Sashe 56
Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace "nasallameki ne"? ahankali tace "a'a" dan shiru yayi kusan 1min baice komiba ahankali vace "have u had ur dinner?" Ahankali tace "eh" "mekikaci"?Kwanciya tayi ahankali daidai zata bada amsan taji muryan Baba yana magana da Baffa zai shigo dakin atsorace tace "Baba yazo bye" tura wayan karkashin pillow tayi ta runtse idanunta tai lamo daidai Baba yay sallama yashigo Farida tace "Baba sannu da zuwa" karasawa gaban Farida yayi yace "yauwa Farida ya akayi bakiyi note a school ba" adan tsorace gain yanda ya kafeta da ido tace "Baba kaine na ciwo ne lokacin a class" dan sassauta mura yayi yace "dakika dawo kin fadama Mamanki kanki na ciwo kinsha magani"? Gyadamai kai tayi ahankali tace "nasha" hannunshi yakai yataba goshinta kafin yakai wuyanta jin ba zafi yace "idan yasake damunki gobe lemme know zan kaiku hospital kiga Dr" anatse tace "to Baba" tashi yayi yakalli Yasmeen datai lamo itama Farida faduwa gabanta yake dan kada yakamata karasawa gaban gadon yayi yakalleta ganin kaman tai nisa abacci yasa yajuyo yakalli Farida yace "Ina Sa'adatu"? "Tana wajen Yaya" Gyadamata kai Baba yay cikeda gamsuwa Yasmeen yakara kallo yabi dakin da kallo kaman nai neman wani abu sannan yajuya yafita yace "saida safe kiyi addu'a kafin ki kwanta" "to Baba" Farida Farida tafadi ahankali tareda sauke jjiyan zuciya ganin yafita takalli Yasmeen tace "Allah yasoki bai kamaki kina waya ba hope dai kin katse wayan"? Dasauri Yasmeen tasa hannu taciro wayan daga kasan pillow ga mamakinta Maheer nakan layin dasauri takai wayan kan kunnenta tace "daman ban kasheba kai mesa baka kasheba" ahankali yace "ban sallameki ba" "to me kakeso?" Yasmeen tai maganan tana kallon kofan su jin antaba gain Sa'a ne tashigo yasa tasauke ijiyan zuciya, jin shiru baice komiba yasa ta turo baki cikin kunkunai tace "ni zanyi bacci" almost 10secs baice komiba kafin chan yace "bakida kunya ko" dan dariya kadan tayi mara sauti tace "toka barni na kwanta baccin" yanda taja baccin saida yaji aranshi, anatse yasauke ijiyan zuciya cikin tattausan murya yace "good night Fateema" kasa magana tayi tai shiru tama rasa takamaimen metakeji danji tayi inama baice good night ba, anatse yace "zanzo ranan Sunday by 3, 4 zan tafi" cikeda tsiwa tace "karka sake kazo gidan mu ni, kuma bara'a aureka ba din, bye" dip ta katse wayan. [8/1, 5:44 AM] AMINA KABIR CAPS: Ta tura wayan karkashin pillow dasauri tareda lumshe idanu wh batasan mesa ba bala'in dadin wayan dasukeyi takeji har aranta itadai tabani meke damunta ne haka, fuskanshi tafara gani ahaka daga baya bacci yay awon gaba da ita. Yau tunda ta tashi gabanta faduwa yake ita tunda take bata taba shiga irin wannan vanayin arayuwanta ba, wani bangare na zucianta na toron mutumin nan da shakkan shi sabida tasan criminal ne, koba komai ya gwada mata kadan daga halinshi, wani bangare na zucianta najin wani iri game dashi tun ranan Friday dasukai waya basu kara ba sotake yasake kiranta suyi magana taji muryanshi, tabude message nashi takaranta yafi sai dari na Sweet dreams din nan, tabude number shi takalla harta haddace akanta tsabagen yanda take tunaninshi she's just dying to hear from him, kewanashi infact babu abinda bamataji game dashi, wani bangaren na zucianta bayaso yazo gidansu yau amman har kasan ranta wh wl takosa taganshi, tarasa mezatai tunani to idan yazo su Farida suka ganeshi fa suka fadi koda yake Farida tace ita bata iya ta kalli fuskanshi ba Nana wannan daman kuka take batasan shi ba harsuka dawo daga hadda wuraren 1 tarasa meke mata dadi mix feeling takeji sosai daman gashi sunyi test bata iya tayi komiba. Wuraren 1 aka bude labulen kofanta dasauri ta dago kanta Baba tagani yana sanye da manyan kaya dasauri ta tashi ta zauna tana jawo dankwalinta dan rufe kanta, Baba dake kallonta ganin tamai wani iri yace "kinyi salla"? Gyadamai kai tayi ahankali, Baba dake kallonta ganin duktai wani iri yace "baki da lafiva ne?" Baki tabude zatai magana saiga hawaye sharrr sun zubo dasauri Baba yasaki labulen yawuce yashiga dakin, abakin gadon su yazauna yana kallonta baice komiba itama kallonshi tayi kaman tafadamai abun da ya tsayamata awuya amman bazata ivaba batason tazama sanadin dazaisa akashe mata iyaye hannayenta kawai tadaura kan fuskanta tafashe da kuka sosai, Baba yakai cikakken 1min yana kallonta bai hanata kuka ba chan yace "Yasmeen" cikin kuka tace "naam Baba" hannunshi yakai saman fuskanta yazare hannayen taredakai bayan hannunshi yashare fuskanta tsaf yace "meke damunki"? Dan yasan kukan damuwa takeyi bana ciwo ba, vanda Baba ya tsareta da ido yasa ahankali cikin murya Mai balain rauni tace "muni test a hadda ko daya ban iyaba Baba, zasu karamin repeating ko halama nan gaba Nana tazo tafini aji, Baba maisa banda ilimi maisa har yanzu bana iya rubuta kowani kalan baki, nasan amsan tambayan but ban iya narubuta ba banda kokar...." " kuka vakaracin kartinta dasauri Baba yasata ajikinshi kankameshi tavi bayanta ya bubbuga yace "shiti kada ki kara cewa bakida kokari, kinada kokari kini bari akwai wata Malama da akamin maganan ta zan daukota tadinga zuwa gida tana miki all abubuwan kinji now stop crying" kara sosuwa zuciyanta yayi all Baba ever did was to support her daidai da sau daya Baba baitaba complaining cewa batada kokari ba dudda kowa na gidan nan yayi, baya gajiya da nema mata ilimi, baya gajiya da sata a makaranta daban daban, tayaya itama yanzu lokaci yayi bazatama mahaifinta hallaci ba, ta ceceshi koda mutuwa zatayi ta hanyar haka daya taba iyayenta gwara ta aureshin kome zaiyi yayi da ita idanma kasheni zaiyi yayi amman ya kale Baba yasa adaina binshi ya kyale yan uwanta. Sallama Ammi tayi tashigo ganin Baba dakin saida abin yabata mamaki baki tasaki tana kallon Yasmeen dataga idanunta sunyi ja dasauri itama tazo wajen tace "Yasmeen meya sameki"? Takai hannunta tana cirota daga jikin Baba, ahankali tace "muni test ban rubuta komi ba Ammi" Ammi jitayi zuciyanta ya sos dasauri ta rungumeta tana kallon fuskan Baba dake kallonta tace "stop crying a karatu the most important thing shine kanka yarike and Alhamdulillah kanki yarike was dan haka ki barma Allah komi watarana sai labari kinji saisa gara kiyi aurenki kihuta da wannan bakar wahalan dakike a makarantu" wani mugun harara Baba yama Ammi itama ta maida mishi hararan back, tashi yay yakalli Ammi yace "nafita idan yaron yazo kada yawuce awa daya agidana dan haka ku kiyaye" yay maganan da kakkausan murya yawuce yafice Ammi tabishi da kallo baki sake kafin tasauke jiyan zuciya tace "kaji dashi" tadago Yasmeen tace "ke dalla chan yau saurayinki zaizo duk kinbi kin kuka jibi idanunki, tashi kije kiyi wanka kizo dakina ina jiranki" makema Ammi wuya tayi cikin muryanta dakeda gobe na kuka tace "ni bazanyi wanka ba" haba Ammi takama tace "au yau shagwaban yatashi ne ahhh lallai Aiko mangareki zanyi anan niba Babanki bane dazai tsaya lallashinki ba, tashi muje ma abayin nawa zaki wanka" badan taso ba Ammi ta tasata agaba suka tafi dakinta wanka tasata tayi sannan tafito mata dawata sabuwar atampa superwax gal wanda na salla Baba ya dinka musu dan dazaran yasami kudi yake abubuwa da wuri duk a ijiye, kayan Ammi tanuna mata tace "imaza saka kizo kigani" Ammi tasauke wani babban akwatinta tunna aure taciro wani gyale chantily milk sabo a leda tace "kinga tsaraban gyalen da makociyar mu Hajiya Mariya tabani yau ga amfaninshi" Yasmeen dake jan zip na skirt din datasaka takalli Ammi cikeda rigima tace "waye zai da gyale Ammi"? Hararanta Ammi tayi tace "wale tunda kaina nake cirowa gyalen" kaman Yasmeen zatai kuka tace "Ammi ni hiabi zan saka" akwatin Ammi tadauka tamaida sama tace "uku saura kwata fa kike shirmen nan wh Yasmeen nadade banga fitinanniyan yarinya irinki ba bari kiga naje nakira miki Sa'adatu da Farida" juyawa Ammi tayi tafita dakin Yaya tawuce Sa'adatu na zaune da Farida afalon da Yaya da Hajjo suna hira shigowa Ammi tayi ciki tace "Yaya yarinyar chan na sani ciwon kai wh, Sa'a keda Farida kuje ku mata kwalliya naciro mata gyale dan gidansu shi zata saka" tashi sukayi suka fita da sauri Yaya tace "ai Yasmeen ni bantaba gani yarinya baiwar Allah irinta ba, Allah dai ya tabbatar da Alhairi" atare duk sukace Ameen. Yasmeen duk yanda take rigima bataso bataso saida Sa'a tamata kwalliya 53| lafiyayye mai kyau tasamata jan baki tamata dauri daya fito da jelan gashinta ta daurin yay wani kyau Sa'a ta yafamata gyalen awuya daidai nan aka sallama cewa yazo Yayacw ta leko tace "ace yashigo" tunda Yasmeen taji haka gabanta ke faduwa sosai da Sa'a da Farida suka kwashe da dariya Sa'a tace "wlh yanda kikeyi kaman wata amarya Yasmeen that means randa zaa kaiki gidan miji ba karamin kuka zakiyi ba" daidai nan Maheer yashigo cikin gidan, yana sanye dawata milk yadi anmai dinkin jumper dayamai kyau ga hula akanshi Ya Allah! Zaka dauka wani kalan angon e tundaga gate kamshin shi yacika ko'ina Farida ne tafito daga dakinsu takalleshi yana tsaye wajen gate aranta tace wow wanna kyakkyawan ne mutumin Innalillahi karasawa tayi har inda yake akunyace tace "ina yini Yayan mu" Maheer yadade yana kallon Faridan, she's just like Yasmeen amman Yasmeen tafita kyau nesa ba kusa ba, murmushi yasakin mata mai sanyaya zuciya yace "Anty Faridan mu" wani kalan kashe Farida yayi da dadi tace "zo muje na Kaika daki ance kashigo" anatse yace "ok" tana tafiya yana biveda ita abayin gidan tsaf tsaf dudda ba gidan masu kudi ba amman ko datti daya bai gani ba, dakin Ammi tashiga tajuyo takalleshi tace "bismillah" cikin dakin ya kalla kafin anatse yace "Assalamu Alaykum" yashiga ciki Farida ta amsa kuiera tanunamai tace "kazauna wata one sitter yazauna akai sannan tashiga ciki cikin whispering tace "Innalillahi Ya Sa'a kinga yanda saurayin Anty Yasmeen keda kyau kuwa kuje ku gaishe shi bari naje dakin Yaya na kwasomai ruwa" fitowa falon tayi akunyace yawuce tafita Sa'a takalli Yasmeen dava zauna tai kuri kaman jira take ace kule tafashe da kuka tace "tashi muje" makemata kafada tayi hakan yasa Sa'a tace "wh zanje nagayama Ammi" dasauri ta mike tsaye hannayenta narawa har saida Sa'a ta lura hakan yasa yakama hannunta tajawota suka fito, tunda suka fito Maheer yadaura idanunshi kan Yasmeen