← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 145

Sashe 18

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wike dake cikin wata black van dawani yaronshi ke tukawa ne sunabin Keken da Yasmeen keciki wayanshi tahau ruri dasauri yace “it must be Oga” ciro wayan yayi daga wandonshi yakalli screen din ganin number dayay saving da Dan yasa ya amsa da sauri yakai kunne yace “Dan” anatse Dan yace “Oga yace execute operation” cikin murna Wike yace “angama” katse wayan yayi yashiga dialing number yaranshi dake school nasu Farida yace “CP idanma bakasan Pablo Escobar ba, yau zaka sanshi zamuga wazaici wannan yakin and wazai lose” daidai yaron shi yadauka, anatse yace “execute the plan Usman” dasauri yace “daman nagama shiryawa tsaf Oga bari naje” katse wayan yayi, sauka yayi daga motar yabar wani saurayi shima sanye da kayan police station aciki, sannan yawuce cikin school din yana sanye da kayan police harda nametag da aka rubuta Aliyu SS ajiki, private school ne normal one ba irin masu tsadan nan ba, direct office na principal yawuce yana shiga matar tace “welcome” murmushi yamata yana kallon agogon hannunshi yace “barka da safiya Hajiya, Ogana ya aikoni Commissioner of police Ibrahim Ibrahim na dauko yaranshi za’amusu interview ne a office nashi kinsan jiya aka maidashi commissioner” cikeda farin ciki matan tace “ai nakalla a AIT wlh, bari nasa akirasu, Farida da Nanah ko” tashi tayi ta leka waje tasa wata Malama taje ta kirasu sannan tadawo tazauna tace “ai daya kirani da kaina da ko direbanane sainasa yakaisu” murmushi Usman yayi yace “yana meeting ne wlh” daidai nan Farida da Nana suka shigo office din dukansu police din suka kalla murmushi yamusu, Principal tace “Baban ku ya aiko akaiku wajen aikinshi za’amuku wani interview” dasauri Farida dake kallon mutumin tace “dama kaine Aliyun da Baba yake yawan magana”? Gyadamusu kai yayi tareda mikama Nanah hannu yace “muje” makemai kafada tayi takama hannun Farida tarike tace “hannu Baba kawai nake rikewa Baba yace babu kyau rike hannun wasu maza” mugun kallo Farida tamata alamun tadaina rashin kunya hakan yasa tai shiru yana gaba suka binshi abaya har zuwa wajen motan baya yabude musu duk suka shiga suka zauna suna gaida dayan police dasuka gani agaba sannan yazagaya yashiga mazaunin direba yatada motan suka shiga hanya daga Nana har Farida sukai shiru Farida sai kallon cikin motan take dataji yana wari wari kaman na wiwi, sundanyi nisa atafiyan sannan Usman yama dayan sign hakan yasa yabude wata leda ya zazzaga hoda a hannun yajuyo da kanshi yace “girls” duk sun dago kai sun kalleshi kawai ya hura musu hoda, ihu Farida tayi tana kakkabe hodan tace “mehak……..” bata karashe maganan ba luuuu kawai ta zube itama Nanah haka dasauri yakira Wike yace “Oga operation successful gamu nan mun dauki hanyar palace” dasauri yace “muma yanzun nan zamuyi grabbing babban.”
Wannan kenan.

Wani kalan shan gaban Keken Van din yayi saida keken yaci bala’in burki dudda haka saida suka daki van din. “Subhanallahi” Yasmeen dake cikin keken tai ihu daidai Wike yabude gaban motan yafito yace “kasha wiwi ne baka ganin gabanka” shima azuciye Mai keken yafito yace “kaine kasha wiwi dan kaine baka ganin gabanka” Yasmeen zaro idanu kawai take ita kadai acikin keke tana kallonsu, dayan mutumin dake tareda Wike ne yasauko daga motan yana kallon mai Keken da Wike yace “dan Allah kuyakuri bari na duba passenger ko taji ciwo” yabar mai keke da Wike na chachan baki, baya yaje inda Yasmeen ke zaune kallo daya tamai tasauke kanta kasa tana kara kankame jakan school nata ahankali yace “sannu baiwan Allah kinji ciwo ne” girgizamai kai Yasmeen tayi batare data kalleshi ba, dan jujjuyawa yayi ganin babu mutane wajen yasa yakai hannu aljihun shi yazaro wani handky yace “to ga handky kishare fuskanki kinata zufa” yay kaman zai bata hanky hakan yasa Yasmeen tadago kanta danna mata hanky yayi ahanci tana mitsi mitsi yana kokarin magana da ihu hango haka yasa Wike yawani fizgo mai keken ya matseshi jikin mota yaciro bindiga yadannamai aciki yace “kawai ka tsaya ahaka kona harbeka wacce ka dauko nake bukata bakaiba” zaro idanu mai keken yayi fitsari na gangaromai jin bindiga acikinshi, Wike yajuyo yana kallon keken daidai Yasmeen takarasa passing out, chak Guy din yadauketa yafito da ita Mai keken na kallonsu van din yabude yasata aciki sanna yarufe yazaga da gudu yadhiga gaba yace “come on Wike” wani kalan wurga mai keken Wike yayi bayan ya fizge key keken sannan yashiga mota sukaja motan da mugun gudu sukabar wajen.✨KYALKYALIN KAUNA✨

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣2️⃣

Maryam Eygpt abaya gidane na abayoyi daban daban na Egypt da sauransu, tana bada sari tana saida daidai abayanta are damn affordable, click on this link and join her group.
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

Yana zaune kishingide acikin office dinshi ya lumshe idanu kaman wanda ke bacci akai knocking, batare daya bude idanunshi ba hannunshi ya mika ya danna wata botur hakan yasa aka bude kofan office din aka shigo, anatse Dan ya maida kofan yarufe yajuyo yataho zuwa gaban table din, cikeda girmamawa yace “Sir Wike yakawo girls din” shiru yayi still idanunshi a lumshe batare dayay motsi ba, kusan 2min yayi ahaka sannan yabude idanunshi ahankali sundanyi ja kadan ya zubasu akan Dan, sauke kanshi Dan yayi kasa, ahankali yace “kayi abinda nace kama dakin?” Gyadamai kai Dan yayi yace “yes sir” tashi yayi ahankali dagakan kujeran yadauki kwalin tabanshi dake kan table yazaro daya yasa abaki yadauki lighter ya kunna sannan yafara tafiya kadan kadan yana busan taban yatafi zuwa wajen babban window dake dakin dakenan da wasu hadaddun plain design milk curtains, wani dan remote dake gefen labulen dake makale a bango yakai hannu yataba hakan yasa window yabude, garden ne lafiyayye abayan window da flowers but daga window kana iya hango wani separate building again wanda yakenan ta bayan gidan, ga yaran Wike tsaye gaban flat din rike da bindigogi suna gadi, taban yakai bakinshi ya zuka ya busar idanunshi kyar akan building din kaman mai tunanin wani abu, hannunshi daya yakai yatura a aljihun wando dayan hannun kuma rikeda karan taba yana zuka yana kallon building din chan yace “take that phone kamini snapping nasu all 3 together” dasauri Dan yace “sir the girls are unconscious” batare daya juyoba yace “that’s how I want the pics” dasauri Dan yace “yes sir” yawuce gaban table din wannan special phone din daya kira Baba dashi yadauka yawuce yafita daga office din, Maheer na tsaye yana shan taban yana kallon Dan yawuce yaje building din yashiga ciki ko 1min baiyiba acikin dakin ba yafito duk Maheer na kallonshi ta window yadawo, kai tsaye wannan karan yashigo office din har inda Maheer yake tsaye gaban window yazo yamikamai wayan yace “gashinan nayi hotunan” ko juyowa baiyiba balle yayi alamun karban wayan saida yakarashe shanye taban tass sannan yamikamai hannu batare daya juyoba, samai wayan yayi a hannu hakan yasa yadawo da wayan gabanshi ya danna screen din tai haske saiga Yasmeen, Farida dakuma Nanah, dukansu zazzaune akan wasu kujeru irin na kulle mutanen nan, kujerun nada belt tawajen hannu da wajen kafafu duk an kulle hannuwansu da kafaffuwansu da belt, dukansu idanunsu lumshe suna bacci kansu ya lankwashe babu wacce tamasan inda kanta yake, kusan 1min yabata yana kallon hoton sannan yasa fingers dinshi yashiga scrolling yana kallon 5 different pics da Dan ya dauka nasu checking and rechecking dan tabbatar babu wani abu dazai incriminating ko sanar da komi game da inda suke, sannan yajuya ahankali yakoma kan kujeranshi hoto daya ya zaba cikin hotunan yay sending nashi as MMS ma CP tareda kashe wayan dip sannan ya ijiye agogon hannunshi ya kalla yace “today is Friday yeah”? Dasauri Dan yace “yes Sir” tashi yayi yadauki wayanshi kadai dagakan table din yawuce batare daya jira Dan yabudemai kofa ba yabude da kanshi yafice yawuce sama dakinshi yashiga lafiyayyen wanka yayi yafito ya goge jikinshi yawuce closet yana tsane kanshi wani Riga da wando yadauko na jean dark blue da farin riga yadawo ya shirya tsaf bayan yagama wankan turare, dadduma yadauka ya shimfida sai alokacin yay sallan asubahi sannan yatashi yafito Dan na falo ganinshi yasa yay wajen kofa budemai yayi yana zuwa yafice yace “take me to mosque”.
Chapter 18 · 0% Book details