Sashe 7
Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wuraren 10 su Baba suka shigo gidan, direct dakin yara yawuce, shikuma Baffa yana kulle gate, ahankali yatura kofansu yashiga wayan hannunshi ya kunna saida ya dudduba su ganin duk sunyi nisa abacci sannan yasake Tofa musu addu’a yafito tareda maida kofan nasu ya kulle sannan yama Baffa sallama duk kowa yashige dakinshi maida kofan dakinsu yayi yarufe sannan yawuce uwardaka, jallabiyan shi yashiga cirewa yana kallon Ammi dako sallaman shi bata amsaba kuma yasan ba bacci take ba, bayi yashiga bakinshi ya wanko tareda dauro alwala wanda wannan haka yake kullum sannan yafito ya kashe wuta taredayin bismillah yahau gadon, ahankali ya matsa kusada Ammi yakai hannunshi yana kokarin juyoda ita cikin wata kalan murya yace “juyo kimin Allah sanya alheri dan ke kadai ce kika rage baki samini albarka ba” kabarda hannunshi tayi cikin fushi da rashin son yin magana dashi tace “stop touching me” dan shiru yayi saikuma chan yace “kiyakuri to” kaman jira take wani kalan juyowa tayi saikuma ta tashi zaune cikeda masifa amman bamai karfi sosai ba gudun kar ajinsu tace “nagaji da hakurin dakeke bani kullum saikagama cimini mutunci agaban uban kowa sabida yara saika biyoni da daddare kana cemin nayakuri yau bazanyi ba kaji Ibrahim bazan yi ba” shiru Baba yayi jin takira sunanshi yau kai tsaye yasan ranta yabaci, cikin wani yanayi na nuna kunci tace “Ibrahim ka manta cewa nine mahaifiyar yaran nan, nine nadaukesu wata tara acikina, nine nai laulayinsu, haka kuma nine nan nikadai nashiga labour room nasha nakudan yaran nan nahaifosu maisa kake treating dina kaman banson yarana kaine kadai ke sonsu why? Inda ba nine na haifesu ba sai ace eh dama banice mahaifiyar su ba but this girls are mine, nine mahaifiyar su, mesa kakemin abinda kakemin akansu eh Baban Nanah”? Shiru Baba yayi baice komiba baki Ammi tabude zatai magana sai kawai kuka ya kufce mata kawai tafashe da kuka sosai dan abinda yake mata na kona matarai ainun, wani kalan sanyi jikin Baba yayi ahankali yajawota zuwa jikinshi batai musu ba tashige bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi yace “kiyakuri bazan karaba, I know you love our girls beside yaranmu ne nidake muka haifesu sometimes ina miki fadane sabida sakaci, Maryam yara mata muka haifa guda uku, hakki ne su akanmu nida ke we have to protect them, support them, musa idanu akan lamarin su, mu tarbiyantan dasu da kyau kinsan idan ka tarbiyantan da yara mata da kyau ka aurar dasu Allah zai bamu aljanna ranan gobe kiyama? Hadisai daban daban daga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi inda yake nuna falalan da iyaye suke samu ranan gobe kiyama dasuka tarbiyantan da yara mata da kyau, Please understand me kidaina fushi dani, inaso kiyi tsayin daka kaman ni akansu that’s all stop crying matata, I am simply doing the right thing” yay maganan yana bubbuga bayanta, da kyar tai shiru ta dago daga jikinshi sannan takalleshi dudda cikin duhu ne tace “I understand abinda kake kokarin yi kan yaran nan perfectly well but is too much! You are overreacting, Yara mata garemu kana tareda yaran nan 247, kana yawo dasu kana rike musu hannu a anguwa, anguwan nan kap babu wanda baisan how protective you are towards this kids ba, wazai taba zuwa ya aure su kowa tsoron tinkaranka yake, Yasmeen dinmu is 20yrs kasan mates nata guda nawa sukai aure yanzu alayin nan kadai? Ita ko saurayi batadashi sabida kai, kowa yasan babanta dan sanda ne kuma bai bari akula yarshi” Haderai Baba yayi dasauri kaman bashi ba yace “nina gayamiki aurar da ita zanyi yanzu?” Dasauri itama Ammi dan yau kome zai faru yafaru daidai take dashi tace “to karatu kakeson tayi da kana gani dai she is not going anywhere akaratun”? Shiru Baba yayi yajuya kawai zai kwanta dasauri Ammi tarikemai hannun tace “Ibrahim listen to me ba lallai saikabi abinda nake fadi ba amman inaso kai nazari kan maganata, nagaji damaka shiru ne so I have to tell you abinda ke raina yau, Baban Nanah” Ammi tai maganan asanyaye tace “Yasmeeen tun tana yarinya bansan ko dan ita yar fari bace amman dai me and you munsan tun tana yarinya batada kokari, adaddafe a repeating da chanje chanjen makarantu daban daban sabida kai kanka kagaji da repeating da ake mata aka samu tagama sakandare at the age of 18, tai waec na farko duka f9, waec din daka biyamata tana 19yrs Allah ya taimaka taci shima Allah kadai yasan tayaya tai passing dan am sure kai karan kanka har yau u are still in shock ya yanda tai passing exam din, har yau har gobe bakomi Yasmeen ke iya gani takaranta tsaf ba wani zubin Farida nan kanwarta that is just 15yrs SS3 student ke taimakonta dasu Sa’a, dudda babu kalan lesson teachers da lessons dabaka sata ba, Yasmeen is just like that haka Allah yayo brain nata, I am sorry to say this banson nakira yarda na haifa dakikiya amman me and you munsan cewa kusan hakanne, ka kaita school of nursing tafara anayin weeding exam nasu aka koreta batai passing ba shima F tasamu, dudda lokaci yakuri ni nasan dayaya dayaya kasamu da kyar kasamo mata admission na FCE part term shima yanzu tafara an bata Islamic studies amman she’s not going anywhere with it, infact ni aganina ma FCE yafi bata wahala kan school of nursing, subject daya kusan malamai ashirin akai Baban Nanah kuma kowa da nashi abubuwan karatun ina kakeson yarinyar nan tasa kanta?” Ammi tai shiru tana kallon Baba ganin yaki magana yasa ahankali tace “nasan ka hadata dawata lecturer daka biya tana zuwa office nata ana kara maimaita mata komi sannan da kanka kadauketa ka kaita school na Maman Intee nakoyan su abinci, drinks da cakes which shine abu na farko danaga Yasmeen tasoma iyawa sharp sharp tunda na haifo yarinyan nan” Ammi tai shiru sai alokacin Baba yajuyo yakalleta yace “all lissafe lissafen nan what are you trying to say? Nagayamiki nagaji da kashe kudina akanta ne? Koko kintabaji nai korafi kan rashin gane karatun ta dawuri ne? Ai ni ke biya bakeba ko to ki barni da maganan nan please bansonji” girgiza kai Ammi tayi trying to make him understand her tace “Baban Nanah, abinda nake kokarin cewa shine you might thing abinda kakema Yasmeen shine the best thing any father zaima diyarshi but you are wrong yarinyar nan is going through a lot nine mahaifiyarta kwayan idanunta kadai nake gani nasani, karatun nan yamata yawa, sannan yanda ka tsaya tsayin dakan nan akan yaran nan baka basu breathing space karage, let this children be ko masamu wani yayi approaching Yasmeen da maganan aure, Yasmeeen tayi girma, she’s a very fine beautiful girl, give her space wannan kaita FCE dakake duk Saturday da sunday sannan ka koma ka daukota kabari, let her go on her own and mingle da dalibai irinta, allow Yasmeen kullum tadinga zuwa shagon Maman Intee da kanta, stop holding hannun Yasmeen a anguwa kowa nagani yes ansai kai babanta ne but stop treating this children kaman zaka maidasu cikinka u are being over protective and yaran da maza suka gani daddy’s girls ne tsoron approaching nasu ake barinma kai da u happen to be a police man uniform mutum, kar halin nan naka da tsayayyen uba yasa yarana su rasa mijin aure” wani kalan dogon tsaki Baba yaja yace “maganan banza maganan wofi” kawai ya kwanta tareda juyamata baya Ammi tadade tana kallonshi dama deep down tasan za’ai haka shifa indai kan yaranshi ne bayaji bayagani, abinda yayi shine always best akan yaranshi, tadade ahaka sannan takoma ahankali kawai ta kwanta itama tajuyamai baya kowa da abinda yake tunani, almost 20min suna ahaka sai kawai Baba yajuyo dudda yaso yabarta yahakura kasawa yayi cikeda masifa yace “bani hakki na, kuma wannan abun dana barki kikaje aka makala miki a hannu gobe karna dawo aiki naji shi a hannunki, nafasa dagamiki kafan haihuwa nakeso yara uku sunmin kadan” dukfa fitinanta mijinta yafita tanaji tana gani haka yashiga yin yanda yaga dama da ita kaman ma punishment yake bata, duk yanda takai ga jin haushin shi saida tashiga bashi hakuri sannan yasata ajikinshi Ya matse sosai yace “dagayau kada ki kara fadamin wata magana akan yarana, ni mahaifin su ne bazan taba cutar dasu ba, nafiki sanin abinda yadace akan yarana, inason yarana sama da rayuwata, inason yarana sama da zuciyata, my children are my entire life and reason for my existence, inhar kinason mu zauna lafiya ki koyi sonsu kaman yanda nake sonsu dan indai wannan abin dakike fadamin nayi aganinki shine so to kinyi kuskure ba so bane, idan abinda nake musu shine zaisa kada su sami miji to kada su samu din bangaji dasu ba ban gaji da ganinsu ba bazan taba gajiya da yaran da Allah yabani ba, sai maganata ta karshe kada ki kuskura ki kara kiramin yarinya da dakikiya Yasmeen ba dakikiya bace, my daughter is smart, ranan dana fara kaita makaranta aduniya ko A bata iyaba amman yau anwayi gari ta iya A har Z, ta iya 1234, tasan abubuwa da dama, kisan banbancin tsakanin wanda baya iya gane abu dawuri kokuma karanta abu da wuri da dakikiya, kada ki kara kwantata mini yarinya da mummunan kalman nan kinajina” gyadamai kai Ammi tayi dan sosai taga ranshi yabaci sakinta yayi yajuya mata baya yay bacci abinshi yabarta tana matsan hawayen tsantsan bakin ciki..EPISODE 4️⃣