← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 66

Sashe 40

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daki mama tashiga dan tabarsu suci abinci , , serving din Mr azaad tayi a plate hade da sa mishi ruwa a glass cup da drinks din ta jera mishi komai agabanshi sannan tasa musu nasu itada zeenat tamike takai musu dakinta da ruwa ta ce zeenat muje ciki , shiga dakin zeenat tayi fanan na kokarin tafiya Mr azaad yariko hannunta yajawota kan kujeran ya ce " inazakije kuma?" " zamuci abinci ne nida zeenat " cewar fanan, rike habarta yayi yana kallon cikin idonta ya ce " nikuma dawa zanci abinci in kika tafi " zaro ido waje tayi ta ce" ka lan mama tafito taganni ina cin abinci tare da kai ah ah gaskiya " bata fuska yayi" to shikenan tashi kije kici keda zeenat din nibazanci abincin ba hakan yamiki ina " ya karishe maganar yana kwantar da kanshi ajikin kujeran ya lumshe ido haka bayanda ta iya ganin ranshi yabaci dantace zasuci tare da zeenat yasa tadibo hadaddiyar jallof din dankalin takai mishi baki, bude ido yayi yasaukesu akanta bece mata komai taci gaba da bashi abinci se lumshe sexy eyes dinshi yakeyi tsabar yanda girkin ya mishi dadi , takawo mishi spoon dede bakinshi kenan yasa hannu yarike spoon din yakarba yakai mata baki , haka sukata feeding din juna har suka koshi sukasha ruwa da drinks.
abangaren zeenat kuma gajiya tayi da jiran fanan yasa tafito dan kiranta taga sunacin abinci ita da Mr azaad, komawa ciki tayi ta zauna tana "lallai matar nan shine zata sani jiranta tasan da mijinta zataci nima de Kwanan nan zanyi mijin yauwa " ita kadai take wayan nan magana tanacin abincin . Kwashe komai fanan tayi takai kitchen tadawo gun Mr azaad din bata dade dazama ba sega auta tashigo da gudu tayo wajan Mr azaad, ganin tanufo wajanshi yasa yabude mata hannu tarungumeshi tana " oyoyo Yaya balarabe, ai ina ganin car awaje nace it must be you ashe kaine " tafada tana haki dan dama gashi sun gaji ga gudun datayi ya ce " cutie Ina kikaje haka ?" ta ce " ya usman ne yakaimu yawo nida anty hairah kasan ina da ina mukaje ?" girgiza kai kawai yayi tacigaba " munje ice cream planet bayan mungama shan ice cream mukaje makay shawarma daga nan ya usman yakaimu shaf'an sekuma yakaimu G_connect nayi lilo " fanan kam bin auta kawai takeyi da ido ganin yanda intana magana bata tsayawa kamar suhaima ta ce" sannu fa auta tunda ba magana ko ganina ne bakiyi ba ?" " Laaah anty fanan kece nadauka ai Yaya balarabe ne kawai yazo " yanda take fitar da magana kamar wata uwar mata , shuru kawai fanan tamata . dariya Mr azaad yayi ya ce" ah gaskiya kunsha Lilo kam " yana rufe bakinshi ya usman suka shigo shida hairah tsugunawa hairah tayi ta gaishesu suka amsa fuska asake, musabaha ya usman da Mr azaad sukayi nanma fanan tafadawa ya usman anyi rasuwa, taaziya yayi musu . Seda sukayi sallar la'asar fanan da hairah suka dawo falo suka zauna tana tambayarta ya karatu , Zeenat dake daki fitowa tayi ta gaishe da ya usman da basu dade da shigowa ba daga masallaci shida Mr azaad. kallon fanan tayi ta ce" bari in shiga gidansu amira! hairah zoki rakani " tashi hairah ta ce " tom " dakin mama tashiga tafada mata zata raka zeenat gidansu amira mama tace sekun dawo fitowa tayi tasamu zeenat najiranta ta ce" anty zeenat muje " harsun kusa bakin kofa fanan ta ce" ku tsaya " sannan ta kalli Mr azaad murya kasa_kasa ta ce" habiby ayyah inje gidansu amira?" " Eh " yace aikuwa dasauri ta mike tayi gaba tabarsu abaya, dariya ya usman yayi ya ce " to sannu iyah ! sun jiraki shine ke kina zuwa kikayi gaba kika barsu " dariya kawai tayi batace komai ba , tafiya sukeyi suna har hira harsuka isa gidansu amiran afalo suka sameta tana waya da ya al ameen se zuba mishi shagwaba takeyi tana ganinsu ta taso tarungume fanan " oyoyo my bestie" " oyoyo bestyna kuma antyna " cewar fanan ya al ameen yanajinsu yayi dariya kawai yakashe wayar. dakin Amira suka shiga suka yada zangon hira hairah de jinsu kawai takeyi batace komai ba saboda duk sun girmeta babu yanda zatayi tasa musu baki a magana basu sa ko ta ba aciki , lura da hakan dasukayi ne yasa suke hiran harda ita , takuwa sake jiki dasu sunata hira drinks Amira takawo musu sukaci gaba da hira. Agidan sukayi sallar mangrib sannan suka fito suka shiga dakin hajiyarsu suka gaisheta da fara'a ta amsa musu fanan tafada mata anyi musu rasuwa hade da gobe zasuyi tafiya tazo musu sallama taaziya hajiya tayi musu da adduah Allah yakiyaye hanya , sannan suka wuce gida sunko dawo adede baba yadawo yana gida gaidashi sukayi yayi musu taaziya domin mama da ya usman sun sanar dashi kuma sun sanar mishi da gobe zasuyi tafiya hakan yasa yabukaci ganin su , su biyun adakinshi , shinfida sallaya fanan tayi akan carpet din suka zauna adakin baba , ganin yanzu sun dedeta kansu ne yayi wa baba dadi nasiha me ratsa zuciya da kashe jiki yamusu yahada da musu fada , daga karshe yamusu Allah yatsare hanya,suka fito akunne Mr azaad ya rada mata ku shirya kuzo mutafi saboda zamu tsaya agidan maman junior tace mai to tasanar da zeenat kintsawa sukayi . Suka fito zasu tafi mama ce tafito hannunta rike da fashion bags guda uku tabawa fanan daya tabawa zeenat daya sannan tabawa amira daya godiya suka mata takoma ciki duk suka rakasu har bakin mota suka tafi hade da kewarsu Amira ta wuce gidansu tana me musu seda safe .

Shiga gida ya usman, hairah da auta sukayi dakin baba ya usman yayi sallama izinin shigowa baba yabashi zama ya usman yayi akan sallayar yana sunnar dakai kasa, tunda yashigo baba ya lura dashi yasan akwai magana abakinshi ya ce " kazo kamin shuru kode babu abinda zaka fada ne usman?" Ya tambayeshi yana kallonshi sosa wuyanshi ya usman yayi ya ce " am dama baba maganar hairah ne" sekuma yayi shuru , murmushinsu irin na manya baba yayi domin kuwa ya ganoshi seya nuna kamar besan meyake nufi ba ya ce " tofa! meyasami ita hairah ?" yasake jefo mishi wata tambayar. Ya usman ganin baba yakasa gano inda ya dosa ne ya ce " dama inason a tambayamin aurenta ne " gyara zama baba yayi ya ce " to shikenan tunda naga kazo da wannar maganar nasan kun gama dedeta kanku kai da ita hairah in sha Allah zaa tambaya maka aurenta inyaso se a hada auren nakun dana sauran yan uwan naka ! se anjuma tashi ka tafi bacci zanyi " dariya ya usman yayi dan ya lura yau baba naji da barkwanci ya ce " nagode sosai baba Allah yakara girma " ya amsa da" ameen" sannan yafita da farin ciki aranshi kamar yazuba ruwa akasa yasha dan jindadi . Kiran Abba baba yayi yamishi taaziya.

Wasa takeyi da junior dake kan cinyarta se dariya yakeyi ga anty firdausi akusa da ita daddyn junior Kuma sunje sallah masallaci shida Mr azaad basu dawo ba.

Ina jiran comments dinku.

Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏 .
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
(* Yar lelen Jarumai*)

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

⚜️📚 J. W.A 📚 🖋️

Gargadi.....
Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin.

Page 5️⃣9️⃣
Chapter 40 · 0% Book details