← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 145

Sashe 48

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har gari ya waye bai runtsa ba Dan yakira wuraren 7 yataho dakinshi, ba karamin mamaki Dan yayi ba ganin Oga na parking kayanshi da kanshi a closet, Maheer dake hada uban kaya cikin desginers LV suitcases nashi ne yace “kakai sabon motan danai order airport kai parking”? “Yes sir” Dan ya amsa, gyadamai kai yayi yace “yanzu direban will take us to airport sabida yadawo incase wani ya tambaya ya sanardasu yakaimu airport cus I know that woman will ask” gyadamai kai Dan yayi, Maheer yace “daganan we take the car mutafi school dinsu” dasauri Dan yace “I thought zamu fara kai luggage gidansu Hamad” girgiza kai Maheer yayi ahankali yace “I can’t wait to see her” kaman wanda yatuna wani abu saikuma yajuyo yakalli Dan da sauri dan baisan lokacin daya fadi abinda yaceba, sauke kanshi kasa Dan yayi yana hadiye murmushin dayakeji hakan yasa Maheer yahade rai yace “makesure baka kwashi wayan nan suit din as kaya ba, I want you dress like a student da backpack abaya” gyadamai kai Dan yayi yana murmushi yace “yes sir” dan murmushi kadan Maheer yayi yace “take the luggage to car” daukan akwatunan Dan yayi yafita dashi yana mamakin yanda kawai just like that Oga yafada soyayya mai karfi da yarinyar dayay kidnapping shi kanshi bai sani ba he’s in love, on the other hand kuma is Hajiya, dudda su Nas da Wike yasan suna gulma kaza kaza something is going on tsakanin Boss da Pablo bawai they’re sure bane but shi yasan something is definitely going on, ko jiya yana falo yaji Oga da Boss suna having sex, he knows Oga bayason Boss dan babu soyayya akan idanunshi tattare da Boss kaman yanda yake ganin soyaya a idanun Oga tattare da yarinyar CP nan, he is very worried baiso Oga to get himself into trouble, duk yanda yakalli abun is trouble dan soyayyan yarinyar CP nan da Allah ya dauramai kadai is trouble gakuma Boss, tsayawa yayi gaban mota ahankali ya lumshe ido yace “Holy ghost fire please protect My Master, protect him from any trouble and keep him safe” bude idanunshi yayi yadauki jakan ya wurga a mota daidai nan Maheer yafito yana danye da wani suit dark blue yamai fitinannen kyau yazo yana murmushi yashiga mota yace “hope ka karbomini papers din dana bari a motan Hamad”? Anatse Dan yace “yes sir” murmushi yayi yashiga mota yaji dadin yanda zai bar gidan Hajiya na bacci. Maida kofan Dan yayi yawuce yashiga gaba direba yajasu zuwa airport.

Suna kaiwa parking direban yayi Dan yafito yasauko da akwatinsu yabudema Maheer kofa yafito ya sallami direba sanan suka wuce ciki direba yawuce dan no parking ne wajen, saida yatafi Dan yace “sir wait here bari naje nadauko motan mu” gyadamai kai Maheer yayi Dan yawuce bai dade ba yadawo dawata 2013 Toyota Camry ash color glass dinta tinted, baiso yay amfani da babban mota da zaisa afara tambayan waya shi ko yay raising suspicious, shiga motan yayi Dan yaja motan, ta glass Dan ke kallonshi sai murmushi yake yakosa sukai school din kaman bazasukai ba.

A parking space na department dinsu sukai parking a roll na gaba ta yanda kotayaya Yasmeen tazo zai ganta, dan Juyowa Dan yayi yakalleshi yanda yake kallon waje yace “Sir bara muje office ba tukunna naga baa fara zuwaba” paper hannunshi yakalla yace “tanada lecturer ba 10, 11-1 shine lokacin dazanje auditorium dinsu for English itama zatazo wajen” gyadamai kai Dan yayi yace “do you need anything inje in samo maka”? Girgizamai kai Maheer yayi fuskanshi na kallon waje yace “a’a”.✨KYALKYALIN KAUNA✨

✍🏻M SHKUR

EPISODE 4️⃣2️⃣

Jama’a ina sababbin amare da matan aure dasuke so su koyi abubuwan da basusan da akwaisu daba, M shakur dinku is back again with another banging class na MATAN AURE dazan fara muku next month dazaran nagama wannan novel din na KYALKYALIN KAUNA💃💃💃

Classes namu asabar da lahadi ne na tsawon wata daya wato 4 good weekend classes kenan.
Ki shigo class dina lemme teach you how to catch your husband a hannu ba kayan mata ba magani tsabagen iyawa kawai da kwarewa a harkan oza room🥰
Registration is 1k
Chat me up idan kinason shiga wannan class din nawa.
wa.me/+2347012181461

https://vm.tiktok.com/ZM2DAkuct/

9:30 tagama shiryawa dan sosai take murna yau Baba yabarta takoma school, wani Riga da skirts na material ne ajikinta mai kyau, kanta anyi shuku dayayi mata kyau sosai yakara fito da goshinta babu komi a fuskanta jakanta ta dauko da maroon hijabinta har kasa gogagge a hannu tafito daga dakinsu zuwa dakin Ammi, da sallama tashi Baba ne kadai zaune a falo ya shirya tsaf cikin shadda fara dan yau Friday yasa hula tamai kyau ganinta yasa yace “kin shirya”? Gyadamai kai tayi tace “eh Baba” tashi yayi dagakan kujeran yace “muje to” daidai Ammi tafito daga uwardaka tace “tsaya kagani nasa mata kwalli haba yarinya kullum idanu fari kaman ba budurwa ba” turobaki Yasmeen tayi ahankali kaman zatai kuka dan ita bataso, tsayawa tayi Ammi tasamata kwallin aiko take ta rikida, murmushi tayi Ammi tace “to saura janbaki” baki Baba yabude yace “banson shirme school zata ba gasan kwalliya ba” hannunta Ammi taja zuwa uwardaka tace “kai dama kafison kaga yaranka fuskokinsu kaman na maza basasa komi, Bakasan Yasmeen budurwa bace tana jami’a bata gayu ba saurayi” akunyace Yasmeen tace “Ammi” dungure mata kai Ammi tayi tace “dalla barni nai magana kunyan Baban naki kike ai dashi nake, sa’o’inki na gidan miji, ni wlh addu’a na ba dare ba rana Allah yafito miki da miji Allah baki miji nagari mai hankali” tai maganan tana daukan janbaki pink ta shafa mata a lips sannan tadauki brush ta gyara mata gashin giranta ita kanta Ammi saida tasake kallon Yasmeen din tace “ke kinganki Alhamdulillah, Allah kabani diyar yar kyakkyawa, yar budurwan Ammin ta iyyee” lokewa Yasmeen tayi akunyace daga falo Baba yace “let’s go Yasmeen shirmen mamanki yayi yawa” karban hijabinta Ammi tayi ta warware tasamata “wlh kinyi kyau Yasmeen” Ammi tafadi ahankali juyawa Yasmeen tayi tace “bye Ammi” Baba harya fice sallama Yasmeen tama su Yaya da Hajjo sannan tafice motan Baba tashiga Baba yatada motan yafara tafiya sundanyi nisa sannan yace “I don’t want kiyi paying attention to maganganun Mamanki, banson shirmen samari, kada kiyi kuskuren tsayawa kula samari awaje, inhar yaro nagari ne dayasan darajan iyaye idan kuma yana sonki da gaske kafin ma yakulaki zaizo yafara sanarda mu iyayenki mubashi izinin magana dake, inhar Allah yabaki miji bazan hanaki aure ba, amma dai concentrate on school okay banda wasa, kallon maza kokuma magana da maza am I clear”? Ahankali tace “eh Baba, naji” “kina bukatan wani abu”? Girgixa kai tayi tace “a’a” school sukakai Maheer na zaune a motanshi kaman a mafarki yaga Yasmeen tabude gaban wata mota datai parking gaban classes na department nasu tafito hakama Baba, wani kalan sanyi Maheer yaji ajikinshi yakara zuba mata ido yana kallonta tundaga kan takalmin datasa akafa zuwa saman hijabinta, zagayowa Baba yayi yazo ta inda take yana kallon fuskanta hannunshi yakai aljihunshi yazaro handky baiji kunyan kowa da dalibai dake zuwa wajen ba yace “wannan abin da mamanki tasamiki yay yawa” share janbakin yayi yarageshi sosai yarage kadan sannan yakalleta yamaida hannunshi aljihu yazaro dubu biyu yaciro jakanta ya karba yasa 2k ciki yace “ga transport naki idan kun tashi 5 zaki gama lectures yau ko”? Gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba” karban jakan Yasmeen tayi Baba yakama hannunta yawuce da ita har ajinsu, class nasu yashiga sai kallonsu ake Yasmeen tasauke kanta akasa Baba nabin kowa na ajin da kallo just to makesure yarshi is safe wani kujera yakaita yace “take care kiyi karatu da kyau ki” gyadamai kai tayi duk kunya yacikata, kanta ya shafa kaman yar yarinya yajuya yafita daga ajin dalibai kowa na dariya kasa kasa wasu na cewa Daddy’s gurl, fitowa Baba yayi daga ajin duk Maheer na kallonshi jujjuyawa yayi yakalli ko’ina kaman mai duba wani abu sai chan Maheer yaga ya maida idanunshi wani bangare daban hakan yasa yakalli wajen dasauri Aliyu yagani Baba nama magana da ido, wani kalan murmushi yayi yace “CP if I want ur daughter ko security dubu kasa I will get her” dan dariya yayi yana kallon Baba daya wuce yatada motanshi yatafi, hakan yasa Maheer yace “let’s leave daganan kaini office dina”.

11 suka fito daga lectures din, jakanta tadauka dan wucewa auditorium yin English, ahankali take tafiya ita kadai dan batada kawa bata iyama yan ajinsu magana kodan harda kowa jijji dakanshi yake as per new student oho, ita kunyan abinda Baba kemata ma yasa ko dagakai ta kalli wata ko wani a aljin bata iyayi, wucewa tayi tana tafiyan nan ahankali anatse zuwa auditorium ancika sosai abinka da yan different department anzo ayi english da kyar tasamu sit a tsakiya ta zauna tareda ciro handout nata na english tana dubawa sai hayaniya ake kaman gidan biki, all of a sudden taji ajin yay tsit kaman anyi ruwan sama an dauke hakanan taji feet nata sun mata wani irin sanyi saiga kamshin turaren da har yau gobe batajin zata manta da kalan kamshin nan ba dawani kalan sauri ta dago kanta ta jujjuya gefenta kaman wani abu take nema saikuma chan kaman ance ta kalli chan stage gaban aji ido da ido tayi da Maheer dake tsaye yasa wani dark blue suit idunshi sanye da glasses bakake amman tasan ita yake kallo, yayi mahaukacin kyau kaman ba dan Nigeria ba, gently yakai hannunshi yazare glasses na idanun nashi yana kallonta still faduwa gabanta ya mugunyi dasauri tadafa table, almost cikakkun 2mins yayi yana kallonta kafin yajaye idanunshi daga kanta yadan kalli student din tareda sakin little smile yace “good morning student I’m Maheer M Maheer your new English master” wani kalan tafi ajin yadauka dan he’s so charismatic kanajin yanda yake turenci kasan ba’a nigeria yay karatu ba ga kyau ga pink lips ga gayu ga tsayi, kowa kallonshi yake both maza da mata babu kyafta idanu.
Chapter 48 · 0% Book details