← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 145

Sashe 2

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Batare daya janye idanunshi dagakan abinda yakeyi ba cikin wata kalan murya dake nan adikile irin muryan nan na no nonsense person ba wasa kokuma fara’a yace “how is my shipment Nas?” Firgigit saurayin daya kira da Nas ya farga daga duniyan tunani dakuma kallon Maheer dayake yadan sosa kanshi yace “I spoke to the captain gobe around 1500hrs zasu iso port na lagos so anything jibi shipment dinmu zai iso nan I assure you Escobar!” Sai a sannan yadago kanshi ahankali yadaurasu akan Nas tareda folding hannunshi a kirji kaman mai nazarin wani abu, murmushi Nas yayi yajaye idanunshi da dan sauri daga kallon da Maheer kemai yakalli about 40grams na cocaine dake kan table din da akai packaging ga wata yar karaman farin roba da aka zuba cocain yar kadan aciki taster yakai hannunshi yadauki yar roban yana budewa yace “coke din nan fa Pablo? Na waye”? Danne hancinshi daya yayi yashaki cocaine din jikinshi nawani kalan tsuma yana kyarma yace “Ya Allah!” Ya maida roban yarufe ya ijiye yana dan mika yace “amman wannan coke din wacce ta iso jiya ne daga Mexico ko dan wlh tayi dadi, har cikin bargon kashina najita, Wallahi tasa kyankyasan kwakwalwata sun watse dukansu sun fara tafiya suna gudu kaman an watsa musu fiyafiya” yay maganan yana murmushi yana daukan roban yana kokarin kara bude roban ya shaki na biyu Maheer yamai wani mugun kallo dayasa ya rufe ya maida ya ijiye roban dasauri yace “you don’t get high on duty nasani Oga!” Cikin wani kalan karisma Maheer yace “good” sannan yacigaba da aikin dayake yi daidai nan wata waya kirar iphone 14 pro max amman customize na gold dake kan table na wajen tashiga ruri kallon screen din Maheer yayi saikuma yadauke kanshi yacigaba da aikin dayakeyi hakan yasa Nas da kanshi yadan fara juyawa sabida yar kankanuwan coke din daya shaka yakalli screen din dan murmushi yayi yakalli Maheer yace “wai yaushe Boss zata dawo ne”? Batare da Maheer yakalleshi ba yace “bakada number ta ne”? Dasauri Nas yace “amman ai the whole empire ansan kaine favorite nata dan haka nasan tafada maka” batare daya kalleshi ba yace “tashi kabarmin office dina” dasauri Nas yace “Boss is obsess with you wlh, you yelled at her, imagine you even Bosses her around Pablo kaman kaine Mai empire dudda dai nasan you guys are partners in business yanzu but ai ita takawoka kaman yanda takawomu muma what’s so special about you dakai kadai takeji take kuma gani dudda akwai maza dai dai sama da maza dari biyu dake mata aiki banda external ones dake kawo Mata hari”? Yay maganan yana kallon Maheer dayay kaman baimasan wani na magana awajen ba, jaye idanunshi yayi yana kara kallon wayan da kusan this is the fifth call yake shigowa wayan kenan daga same number dayay saving da Hajiya, knocking kofan akayi hakan yasa Maheer yadago kanshi batare dayay magana ba yadanna wani boturi akan kujeranshi hakan yasa aka bude kofan aka shigo Manager club din ne yashigo yana sanye da suit black looking smart, cike da girmamawa yakaraso cikin office din yagaida Maheer yace “Sir we need XTC (Ecstasy akafi kiranki, ko methylenedioxymethamphetamine MDMA) saikuma Liquid X (Gamma-hydroxybutyrate GHB)
duk angama da wayanda aka fito dasu yau, kusan guest namu na yau yafi na kowani Friday” dasauri Nas yace “ba last dose of Liquid X aka fito dashi yauba”? Ahankali Maheer yamike tareda jaye kujeran dayake zaune kai baya, bindigar dake kan kujeran kiran Glock 17 Gen 4 yadauka yasoke abayan wandonshi sannan yafara tafiya kaman wani sarki da isa da takama dasauri suka biyoshi abaya kaman fadawa bude office din yayi yafita yahau stairs duk suna biyedashi zuwa sama wanda nan ne supply room na komi yake a club din dakuma kitchen, kwali biyun XTC yabawa manager yace “lemme make the Liquid X come back in the next 30min” dasauri Manager yace “da kanka yallabai zaka hada mana yau”? Murmushi Nas yayi yace “chemist kake gani anan” murmushi Manager yayi yawuce yafita shikuma Maheer yay wani kitchen dakeda fadi sosai kana ganin kitchen din kasan kwayoyi kawai ake hadawa awajen wani black apron yadauka yadaura asaman kayan dake jikinshi yadauki tukunya yana tara ruwa hakan yasa Nas yasami waje yazauna kan kujera yanabin Maheer din da kallo danshi ko zaa kasheshi dudda shima ya dade a harkan amman bai iya hada daidai da burkutu nan nan ba, Maheer, Maheer sheggen yaro kake gani awajen nan saisa baya ganin laifin Boss data gama mutuwa akanshi dudda suna boyewa but yasan akwai something that is definitely going on tsakaninsu zai iya rantsewa cin juna suke dan Boss tai Kane kane akanshi saisa har yau baitaba ganin Maheer da wata budurwa aduniyan nan ba dudda kusan 30yrs kenan dayasan Maheer, bayama mata magana apart from Boss, ga yaron shegen kwaro ne duk randa Maheer yabar business din nan to empire din nan ta tashi aiki wlh dan kasuwan mutuwa zatayi mut ko abinda yasa Boss keji dashi kenan oho dan Maheer shine business din nan business din nan shine Maheer, ba abanza akamai lakabi da PABLO ESCOBAR ba the biggest drug lord in history, zai iya fadin this aduk inda yashiga ayanzu dai the biggest Drug lord in the whole Africa as a continent is Maheer Escobar na Africa!!!

Yana cikin tunanin wayanshi yay kara hakan yasa da sauri yakai hannunshi gaban aljihun riganshi yazaro wayan ganin Boss yasa dasauri yakalli Maheer da hankalinshi kekan abinda yake dafawa a kitchen sannan yakai wayan kunne cikeda girmamawa yace “ranki shi dade Boss, Hajiyar mu Maman mu kuma gatanmu” dan shiru yayi yana sauraron maganan da akeyi daga ta dayan bangaren sai chan yadago kai yace “eh gani nan tareda shi yana dama Liquid X ne a kitchen” yay shiru yana sauraron maganan da ake saikuma yatashi yataho cikin kitchen din bama Maheer wayan yayi yace “gashi za’ayi magana dakai” kallon wayan Maheer yayi awulakance kaman baiso yay magana, kaman wanda magana kemai wahala yace “waye”? Wani kalan murmushin kunma rainamin wayau Nas yayi yace “Boss ce Oga takira, Hajiya ce” cikeda halin wulakancin nan nashi yadauke kai yacigaba da juya substance din dake wuta, baki Nas yasaki yana kallon Maheer, almost 1min yabata tsabagen wulakanci sannan yace “tell her am busy” maida wayan kunne Nas yayi yace “Boss kinji shi ko” dan shiru yayi saikuma yace “okay” zaro wayan yayi daga kunnenshi yadanna speaker sannan yace “Boss wayan na speaker” wata muryan yar matace da bazata wuce 45-46yrs ba dan tadan manyanta dagajin muryan authoritatively tace “Naseer ijiye wayan kawuce kafita inaso nai magana dashi” dasauri Nas yadan juya idanu yace “okay Boss” Nas yafada da girmamawa sannan ya ijiye wayan kan table dake wajen yajuya yafita daga kitchen din yarufo kofa.
Chapter 2 · 0% Book details