← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 145

Sashe 43

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ganin takasa magana sai kuka take yasa Aliyu yace “muje nakaiki wajen Baba” ganin taki tafiya sai kuka take yasa ahankali yakai hannunshi zai kama nata, boye hannunta tayi abaya sannan tafara tafiya hakan yasa yace “yauwa muje” bude mata motan yayi ta shiga ya maida ya rufe shima yashiga daman fitowanshi kenan kuma Babane ya aike shi kwana yayi yakoma zuwa police station din shiga ciki yayi yay parking wajen parking, ganin ko Hajibi babu ajikinta sai dan kwalin data daura awuya yasa yaciro wayanshi dialing number wayan Baba yayi, wayan na gab da katsewa Baba ya dauka anatse yace “Aliyu” dasauri Aliyu yace “Yallabai I just found Yasmeen akan titi gatanan amota na kafito banso na……..” katse wayan Baba yayi baima jira Aliyu yakarasa magana ba, gudu gudu sauri sauri Baba yafito daga cikin police station direct wajen parking yaje zuwa wajen motan Aliyu Yasmeen bama ta luradashi ba sabida yanda take kuka Baba yadade tsaye yana kallon Yasmeen ta glass he can’t believe itane kafin ahankali yabude kofan motan dasauri tadago kanta ganin Baba batasan lokacin datai wani jumping tafito ba kawai tafada jikin Baba ta kankameshi, kankameta Baba yayi yana shafa bayanta kaman zai haukace sabida dadi dagota yayi daga jikinshi ya wani kalan mammanna mata kiss agoshi kawai yasake sata ajiki duk Aliyu na kallonsu, yanda Baba keson yaranshi yadade baiga wani dan arewa mai son yara haka ba, sun dade ahaka ganin kukan yaki karewa yasa Baba yabude bayan motan yashiga da ita shima yashiga tareda rufo kofa anatse yace “take us home Aliyu” tada motan Aliyu yayi shikuma Baba kawai ya kankameta yayi shiru yanabin tundaga kan kafanta dayaga bandage da kallo zuwa goshinta dabai gama dawowa daidaiba kaman yatayata kukan datake yakeji, he’s so happy at the same time sad, wuraren 7:30 suka kai gida ga yan sanda akorfar gidansu guda uku, bude bayan mota Baba yayi yafito tareda mika mata hannu ahankali yace “fito” fitowa tayi ahankali yana rike da ita yawuce yabude gate babu kowa a tsakar gidan banda Ammi da ita kadaine zaune abakin kofanta akasa babu ko tabarma tasa hijabi hannunta rike da charbi tanaja tana kallon sama idan ka ganta zaka iya kuka harta rame ta chanza kaman ba Ammi ba, jin an taba gate saida tadanyi motsi amman bata juyoba, ahankali Yasmeen dake tsaye wajen gate din cikin wata kalan raunanniyan murya ganin Mamanta tace “Am…….Ammi” wani kalan juyoda kanta Ammi tayi jin muryan Yasmeen, ganin Yasmeen gatanan Yasmeen dinta sanye da kayan datasa ranan dazataje makaranta amman banda Hijabi danda Hijabin Farida tadawo yasa Ammi ta shiga tattaba bango kaman makauniya tana kokarin tashi amman takasa sabida yanda kafanta yayi sanyi, dawani kalan gudu Yasmeen ta taho batai wata wataba tawani kalan shige jikin Ammi tace “Ammiiii” kankameta Ammi tayi tace “Yas…..yarinyana kene, Yasmeen dina” tafashe da kuka bude kofa Yaya tayi jin hayaniya dan gidan nasu yadawo kaman na makoki tun bayan an sace yaran, ganin Yasmeen yasa tawani kwala ihu “Baffa fito Yasmeen” kowa na gidan fitowa yayi hadda su Farida da Sa’a haduwa sukayi dukansu suka kankame Yasmeen, kowa na gidan Hamdala yake ganin Yasmeen, sun dade ahaka sannan Ammi tasake ta hannunta takai ta daura kan goshinta inda Ya kumbura dakuma kafanta da hannunta duk tana dubawa, wani kalan murmushi Yasmeen tayi ahankali tace “jiya naji ciwon da ina kokarin guduwa ta window dakin danake, don’t worry Ammi lafiyana kalau” Gyadamata kai Ammi tayi sai kuma tasake jawota jikinta ta kankame fincike Yasmeen Yaya tayi daga jikin Ammi tace “ke Maman Nanah bakida kawaici kinsan kwana na nawa bama bacci sabida Yasmeen dina, zonan diyan kirki” tarungume Yasmeen tace “barka barka Allah ya fito mana dake” karasowa wajen Baffa yayi ahankali ya rungumeta yama kasa fadin komi sannan yacirota daga jikinta tareda shafa mata kai hakama Baba karami da Hajjo Ammi sai bin Yasmeen din take da kallo, kafin ta tashi da sauri bucket tadauka tawuce kitchen dasauri ruwan zafi ta debo ta sirka bucket din yacika tadauko dasauri Baba yazo yasa hannu zai karbi bucket din wani kalan kallo Ammi tamai hakan yasa ahankali yacire hannunshi dagakan bucket din, wucewa Ammi tayi da bucket din dakinta dan bazama tabarta tai wanka atsakar gida ba bayinta ta ijiye tafito takalli Yasmeen din dahar ta zauna kusada su Farida da Sa’a duk sun rirrike mata hannu su Baffa kuma duk sun tsaya kallonta suke Ammi tace “zomuje kiyi wanka” tashi tayi ahankali tabi Ammi ciki hakan yasa Baffa yakalli su Yaya da Hajjo dasukai charko charko yace “aje ahada karin kumallo” yakalli su Farida yace “kuje ku taya iyayenku aiki a kitchen” duk suka watse Baffa yawuce yashiga dakinsu hakan yasa Baba ahankali yawuce yashiga daki afalo yazauna yay shiru yanajin Ammi da Yasmeen.
Chapter 43 · 0% Book details