Sashe 37
Nida Patient Dina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya ce " kamar yanda dukkanku kuka sani hafsat itace matata ta farko ! yar wazirin gombe ce tun kafin in kammala karatuna muka fara soyayya da hafsat , amma mahaifiyata wato marigayiya ammi , bata bada goyon baya ba saboda hafsat batada kunya bata son mutane kullum ako da yaushe adaki ake samun hafsat bata mu'amula da kowa seni sekuma yan gidansu ga ta da tsiwa ga shegen rashin kunya, amma dukda wannan dabi'ar nata take sona kuma nima inasanta, me martaba da waziri sunyi farin ciki sosai da kasantuwar wannan al amarin bayan na kammala karatu aka mana aure , me martaba yace tunda yanzu na kammala karatuna kuma nayi aure ni zan karbi sarautar gombe , hankalina yatashi domin ni bantaba kaunar zama sarki ba hasalima abubuwan sarauta baya burgeni ni babban burina shine inzama business man, shisa na ki kuma fulani ta goyamin baya , haka me martaba yakyaleni nayi abinda nakeso .
dede da rana daya ammi bata ta ba son hafsat ba in an tambayeta dalili setace jikinta nabata akwai wani mugun abu atare da hafsat tana ganinta amafarkinta. babu wanda yataba daukan maganar ammi serious kowa gani yakeyi kawai dan ta tsaneta ne yasa take fadar haka. bayan aurenmu da wata daya ammi ta rasu sanadiyar bugawar zuciya haka akayi zaman makoki aka watse tundaga nan ne hafsat ta fara nunamin mugayen dabi'un ta, bata sallah , ba karatun addini ko adduah bantabaji tayi ba,bata kaunar kowa ya rabeni , sannan kullum tana daki yanda na fita nabarta haka zandawo in sameta bata, bantaba sanin ya kalar test din girkin hafsat ba har yau danake muku wannan maganar sede masu aiki suyi mana abinci. bata rayuwarta da kowa tun ina mata fada harna hakura nazuba mata ido domin daga zaran nafarayi mata fada itama zata hayayyakomin kamar zata dakeni nikuma bazan iya sa'in sa da mace ba yasa se inbar mata part din se dare in dawo haka har tasamu cikin zainab ta haifeta, tunda nake arayuwata bantaba ganin macen da ta tsani abinda tahaifa ba se akan hafsat ta tsani zainab har kamata natabayi tashaqe ta tana kokarin kasheta dakyar nakarbi zainab ahannunta jaririya dabatasan komai ba se zabga kuka takeyi . daukan zainab nayi nakaiwa fulani nafada mata abinda yake faruwa hannu biyu ta karbeta renon zainab yakoma gun fulani. mukaci gaba da zaman doya da manja nida hafsat yau lafiya gobe kuma fada da tashin hankali ahaka harta fara fita araina dan nagaji da mugayen dabi'un ta. zainab nada shekara uku hafsat tasake samun wani cikin bata nuna bataso ba wannan karon har ina murna gata iya gata na nuna mata amma tana haihuwar shayida komai yasake dagulewa tsantsan tsana shayida tagani kamar ba ita tasha wahala tahaifeta ba harta abinci bata ba ta haka zata wuni da yunwa se na dawo gida tunku mukecin abinci abin nata da ya isheni ne yasa nafada mata muddin taci gaba da gallazawa shayida to nikuma zan saketa hakan ne yasa tayi sanyi domin tanasona sosai , akan abinda takewa shayida tarage kashi 20 acikin 100 gashi Zainab bata isa tazo part dinta ba seta mata mugun duka , lamarin ya isheni yasa nasaketa saki daya ta tafi gida nikuma nadauki shayida itama namikata gun fulani.
zuwana dubai gabatar da wani meeting da babban Company na A.A AZAAD, bayan mungama meeting kanin sarki azaad me suna arash ya gayyaceni gidansu cin abincin dare dukda inada wani uzuri haka na amsa gayyatarshi naje babban gidan sarautar dubai sunada matukar mutunci da karrama bako yanda suke haba_haba dani hakan yamin dukda nima dan sarki ne . muna zaune munacin abinci sarki azaad ya gabatar min da ahalinshi da matar kannenshi , matar arash dakuma matar asaad, sekuma matarshi wato mahaifiyar umminku aysha kenan se yaransu dasuka kasance dukkansu maza rai 9 jinjina kai nayi nace " Masha Allah,Allah ya azurtaku da yara maza Allah yarayasu" suka amsa da ameen sarki azaad ya ce" ai sunada kanwa guda daya rak ita kadaice mace agidan nan " murmushi kawai nayi bance komai ba , kiran sunanta sarki azaad yayi " Aysha" fitowa tayi tana tafiya cikin nutsuwa yarinyace dabazata wuce shekara 15 ba aduniya kyakyawar balarabiya sanye da doguwar riga baka kanta rufe da mayafi tunda tafito idona akanta yake lokaci daya naji nakamu da santa, gabatar min da ita sarki azaad yayi, fuskanta dauke da murmushi tagaisheni amsawa nayi iname yaba hankalinta komawa ciki tayi duk matan wajan suka bamu waje , harga Allah tunda naga aysha naji inasonta kuma so na aure bazan iya barin dubai batare danayiwa iyayenta magana ba , ban boye musu komai ba na fayyace musu abinda ke raina nahada da fada musu inada mata da yaya biyu. banyi tsammanin zasu amincemin ba cikin ruwan sanyi ba kawai naga sun amince domin ba kowani balarabe ko farin fata bane yakeson hada jini da bakar fata ba sukace in turo iyayena da full confidence dina nabar masarautar zuwa masaukina dukda sunyi sunyi inzauna na ki. haka nadawo nigeria da farin ciki naje nasamu me martaba nasanar mishi shima ya amince da lamarin saboda suna shiri sosai da sarki azaad haka suka nemamin auren aysha, tunda hafsat taji labarin zan kara aure ta dami waziri da sede yanemeni zata koma gidanta haka waziri yanemeni yarokeni da inmaida auren haka kuwa akayi namayar da auren . hafsat takoma gidanta mukaci gaba da rayuwa balaifi dukda bakamar da ba , har a wannan lokacin bansake haduwa da aysha ba saboda a al adarsu inde yarinya zatayi aure bazata sake ganin mijin ba ko jin muryanshi ba se randa aka daura musu aure. Bayan nagama gina wannan gidan ne aka daura aurena da aysha saboda nafison zama awajen masarauta, hafsat itace uwar gidana yasa nabata zabi tazabi part din da takeso haka tazaba , aka kawomin aysha gidana yan uwanta mutane hudu ne suka rakota bayan anyi shagalin biki anwatse , natarasu a part dina dan musu nasiha dukda aysha batajin hausa daga larabci se turanci haka namusu fada sannan naraba musu kwana , hafsat bata nunamin komai ba ta tashi ta tafi abunta , haka rayuwa taci gaba da tafiya nan ne nafara samun kwanciyar hankali. takuramin aysha tayi akan lallai sede indawo da shayida da zainab wajanta haka nakarbosu daga wajan fulani na damka mata su aikuwa suna ganin gata sosai kamar ita ta haifesu ana haka aysha tasamu ciki tayi laulayi sosai fulani na yawan zuwa dubata kuma kullum ita take mata abinda takeso ta bada akawo mata. bayan wata tara tahaifi ya mace akasamata suna amina wato sunan kakarku ammi kenan ,haka tahada yaran dukkansu uku taci gaba da kula dasu tunda aysha ta haihu har akayi suna tayi arba'in ko kafa hafsat bata taka a part dinta ba nayi maganar harna gaji , amina nada shekara hudu aysha tasake haihuwa ta haifi da namiji yaci sunan kakanshi wato azaad sosai yaro yaga gata nan ne kadai hafsat tazo suna daga nan batakara zuwa ba amma aysha tana zuwa mata ta gaisheta lokaci zuwa lokaci , daga nan ne hafsat ta tayar da bori sede abata yayanta gudun masifarta yasa na kwashi yaran nakai matasu duk tunanina tacanza halayenta ashe bahaka bane ta karbesu ne dan ta kashesu , bazan taba mantawa wata rana inazaune a office meyi mata aiki takirani aboye tana sanar dani hafsat ta bawa shayida da zainab guba ba shiri nadawo gida tare da motar ambulance aka kwashesu akayi asibiti dasu dakyar aka ceto rayuwarsu saboda guban bedau lokaci ajikinsu ba , haushi kamar ya kashe hafsat raina abace nadawo idona yarufe bansan lokacin da na dinga zabga mata maruka ba tsabar taurin rai irin na hafsat ta kalli idona tacemin inde yaran nan ne seta kashesu domin bazata taba sonsu ba har duniya ta nade, banyi mamaki ba dan yanzu nasan hafsat bata sansu haka naje wajan aysha dabatasan abinda yake faruwa ba nace ta shirya muje asibiti duba su zainab hankalinta yatashi jin abinda hafsat ta aikata musu anan ne tasan bata sansu tayi kuka sosai dakyar na iya lallashinta, tadauki azaad da ake goyo muka tafi asibitin satin su biyu aka sallamesu ko da wasa banyi gigin kaisu part dinta ba nabarsu awajan aysha tacigaba da kula dasu . Haka shekaru sukata ja sosai aysha tasake haihuwa ta haifi fawwaz dakuma areef a time din duk suna makaranta duk sun girma , hafsat bata sake haihuwa ba. su shayida da sungama karatu har akayi auren zainab daga baya akayi na shayida , Allah yabawa zainab haihuwa ta haifi dan ta namiji akamin takwara Muhammad wanda yanzu yake Russian yana karatu, nan ne hafsat tasake samun ciki zuba ido nayi inason inga wannan karon ma zata tsani abinda zata haifane da iKon Allah tahaifi namiji aka samishi Mansoor soyayya, gata, kulawa babu wanda mansoor be gani ba tasoshi sosai kamar ranta , Mansoor nada shekara daya Aysha tahaifi zeenat kusan atare suka taso Wanda nasan kunsan hakan yanzu bari infada muku ainihin dalilin dayasa nataraku anan.