← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 66

Sashe 17

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe 3 mommy ta dawo gidan ta kashe yara biyar 5 takai kungiya, tana shigowa part dinta tafara jin karnin jini mamaki ne yakamata bin direction din inda karnin jinin ke tashi tayi tafiya takeyi har dakin Mansoor dake kwance babu rai ajikinshi babu koda tsokan nama sede kashi uwar ihu da kururuwa tayi wanda yacika gidan yayi sanadiyar tashin kowa daga bacci har rige_rige sukeyi suka fito kaff dinsu afalon ummi suka hadu suna tambayar junansu meyafaru tsaban rudewa dukkansu da kayan bacci suka fito buga kofar falon akeyi kamar zaa ballata babu ko tsoro Mr azaad yaje ya bude bangaje shi mommy tayi ta nufi abba ta rikeshi kam tana kuka kamar ranta zefita, duk ta daburtar dasu sun rasa gane abinda yake faruwa jijigata abba yayi saboda ta dawo cikin nutsuwarta cikin tashin hankali tace " muhammad sun kasheshi sun kashe Mansoor sun kashemin dana Mansoor" innalillahi wainna ilaijiraji unnn zufa ne yafara yanko musu jin kalamanta saketa abba yayi yawuce part dinta yau ne rana ta farko da yasanya kafa a part dinta tun bayan shekara 12 saboda ya dade da sanin wacece mommy har dakin mansoor din yashiga runtse ido yayi lokacin da yayi arba da gawar mansoor ko kuma in ce gwarangwal din mansoor bakyaun gani, shigowa su ummi sukayi suma duk kallo daya sukawa gawar suka kauda kai, yau kam sun shiga matsanancinyar tashin hankali , babu abinda kirjin fanan yakeyi fa ce bugawa da karfi_karfi tsoronta daya shine kar zargin da takeyi yazama gaskiya akan zeenat saboda yanzu tasake samun hujja ganin dan kunnenta yashe akasan gadon sa kafa tayi ta bigeshi yashige can kasan gadon batare da kowa ya gani ba. bedsheet Mr azaad yasa ya rufe mansoor dashi duk karfin zuciyarshi da taurin zuciya seda yaji tsigan jikinshi yatashi barinma da yaga fuskan mansoor kaf an kwakule komai harta ido an cire , fita sukayi daga dakin zuciyarsu a karye sosai tausayin mommy yakamasu .
haka suka kwana a part din mommy batare da sun runtsu ba yanda sukaga dare haka suka ga rana .
Sallah suka tafi a masallaci Abba yafadawa liman akwai jana'iza agidanshi dan shi ya rasu , liman yayi sanarwa a masallaci mutane suka tayi musu taaziya.
haka akayi jana'izar mansoor aka kaishi gidanshi na gaskiya kowa na binshi da adduah Allah yaji kanshi , mommy kam yar karamar hauka ne kawai batayi saboda duk duniyar nan babu dan adam din da takeso sama da danta mansoor saboda halinsu yazo daya duk wani mugun nufinta bata taba tunkarar shi ba , ko magana bata iya yi balle ta karbi gaisuwar , su anty shayida da anty zainab da anty amina duk sunzo , me martaba da duk jamaar masarauta sunzo, haka su mama suma sunzo sun musu taaziya sun koma sosai mutuwar mansoor ya taba su fawwaz dukda bawani shiga harkanshi sukeyi ba saboda rashin kunyar dayake musu baya ganin kowa da mutunci kuma ko sun dakeshi hakan baze hana yakara musu wani rashin kunyar ba , haka zeje yafadawa mommy ita kuma tashigo part dinsu ta musu rashin mutunci tayi gaba .
duk wannan gaisuwan da akeyi da zaman makoki ko idon zeenat baa gani ba ko lekasu batayi ba tana can ta kulle kanta adaki tana kukan nadaman halin dataga kanta aciki abin na mugun damunta gashi kuma bata isa tafadawa kowa ba kugin yunwa cikinta yafara nan take halittar jikinta yafara sauyawa dogayen hakwara da yatsunta sun fito idonta yarine yayi jaa kuka takeyi da dan karfi dan yau kam tayi niyya sede in mutuwa zatayi sede tayi amma bazata karacin naman kowa ba tun tana iya jurewa harta kasa , fanan tana zaune a main falo dan batason yawan hayaniya sosai tabar wajan zaman makokin ita daya a falo , tana nan tana tunanin yanda zata shawo kan lamarin zeenat kenan taganta ta diro daga can upstairs ta dira a gabanta kamar wata yar biri tashi fanan tayi tana ja da baya zeenat na binta harsuka kai dungun gini yanzu kam fanan tagama tabbatarwa kanta zeenat mayyace , kafa mata hakwara tayi awuya zata fara shan jininta yaseer ya cafketa ta baya gam yariketa yaki sakinta .
kokarin fin karfinshi takeyi dan girgizan da takeyi yawuce iya karfin zeenat da akasani , fashe musu da kuka zeenat tayi tana " wallahi mutuwa zanyi in bansha jini ba dan Allah ku taimakeni kubani in kuma ba haka ba zan iya mutu " hawayene yakebin fuskan fanan dan jitayi duniyar ta dena mata dadi tama kasa karasa wajan yaseer da yake kokuwa da zeenat, son da yake mata ne yasa lokaci daya tausayinta yayi tasiri aranshi hannunshi yamika mata aikuwa karaff ta damki hannun yaseer din tasa abaki ta fara tsotsan jinin shi cike da tausayi suke kallonta shigowar Mr azaad kenan yayi karo da mugun gani da wani irin speed ya isa inda suke ya fincike zeenat dake shan jinin yaseer da takeyi cikin daka tsawa yace musu " dama dukkan ku biyu baku da hankali bansani ba yaseer taya zaka bata hannunka tasha jininka " gam yarike wuyan zeenat yasa idonta cikin nashi aikuwa nan take ta sume bin Mr azaad sukeyi da kallon tuhuma meye abinda ya aikata yanzun nan meye dalilin dazesa daga kallon idonshi zeenat zata suma, bebi ta kansu ba yadauketa cakk yanufi part din ummi da ita yakwantar da ita afalo .
Su ukun duk suna zaune a falon ummin babu wanda yacema dan uwansa kala, fanan tana yiwa yaseer dressing din hannunshi da zeenat tasha jini, daga waya Mr azaad yayi ya kira layin ummi yace mata tazo ita da abba it's urgent, shigowa sukayi su biyar Abba,ummi, fawwaz,areef se anty amina ganin zeenat akwance bakinta da jini_jini Abba da ummi har suna hada baki wajan tambayar Mr azaad meya sameta , fada musu abinda ya gani yayi ,juyawa ummi tayi ta kalli fanan hawaye na fita a idonta jin halin da yarta ke ciki tace mata " my feena meya sameta " girgiza kai fanan tayi murya asanyaye tace " ummi tun dawuwarta jiya nace naji tana karnin jini seta min karya dawani abun daban amma dukda haka ban yarda da itaba seyau na kara tabbatarwa" dama suma tunda sukaga fanan tayi hakan sunsan da walakin goro a miya amma se basu wani bawa abin mahimmanci ba.
tashi fanan tayi taje ta durkusa agaban zeenat tasa hannunta akan goshinta sannan ta rufe ido nan take tafara ganin tun lokacin da vampires union suka fara shirin bawa daya daga cikin ahalin mainasara maita harzuwa time din da daya daga cikinsu yazama karamar yarinya me tallan guiva da siyan da zeenat tayi takoma maiya da cin naman da tayi da komai da komai seda fanan tagani kamar wacce ta kunna film tana kallo . dasauri ta bude idonta ta kalli yan falon da suma ita suke kallo musamman ma Mr azaad duk abinda tagani seda ta fada musu salati kawai sukeyi zufa na keto musu ta ko ta ina duk da sun rasa abinda yahada su da vampires union,
ana haka zeenat ta tashi daga suman da tayi sauka idonta yayi akan areef dake tsayi akusa da ita , hannu takai zata rarumeshi ta ciza yayi baya , damkar gashin kanta fanan tayi suna facing din juna kafin tasa mata hannunta abaki aikuwa nan da nan tafara shan jinin fanan dakatar da ita suke kokarinyi ta daga musu hannu haka sunaji suna gani zeenat tadinga zukan jinin fanan seda suka kai almost 30mint a haka kafin dukkansu biyu suka zube a sume.

Se mun hadu gobe inme duka yakaim.
Masu comment na gode Sosai Allah yamuku albarka.🥰🥰🥰

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Page 4️⃣8️⃣

Zeenat ce ta fara farfadowa tana wani irin amai me dauke da jini da nama_nama seda ta amayar daduk wani abinda ke cikinta tsaban yanda aman yaci karfinta seda kaff kuzarinta yakare riketa sosai anty amina tayi tana kiran abu tazo ta gyara wajan daki takai zeenat ta kwanta bacci , fanan na kwance akan kujera har time din bata farfado ba kusan an hour shuru , tun suna san ran tashin fanan nan kusa har tsoro yafara kamasu jinta shuru duk wani abinda zasuyi danta tashi sunyi amma fa shuru , da karfin gaske Mr azaad ke jijjigata duk da haka bata tashi ba lamarin yabasu tsoro seyanzu suka kara danasanin barin zeenat tasha mata jini gashi yanzu taki farfadowa daukanta Mr azaad yayi yakaita bedroom dinshi yakwantar da ita akan bed sannan yarufeta da blanket.zama yayi agefenta hannunsu rike dana juna . ba abinda yake matsar dashi daga gefenta fa ce sallah gudun karta farfado ba kowa akanta har dare fanan shuru ba labari, haka ya gyara musu kwanciya suka kwanta.

Asuba ta gari.
Chapter 17 · 0% Book details