← Book details Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 66

Sashe 38

Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ranar wata lahadi yakasance kwanar hafsat ne nadawo daga dubai sena sauka a part dinta, nashiga har bedroom dinta bansameta ba senayi tunanin ko tana toilet haka nazauna nayita jiranta shuru_shuru bata fito ba sena je jikin toilet din nayi knock naji ba alamar mutum yasa nabude naga wayam tunani nafara to ina ta shiga saukowa downstairs nayi naduba dakin mansoor nasameshi yana bacci , fitowa nayi har nazo zanfita naji kamar ana magana awani dakin saukan ba ki da hafsat ta hana kowa shiga acewarta intayi ba ki anan suke sauka kuma ni bana ganin kowa yana zuwa wajanta hatta danginta tamusu iyaka da gidan kuma bata zuwa se ta bushi iska , tsayawa nayi ajikin kofar na kasa kunne na dakyau wasu irin sambatu ne ke tashi wanda baze fadu ba kuma bana mutum daya ba . ahankali nabude kofar natsaya abakin kofar mummunar gani idona yayi da har yau inna kulle idona inaganin wannan bakar ranar , sauka idona yayi akan hafsat da wasu mutane kusan mutum uku da ita na hudu cikin wata suffa nadaban me ban tsoro jikinsu duk gashi babu kaya ajikinsu tsirara haihuwar uwarsu , sun sa namomin mutane agaba sunaci hade da shan jini hankalina yakai kololuwar tashi narasa meyakamata inyi in fitane ko in tsaya , yanda nake kallon su haka su ma suke kallona. bacewa sauran sukayi yarage daga ni se hafsat adakin nan take takoma ainihin suffar mutane, matsowa kusa dani tayi ta ce kai mijina ne kuma inasonka amma yanzu yazama dole in kasheka kokuma kahaukace amma kafin nan bari indan baka takaitaccen labarina tafada tana yar murmushi tafara magana , nakasance tun ina yar karama dani nake shaawar son cin naman mutane domin ko a labarai haka ake fada wai naman mutum yafi kowace nama gardi dakuma dadi hakan yasa nadauki son duniya na daurawa naman mutum, wata rana naje makaranta ina primary 5 naje toilet yin fitsari naga yarinya karama yar nursery 3 tafito daga toilet din tanata wasanta dubawa nayi naga babu kowa awajan ganin wannan babban damane agareni inna barshi subucemin zeyi yasa nakirata na mata wayo nakaita toilet din dukda banida wani isheshen karfi haka nayita kokarin murde mata wuya harnayi nasara na kasheta zama nayi dirshen akasan toilet din nasa hakori nafara fincikar namanta inaci senaji wani bankwarakwai saboda shine karo na nafarko amma hakan nadingaci seda nayi nisa acin naman sannan nafarajin dadi nakaimin har tsakiyar kaina haka nacinye yarinyar nan tas yayi saura kasusuwanta, tarkatasu nayi nazuba acikin dustbin nawanke toilet din yanda babu wanda zeyi zargin wani abu daga nan nakoma aji nadauki jakata nakoma gida kwanciya nayi cike da nishadi nafara bacci , abaccin ne naganni awani dokan daji me matukar girma sosai ga mutane sanye da bakaken kaya fuskokinsu arufe, sunatamin barka da zuwa cikinsu banji wani tsoro ba lokacin da suka sanar dani nazama daya daga cikin yan kungiya kuma zansamu duk abinda nakeso daga kudi duk wani abun duniya ga cin nama da shan jini sosai nayi farin ciki shisa duk wayanda sukace inkawo ayi sadaukarwa nake kaiwa , ganin mutane danakeyi ne yasa koda yaushe nake shiga cikin bukatuwa da cin nama idan kuma haka yaci gaba da faruwa to tabbas zaa ganoni shisa nake kebe kaina ni kadai bana shiga harkan kowa wanda kuwa yayi kuskuren takalata senaga bayanshi hankalina yake kwanciya , ana haka Allah yadoramin sanka kuma naji bazan iya cutar dakai ba harmukayi aure dalilin dayasa natsani shayida da zainab kuwa tunda nasamu cikinsu nabayar dasu ga kungiya akan insunzo duniya zaayi sadaukarwa dasu amma kwata_kwata hakan ya gagara akwai tsari ajikinsu domin me martaba yanason jikokinshi shisa tun ranar da sukazo duniya yake basu maganin tsari daga dukan sharrin mugaye acikin ruwan zam_zam , shisa na tsanesu tunda sungagara biyamin bukata , sekuma kadaukesu ka kaiwa matarka su wacce duk duniya babu wayanda natsana sama da ita da yayanta kuma nice nan ajalinsu sena kashesu musamman wannan dan nata azaad. haka tadinga fadamin asalin kalarta kwakwaran motsi nakasa ji nayi duk duniya babu wacce natsana sama da ita dakyar na iya bude bakina nace mata sena tona miki asiri kowa seyasan kedin wacece muguwa azzaluma macuciya kawai bari kiji na sakeki saki uku babu ni babu ke har abada , anan ne tayi kokarin kasheni da tsafi nadinga adduo'i bakina yaki shuru , hakan yasa tayi kokarin haukatani nan ma Allah bebasu saa akaina ba umarni shugabansu yabata kawai suka rubemin baki koda inasan infadawa mutane halin da ake ciki amma se inkasa , na matukar shiga damuwa seda nadanyi rashin lafiya aysha koda yaushe tanakan tambayata meyake damuna sede ince mata babu komai haka rayuwa taci gaba har lokacin da azaad yahadu da muguwar hatsari wanda ita da alh Ibrahim tijjani suka hada hannu dan kasheshi duk nasani amma ba halinyin magana , wato abinda yafaru jiya shine jiya harna fara bacci azaad yakirani yake shaidamin zekasheta kafin indawo inajin hakan nagano yasan komai hakan yamin dadi shisa nazo na warware muku komai " in banda koke_koke ba abinda ke tashi afalon musamman na anty shayida da anty zainab jin wacece uwarsu dakuma irin tsanar da ta musu sosai ummi take kuka lamarin ya girgiza duk wani wanda yake cikin falon domin mommy ta gurbata rayuwarta dakuma cutar da rayuka mara adadi wayanda hakkinsu kadai sun isheta saboda tazabi duniya tayi son kai da son zuciya , kifa kai fanan tayi ajikin Mr azaad tana kuka domin al amarin kamar a film , dukda kasancewar ita tun farkon haduwarta da mommy tasan akwai wani abu ashe macijiyar sari ka noke ce , haka zeenat ma tana rungume da ummi tana kuka , mazan kuwa idanunsu yayi ja jijiyoyin kansu yatashi jisukeyi kamar su kamo mommy su kasheta kowa yahuta musamman Mr azaad barinma inya tuna yanda ta tsani yan uwanshi da ita tahaifesu shuru kawai yayi dan inya bude baki zeyi magana yasan kawai kalmar kashe mommy ne kawai ze fito daga bakinshi, kuma muddin yatashi tom nan ma seya kasheta shisa kawai yayi shuru dan yaga shi yafi alkhari yana lallashin fanan dake kuka .

Abba ne yadaga waya yakira securities yace su kunce mommy sukawo ta , shigowa sukayi da ita duk tafita a hayyacinta domin igiyar da sarauniya ta daureta dasu kamar na dalma ne azaba kadai takeji ga shi duk wani karfin tsafinta yabar jikinta dungurata sukayi a tsakiyar falon ta fadi da kallo kawai suke binta anty shayida ce ta ce " mommy Meye zesa ? Mommy me muka Miki ? Meyasa kika jefa rayuwarki a irin mugun halin me kika nema kika rasa? Mommy bakya tuna haduwarki da Ubangijinki ? meye ribarki yanzu meyasa za ki mana haka bakya tunanin ya rayuwarmu zata kasance ?" muryanta dake fita dakyar ta ce " tsanar dana muku baze taba canzawa ba kuma yanda na kudurta aniyar ganin bayanku tofa sena aiwatar, tsabar tsanar dana miki shisa daga zaran kinsamu ciki nake cinyewa tunkafin kusan da hakan tunda ke kinfi karfin kungiya ai abinda ke cikin be fi karfi ba sau takwas kina samun ciki ina cinyewa haka kema zainab naso in miki se kuma banyi nasara ba kai kuma " tafada tana kallon abba" tunda na fuskanci ammi ta tsaneni yasa nakasheta domin yanda ta tsaneni nima haka na tsaneta, se kai azaad dan iskan yaro duk wata hanyar da zanbi wajan kasheka nabi amma hakan beyuba amma sena kasheka din " daura hannu akai anty shayida tayi tamike tana kuka tana maganganu kamar wata mahaukaciya Jin abinda uwar da ta haifeta tayi mata ashe ita ba juya bace, mahaifiyartace take cinye mata ciki ganin zata iya zaucewane yasa abba yarikota yarungumeta yana lallashinta yana jin ciwon abinda hafsat ta aikata mishi wato ita takashe ammi tabbas dole yadau mataki akan mommy domin ta cutar dasu da yawa , tsananin tashin hankali kam yau sunjishi ,yau itace bakar rana agaresu haka mommy tadinga confessing abubuwan datayi , tsuma kawai da rawa jikin Mr azaad yakeyi mikewa yayi da niyar damko mommy abba yamishi alama da ido komawa yayi yazauna barin falon areef da fawwaz sukayi dan insuna kallon mommy jisukeyi kamar su mata mummunar kisa hakan yasa suka wuce part dinsu zuciyarsu na tafasa.
Ana cikin wannan mugun yanayin mommy ta fashe da wata muguwar dariya tana sambatu da kuma fade_fade nan take tafara fincike gashin kanta tana zubarwa akasa lokaci daya ta haukace, hauka tuburan babu wanda ya kalli inda take domin itadin baabin atausayawa bace mikewa tayi da gudu tafita afalon baba me gadi na bandaki tabude yar karamar kofar gate din tayi waje bin bayanta securities din gidan sukayi , Ina tariga da ta musu nisa tahaukan titi wata katuwar tankan ruwa ne yabi takanta ya takata haka namanta yayi piecing akan titi harta kanta seda yatarwatse kwakwalwarwa awaje haka mommy tayi mutuwar wulakanci atozarce gaba daya jikin securities din yayi sanyi haka wasu daga cikinsu yashiga gida yasamesu afalon yasanar dasu abinda yafaru haka Abba,ummi, zeenat,anty zainab,anty amina dakuma anty shayida dake atare da abba tana kuka suka fita Mr azaad kuwa ko ajikinshi yadauki fanan suka haura part dinshi .
Chapter 38 · 0% Book details