallo taname godewa Allah daya nuna mata matar Mr azaad dan babu wanda yayi tunanin zeyi aure nan kusa kafin ya auri fanan ko andago maganar aneesa seya nemi hanyar da yasa se an kwantar da maganar finally gashi yanzu yayi aure kuma alhamdulillah suna farin ciki da matarshi bude kulan awaran ummi tayi kamshi yabugi hancinta faracin awaran tayi tana jinjina kai dan bata tabacin awara me dadin wannan ba haka tagama se Santi takeyi tana sawa fanan albarka.