← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 145

Sashe 132

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Anatse Alkali yana kallon Maheer yace
"kotu najira saki Fateema" bude idanunshi Maheer yayi yakalli Alkali sunyi jaaa kaman jini, baida ma karfi, maganan shi ma bata fita da karfi ahankali yace "bazan iya sakin Matata ba!" Wani kalan zabura Baba yayi zai mike tsaye Ammi ta fincikoshi cikeda bala'in fushi tace "Wai me haka kaine alkali? Kana abu kaman Today dattijon banza, dan Allah kadaine halin kananun mutane haba Babba babba ne fa" Ganin yanda ran Ammi yake abace kuma yasan shi bai bata mata rai ba yasa yadanyi shiru ya natsu yacigaba da kallo.
Anatse Alkali na kallonshi yace
"kozansan dalilin dayasa bazaka iya sakinta ba"? Juyoda kanshi Maheer yayi yakalli Yasmeen da kanta ke kasa yayi shiru na kusan 1min kafin ahankali yace "sabida tana dauke da d'ana acikinta!" Wani irin zabura Baba yayi yamike tsaye gabanshi na mugun faduwa yace "karya yake Fateema bata da ciki dakaina nakaita asibiti an mata test!" Duka kotun aka juyo ana kallon Baba, cikin kakkausan murya Alkali yakalli Baba yace "yakamata kasan kotu kake ba gidan ka ba the next time ka kara magana batare da an baka hurumin magana ba kotu zata hukunta ka" ahankali Baba yakoma
10:17
yazauna jikinshi har rawa yake zuciyanshi na racing sosai, yakalli Yasmeen da tadago kanta takalli
Maheer gabanta nafaduwa sosai jin yace tanada ciki yace "karya yakeyi makirin yaro karki damu kinji".Alkali yakalli Maheer dake kallon Yasmeen yace "taya kasan tanada ciki?" Batare da Maheer ya janye idanunshi dagakan na Yasmeen ba dake kallonshi yace "sabida nina mata, kuma naji d'ana acikinta!"
10:17
Baba yabuga inda yake zaune yace
"maganan banza maganan wofi" Ammi ta ballamai harara tace "kadauka anama Allah wayau ne, bakaga komi ba abinda Allah yahada mu bamu isa muraba ba, bawai inason yaron nan bane Amman nasan menene kaddara, kuma Allah yatabbatar da cikin zanga yanda zakayi tunda ka dauki karan tsana ka dorawa yaro akai,
10:17
dukanmu nan har su Baffa haushin sa mukeji dan yamana laifi amman ba irin tsanan dakake mai ba, kabi duniya a sannu wih inba hakaba Allah saiyata nunamaka ishara"
10:18
wani kallo Baba kema Ammi zatai magana Alkali yace ayi shiru yakalli Maheer, gently Maheer yajuyo da kanshi yakalli Alkali yace "ina neman Alfarma koda kotu ta raba auren mu abari ta haifi abinda ke cikinta tukunna, banson d'a ko y'ata tazo duniya babu aurena akan mahaifiyarta"
10:18
kuskus mutane suka fara a kotun ana hakane da gaskiyan shi, this and that.
10:18
Sosai Alkali ke kallon Maheer, duk sanda ya kalli kwayar idanun yaron all he sees is a helpless, good, lonely scared youngman dake bala bala 'in tsoron araba auren nan,
10:18
yanda ake cewa criminal ne baiga alamun criminal a kwayan idanunshi ba dan yanada degree a criminology, yanada degree a psychology, banda haka an fara case din nan iyayen yarinyar nan natare
10:18
da ita in every step of the way, supporting her guiding her baiga ko mutum daya a kotun nan dake kama da Maheer bama balle yace ga iyayenshi koga yan uwanshi ba nan, bari yama koma baya, baya, baya a ijiye kasurgumin criminal ne, drug dealer Pablo Escobar ne, who is this young man? Alkali yay maganan azuci, kafin yajawo wani fresh plain sheet na paper ya ijiye agabanshi yature file din din dayake aiki agabanshi zuwa gefe yakalli
Maheer Anatse Alkali yace "who are you Maheer"? Kallon Alkali Maheer yayi jin tambayan da Alkali yayi, Alkali na kallonshi yace "ina iyayenka"?
10:19
Baba Makaho zai mike Hamad da
Malah atare suka rike Baba alamun kada yatashi dan sunason Maheer ya amsa tambayan nan, he should speak up duniya tasan wayeshi at all cost, Alkali yace
10:19
"ya akayi kazama Pablo Escobar?"
Alkali ya gyara zaman glasses na idanunshi yana kallon Maheer yace
"who are you young man?" Kasa magana Maheer yayi yay shiru kotu tai tsit kaman anyi ruwan sama an dauke ana kallon Maheer dan kowa nason yaji amsoshin tambayan, Alkali dake kallon Maheer kyar yace "zan iya raba auren nan dakaina, ko da aurenka akanta ko babu idan dai tanada cikin zata haihu kuma yaro naka ne an sameshi ta halas, but yanzu nabaka avenue to tell me waye kai idan you want to save marraige naka? Naganka, nakarance ka, naga yanda kakeson matarka, kayi kuma nadaman abubuwan dakayi, naga yanda kake girmama mahaifinta, duk naga hakan" Alkali yayi shiru anatse yace "tayaya zanbar auren ku bayan bama asan waye kaiba? Ba asan daga ina kafito ba daga wace kasar kake ba, mutanen dakakawo neman aurenka ba sune mutanen kaba, ba sune iyayenka ba, kafada ma kotu wayekai? Waye iyayenka? Tayaya kazama Pablo Escobar? Kazama drug dealer, kotu na bukatan sanin ka idan har kanason abar auren ku kaida Fateema!". Hamad, Malah, Baba dahar ita
Yasmeen sunji bala 'in dadin tambayan nan da alkali yayi,
12:07
koba komi yau kowa zaisan cewa ba shine Pablo Escobar ba, ahankali
Yasmeen kefadi aranta please speak up Maheer, speak up kaji, don't keep quiet today,
12:08
Baba da kowa needs to hear sannan susan u are not abinda suke tunanin you are, u are just a victim, speak up please Maheer dina, tai maganan tanakai hannayenta kan cikinta dudda bawai tasan tanada cikin ko batada shine ba amman ahankali tace "do it for our baby" hawaye yasake saukowa daga idanunta ganin yaki magana. 12:09
Agogon hannunshi Alkali yakalla yace
"10secs left idan baka amsa tambayana ba zan raba auren nan yanzu dan mahaifinta yariga yace anyi test batada ciki atashi daga kotu,
NINE....EIGHT......SEVEN SIX…FIVE…FOUR…THREE…TWO….
......." Ahankali Maheer yace
"sunana Maheer Maheer"
12:09
hakan yasa Alkali yayi shiru yadaina counting vace "continue, tell me your story, fara dagakan iyayenka" dan ijiyan zuciya Maheer yasauke ahankali yajuyo
da kanshi yakalli Hamad, gyadamai kai
Hamad yayi yasa hannu dasauri ya goge hawayen dasuka zubomai baiji kunya ba dudda tsakiyan kotu ne yace
"it's high time Maheer, open up, be strong"
12:09
kallon Hamad Alkali yayi yanda yaga yana goge hawaye yasa baice komiba yadube Maheer yace "ina jinka"
12:10
anatse Maheer yace "for verification da tabbatar da gaskiyan maganata, zaku iya kiran prison din KRIKRI na mata dake lagos state"
12:10
yadan fuzo da iska abakinshi kadan kana ganin yanda yayi kasan maganan is super difficult for him, ahankali yace
"sunan Babana Maheer Aliyu security ne dake gadin prison din"
12:10
rubutu Alkali yashigayi yana kallon Maheer, Maheer yace "sunan Mamana Hafsatu" yadanyi shiru yasake sauke ijiyan
12:10
zuciya ahankali yace "Mamana yar fashi ne dake tsayawa akan hanyan travelers da daddare ahaka aka kamata anan prison ita da Baba na suka hadu tayi cikina bayan dogon investigation tace Babana yamata ciki dalilin dayasa aka koreshi a aiki kenan ita kuma ta haifeni a nan prison"
12:10

yasakeyin shiru yasauke kanshi kasa kotu akai tsit babu abinda akeji sai yanda Maheer ke fuzo da iska trying not to cry, trying to be bold and strong, ahankali yace "uniform da Mamana ke sawa nada number 03 ajiki dakin datake is block D cell 71,
12:11

ina fadin all this ne dan kuyi verify maganata" yasake shiru, yace "I don't know meya faru government pardon Mahaifiyata sabida ni kan taje tacigaba da kula dani lokacin ina 4/5yrs haka zuwa 6,
12:12

muka dawo gida ahaka suka hadu da Babana sabida ni sukai aure yadawo da ita Abuja kan yasami wani aiki achan yana gadin UBA bank dake central area shima zaku iya zuwa ku bincika"
12:12
Chapter 132 · 0% Book details