← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 145

Sashe 59

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba" Farida tatad! ahankali tareda sauke ijilyan zuciya ganin yafita takalli Yasmeen tace "Allah yasoki bai kamaki kina waya ba hope dai kin katse wayan"? Dasauri Yasmeen tasa t hannu taciro wayan daga kasan pillow ga mamakinta Maheer nakan layin dasauri takai wayan kan kunnenta oda tace "daman ban kasheba kai mesa baka kasheba" ahankali yace "ban sallameki ba" "to me kakeso?" Yasmeen tai maganan tana kallon kofan su jin antaba ganin Sa'a ne tashigo yasa tasauke ijiyan zuciya, jin shiru baice komiba yasa ta turo baki cikin kunkunai tace "ni zanyi bacci" almost 10secs baice komiba kafin chan yace "bakida kunya ko" dan dariya kadan tayi mara sauti tace "toka barni na kwanta bacciii" yanda taja baccin saida yaji aranshi, anatse yasauke ijiyan zuciya cikin tattausan murya yace "good night Fateema" kasa magana tayi tai shiru tama rasa takamaimen metakeji danji tayi inama baice good night ba, anatse yace "zanzo ranan Sunday by 3, 4 zan tafi" cikeda tsiwa tace "karka sake kazo gidan mu ni, kuma bara'a aureka ba din, bye" dip ta katse wayan. [8/1, 5:44 AM] AMINA KABIR CAPS: Jin ana tambayan Ammi ina zata da jaka yasa Farida da Nana dasukai tsuru tsuru adaki suka fito da gudu, ganin Ammin su rike da Babban akwati kowa na gidan ya zagayeta banda Baba dake gefe tsaye yana kallonsu yasa sukai wajenta da gudu gain yanda Yasmeen ke kuka tarike jakan gam yasa yasa suma duk sukasa hannu suma suka rike suka fashe da kuka duk sukace "Ammi ina zaki"? Anatse Baffa dake kallon yaran yace "please Maman Nana calm down kodan sabida yara matan nan uku dake kuka agabanki dan Allah kinji" dago kanta ahankali Ammi tayi duk yanda taso hawayen datakeji takasa fashewa tayi da kuka tace "Baffa nagaji, for 20yrs yanzu kullum cikin jure cin mutuncin Baban Nanah nake kala kala kan yaran nan amman yau for the first time yazagi character na, yazagi tarbiyana ace ina lalata mai vara zan bata mishi Yasmeen tafara Iskanci abinda yake nufi kenan, i will not take that, nahakura da aurenshi, yaran ma na barmai tunda shine the perfect father and mother ma duka yaran nan wh wIh na barmai karyaji komi"tai maganan tareda kallon su Yasmeen da Nana da suka rirrike akwatin ta suna kuka tace "ku saki akwatin nan" cikin kuka Yasmeen tace "Ammi dan Allah kiyakuri" Farida tace "Ammi dan Allah kada kitafi kibarmu" Nanah tace "Ammi idan zaki tafi to saidai kitafi damu duka ko Anty Yasmeen baramu zauna da Baba mai mana fada ba harda ke ko Anty Yasmeen" Gyadamata kai Yasmeen tayi tana kuka, sakin musu akwatin Ammi tayi tabi ta gefensu tawuce dasauri suka bita suna kuka zasu riketa ta daka musu tsawan da saida kowa ya firgita agidan tanuna Baba da hannunta dake tsaye kallonta kawai yake tace "kuwuce kutafi waien Baban ku wlh duk wacce ta tabini saina gaura mata mari harke Nana" duk wanda yaga Ammi yasan tai fushi yau bana wasaba, tsayawa yaran sukayi juyawa tayi tawuce Farida da Nanah suka rungume Yasmeen suna kuka sosai ganin da gaske Ammi take tafiya zatayi tabarsu, daidai Ammi tasa hannu zata bude gate duka yan gidan babu wanda yasan lokacin da Baba yamaje wajen hannunshi yasa yarike hannunta yacire daga gate din yajuya yasa all d sakata na gate din sannan ya tsaya jikin gate din yakalleta cikin fushi soyayya yace "tunda fushi kike aani ai nina bata miki rai ko vent it out on me amman bazaki tafi kibar yarana suna kuka ba wh, kome zakimini kimin" sosai Ammi takalli Baba kaman yanda yake kallonta shifa mai hali bazai taba chanzawa bane, yanzu bai tsayarda ita dan kanshi ba saidan yaranshi, idanunta sunyi jazur tana kallonshi da takaici tace "Ibrahim tashin mini daga jikin gate" "cikeda dakewa dakuma taurin kai Baba yace "bazan tashiba" cikin fushi Ammi tace "nace katashi idan nai loosing temper na zan iya abinda zanyi nadama daga baya" anatse Baba yace "do your worst amman dai baraki tafi ki barmini yara in agony ba kin haifesu zaki zauna mucigaba da basu tarbiya tare har zuwa ranan da Allah zai karbi rayukan mu" fashewa da kuka kawai Ammi tayi tashiga kaima Baba duka akirji tace "nace ka matsamin nafita nabar gidanka ka matsa katashi nace, nagaji nagaji nagaji nagaji dakai Ibrahim" batare da Baba yahanata ba yace "nikuma nan gaji dakeba zama dake yanzu nafara" gain haka yasa Baffa yakalli kowa yace "ku wuce dakin Yaya ku harsu zasu daidaita" dukansu dakin Yaya suka shiga harda su Yasmeen Baffa yamaida kofan yarufe yasa sakata. Duk ta inda Ammi tasamu kaimai duka take tana kuka rungumeta Baba yayi tsamtsam ajikinshi gain babu kowa ahankali yace "dan Allah kiyakuri kiyafemini I am sorry please, haba wife ni zaki toxarta kice zaki tafi ki barni tayaya zanyi rayuwa babu ke Dan Allah ki yakuri" ina Ammi bata jinshi dan ranta yabaci, daukanta yay da karfi da yaji yatafi da ita dakinsu ya maida kofan yarufe yasa sakata yajuyo zatai magana yakama bakinta yawuce da ita uwardaka duk gardaman Ammi saida Baba ya wanke laifinshi tass azuciyanta sukai wanka yafito da jallabiya dan zuwa masallaci, dakinsu Yasmeen yabude yagansu zugum suna zaune idanunsu jazur gwanin ban tausayi kaman was marayu, ahankali yace "kutashi kuje kuyi salla" dasauri Yasmeen tace "Baba Ammi ta tafi" kafin Baba yabada amsa Farida tace "Baba kayakuri" dasauri Nanah cikin tsiwan yarinta tace "Baba kadainama Ammin mu fada, munason Ammin mu sosai ko Anty Yasmeen" kasa amsawa Yasmeen tayi Baba yadade yana kallonsu kafin anatse yace "Ammi bazata ko'ina ba, nabata hakuri and I promise bazan karama Ammin ku fada ba dagayau Baba yay kuskure Ammi tayafemai, kuje kuga Ammin ku" dasauri dukansu ukun suka tashi ta gefenshi suka fita suka wuce dakinta daidai Baffa vafito wani kalan mugun kallo yama Baba dasauri Baba yace "Baff..." Hannu Baffa yadagamai yace "I don't have anything to say to you duk wannan abubuwan dakake sabida bakason Yasmeen tayi aure ne ko, to bari kaji Ibrahim muna dawowa daga sallan nan zan kira Yasmeen inhar ta aminta tana sonshi zan aika amin binciken yaron inhar yasami shaidan kirki aura da Yasmeen zany bana bukatan ko sisin ka mara mutunci kawai agabana kadaga hannu zaka kaiwa matarka mari kai son yara haukan ne metayi da bayida kyau? Tsirara kazo kaga Yasmeen dazaka fara haukan nan" Baki Baba yabude zai bama Baffa hakuri kawai yawuce abinshi. Ammi na zaune afalo duk su Yasmeen suka shigo duk suka tsaitsaya wajen kofa kallonsu tayi jitayi she's feeling guilty saisa bata taba biyema Baban su tayi fada dashi agabansu dan fada na affecting yara sosai, hannu tabude musu da sauri sukai jikinta, Yasmeen tace "Ammi dan Allah kiyakuri kinji kidaina barin maganganun Baba na tabaki yana sonki sosai he didn't meant maganan dayayi wlh kinji Ammi"? Gyadama Yasmeen kai tayi sannan tai murmushi tace "yanzu enough of fadana da Baban mu mun shirya dan haka ya isa kuje kuyi salla" dukansu murmushi sukayi suka juva suka fice aga dakin tabisu da kallo. Tana zaune awajen Baffa yayi sallama daga waje anatse tace "shigo Baffa" shigowa Baffa yayi shi kadaine yasami kujera yazauna yace "Maman Nanah babu wacce nake yabo agidan nan akan hakuri kaman ke nasan halin kanina sarai akanme zaki biyemishi kuyi fada gaban yara da kowa" ahankali Ammi tace "Baffa kavakuri bazan karaba" murmushi yayi yace "Allah yamiki albarka" anatse Ammi tace "Ameen" kafin ahankali tace "Baffa dan Allah ka tsaya akan lamarin auren nan da kanka, soyayyan da Baban Nanah kema yaran nan yana neman rufemai ido wlh aurar da Yasmeen ne bavaso yayi kwata kwata Baffa to idan bai aurar da ita ba mezaiyi Bokon bata ganewa gwarama Islamiya dasauki amman shima wajen rubutu duk abu daya, dazu bakaga kukan datayi da rana ba kan bata rubut komi a test din dasukayi ba, Baffa to tunda Allah yafito mata da miji yaro natsasse yanada aikin yi dazai rufamus asiri ya iya ciyar da ita to me wannan abubuwan dayakeyi eh Baffa" jinjina kai Baffa yayi yace "hakane, kada kidamu komi na hannuna anima zan kira Yasmeen wajena ni kadai tabani amsa zan aika shakikai na tareda Baba karami aje ayimin bincike idan komi lafiya lau zan kirasu ne Azo ada rana duk taurin kan Ibrahim bai isa yahanani abinda nasi yiba" gyadamai kai Ammi tayi tace Back "nagode Baffa" tashi yayi jin ana kiran Isha'i dan musamman sabida ita yau bai tsaya yaji karatun Umdatul Ahkam da akeyi a mosque dinba yabarki su Baba can yazo tabata hakuri yanata sallama yatafi. Wuraren 10 Baffa ya aika Yaya data kiramai Yasmeen, Yasmeen dahar sun kwanta gyangyadi yasoma kwasanta dan tuni Baba yazo yamusu sallama Yaya tabude kofansu dawuri dukkansu suka kalleta, Yasmeen takalla tace "kizo Baffan ki na kiranki" ahankali ta sauka daga gado, hijabinta tadauka tasaka sannan tabi bayan Yaya suka I fito waje, anan waje Yaya takamo hannunta cikin whispering tace "Yasmeen dan Allah Baffan ki ya tambayeki kice eh ki aure abinki kihuta. yaro kyakkyawa ga mota ga aikin yi me kikeso? Ba gwara aure ba da bakin masifan Baban ki da takuranshi, muje muje" binta abaya Yasmeen tayi kirjinta na bugawa dim dim dim da sallama tashiga dakin, Baffa ne kadai zaune kan kujera yana kallonta Yaya tawuce ta zauna kusada shi, zama tayi ahankali akasa tace "Baffa gani" murmushi Baffa yayi yana kallonta cikeda so yace "nakiraki ne namiki tambayoyi kan mutumin dayazo wajenki yau" yadanyi shiru yace "ance malamin kune a FCE?" Ahankali ta gadama Baffa kai tace "eh Baffa" shiru Baffa yayi kafin chan yace "inaso ki natsu ki bani amsa mai kyau dan koba komi at least ke kin had da Maheer din countless time amakarantan ku koda bai taba miki magana a school ba, atleast kin ganshi, kin sanshi, kinga yanayin halayanshi da yanayin rayuwanshi da dabi'un shi, sannan kuma yau yazo wajenki dan haka" Baffa yay dan gyaran murya cikeda kamala dakuma taushin murya yace "kin amince kin yarda da ahada Auren ku Fateematul Zara'u?" Wani kalan faduwa gaban Yasmeen yake batasan lokacin data shiga wasa da yatsunta na tasauke kanta akasa saika hawaye sharrrr, Yaya tai murmushi tace "saisa kap gidan nan nafison Yasmeen tafi halinsu na arziki
Chapter 59 · 0% Book details