Sashe 92
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 7 min read
rakiya har bakin mota yana kallon Ahmad yace "Xan shigo da safe in sha Allah" Ahmad ya hararesa yace "Kar ma ka shigo mana" a haka suka wuce a mota, Abuturrab ya juya ya koma cikin gidan, dubu sha biyar ne kudin da ya kirga, bayan kusan minti ashirin ya mike ya wuce sama ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta kan darduma, ya nufi gaban mirror dinta ya ajiye kudin yana kallonta ta madubin yace "Gashi nan sun baki, dubu sha biyar, amma ban mance turarena da kika fasa ranan ba" juyawa yyi yana kallonta da kyau yace "Kinsan nawa turaren da kika fasa?" Kallonsa kawai take, yace "Dubu arbain da bakwai kika fasa ranan, don haka xaki ajiye wannan dubu sha biyar din har ki samo dubu 32 ki cika min kudin turarena" Yana fadin haka ya bar kudin gaban madubi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can tace "Toh ka tafi da kudin" Ya juyo yace "Sai kin cika" daga haka ya fita dakin. Karfe tara jiddah na wanke wanke a kitchen ya shigo, bin kitchen din ya shiga yi da kallo, ita dai tunda ta kallesa sau daya ta ci gaba da wanke wankenta, kettle din dafa ruwa ya dauko ya bude fridge ya fiddo goran ruwa daya ya xuba a kettle din sannan ya jona, satan kallonta yayi ganin hankalinta na kan wanke wanken da take, ya kai hannu a hankali ya bude murfin tukunyar shinkafar dake kan gas har lkcn, dai dai nan ta juya yayi saurin sakin murfin tukunyar, dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya sosa kansa, sai kuma ya hade rai yace "Shi kuma sauran shinkafar wa kika bar ma??" Ta kallesa tace "Kai mana" ya kauda kai bayan few seconds yace "Na fara wasa da ke ko??" Bata ce komai ba ta dauraye hannunta bayan ta gama wanke wanken ta dau plate ta nufi gun tukunyar ta debi shinkafar duk da ta ci, ta ajiye pot din gun wanke wanke, ta bude miyar ta sa d'an dai dai da nama yanka uku sannan ta rufe sauran miyan ta dau wani plate me xurfi ta rufe shinkafar da shi ta dau spoon ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, shafa kansa yyi yana tunanin wani eatry xai kira yyi ordering abinci da daddaren nan a kawo masa, shayi ya hada bayan ruwan ya tafasa sannan ya fita kitchen din, yana haurawa sama ya kalli kofar dakinta sannan ya wuce bangarensa, bude kofar parlon yayi ya shiga sannan ya kulle, still yyi yana kallon plate din dake ajiye kan center table, ya karasa ya ajiye shayin hannunsa sannan ya bude plate din yana kallon abincin, ajiye murfin yyi ya mike, can ya kalli kofa, sai kuma ya xauna, kamar me contemplating sai kuma ya dau spoon din ya fara cin abincin. Washegari karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad, Umma bata amsa gaisuwar da yake mata ba, ya shafa kansa ya wuce dakin Ahmad, Ahmad na ganinsa ya mike yace "Let's talk" Kama hannunsa yyi ya fita suka tafi bangaren Abbansa, Abuturrab dai kallonsa kawai yake, Ahmad ya kulle kofar parlon yace "Me yasa ka dauke jiddah daga gidan su Ummi jiya?" Abuturrab ya hade rai yace "Gani nayi she isn't comfortable, sannan Aunty duk ta bi ta takurata duk ba wanda yace komai, shkkn saboda ba matata bace ita sai in xuba ido a cuceta?" Ahmad yace "Har Ummi ma cutarta take kenan?" Abuturrab ya shafa kansa ya xauna yace "Ni bance haka ba, wllh da kaga yanda na ganta shekaranjiya ko kai baxa ka bada shawaran in bar ta ba, ita Ummi bak'i sun mata yawa, babu abinda xata yi noticing, and Aunty sai aikenta take tana fita titi, what for?? I hate it when someone is being maltreated kai ma ka sani" Ahmad yace "Hmm, ka gano wani abu kuwa Abuturrab?" Abuturrab na kallonsa yace "Me kenan?" Ahmad yace "You are starting to develop feelings for Jiddah, na lura da hakan tun ba yanxu ba, wannan ya wuce tausayi da kwatar mata 'yan ci, gashi kayi gaggawar rabuwa da ita, don babu aure tsakaninka da ita believe it or not, ko da kuwa baka saketa ba shelan da ka dinga yi kana sanar ma kowa cewar ka saketa, ta saku babu wani kwaskwarima... Babu wani aure tsakaninku ynxu Captain, sannan kar ka manta babu idda a kanta..." Katse sa Abuturrab yyi yace "Nigerians have a very very poor thinking mentality, me yasa baxa ku yi koyi da wasu kasashen da suka fi ku wayewa ba, Shikenan ba dama mutum ya nuna rashin jin dadin abun da ake yi ma mace sai ace yana sonta? Ohk fine... Yanxu in xuba ido ayi ta cutarta kenan tunda ba sonta nake ba, ina ce ita ma mutum ce kamar kai, kamar ni, kamar kowa ma? To don me baxan kwatar mata right dinta ba, ko ka mance akan kwato mata right din nata yasa har naje na aureta? Sannan still a kan kwatar mata right din nata ne yasa na datse auren dake tsakaninmu, and duk wannan wa'axin da kake min ni na ta6a bude baki nace maka da aure tsakaninmu ne?? Ko kuma idan ma da auren gaya maka aka ce xanyi" Ahmad yyi murmushi yace "You are just confusing and disorganizing ur self, shi lamarin da ya shafi addini babu wayo a ciki dai, anyway Ummi is jet angry at you, gwara ko koma yanxu ka dau jiddah ka kai ta can gidan tunda dinner xa ayi yau, daga wajen dinner din sai ka wuce da ita gida, gobe Saturday ka kawota yini tunda baxa ka iya barinta a gidan ba, amma kasan me? Kawai ina ji a jikina xamanku tare da ita ya kusa xuwa karshe" Da ido Abuturrab ya bi Ahmad har ya fita. Motoci biyu ne lafiyayyu suka yi parking kofar gida, El-Basheer ya juya yana kallon warce ke xaune bayan mota ta sha glass yace "Toh ai sai ki sauka mun iso" Da mamaki tace "In sauka fa kace, a kan titin xan sauka d'an nan, motoci sun daina shiga get din gidan ne xan sauka a bakin titi" Yace "Toh ai babu wajen parking a ciki, ke baki ga mutane bane...." Tace "Toh ina ruwana da mutane, har yanxu dama Najeriyan bata canxa ba, mu ba haka ake yi a Masar ba wllh, idan ana biki ko wani shagali wllh dai daikun mutane ake gayyata da daddare, sai a tarfa ma kowa yar gurasar alkama a gefen faranti, a daura kofin madara a gefe, idan da yar cinyar kaza a saka a gefe shi ma, Allah ba a taro irin haka kamar ana yunwa, shi Kabirun yasan haka mutane xa su cika gidan xai bada mota a kawoni nan salon in gantale? wllh mu bamu saba haka a Masar ba, a gaskiya idan baxai yiwu ba a juyar dani kawai a mayar dani Bauchi, daga baya kada Usman ya kullaceni sai in dawo inyi Allah ya sanya alkhairi, amma wllh baxan sauka bakin titi ba duk k'ura ta kare min abinda babu a Masar, ko shi Usman din bai san ina hanya ba ai Aliyu ya sani tunda na sanar masa ta waya.... Aa gaskiya ba dole Allah ya sanya alkhairi juya mu koma kawai... Mu ba haka ake a Masar ba, komai bisa tsari ake yin sa" Kashe motar El-Basheer yyi yace "Kinga Hajja idan xaki sauka ki sauka ni xan tafi gun daurin aure ne, ga ki ga gate kice baxa ki sauka ba" Bude baki tayi tana kallonsa, can tace "Aa toh gaskiya Najeriya ba wajen xuwa bane, tunda nake a masar ba a ta6a min rashin da'a irin wannan ba, sun san girma da mutuncin tsoho..." Tana kai wa nan ta ciro wayarta fuska tsuke ta mika masa tace "Kira min Kabirun, ai shi na haifa ba kai ba" Bude motar El-Basheer yyi ya sauka yayi wucewarsa cikin gidan, ta bi sa da kallo baki bude, sai kuma ta sauko ita ma ta bi bayansa. Jiddah ce xaune bedroom din Umma kanta a kasa tana wasa da gefen hijab dinta, Umma tace "Jiddahh" dago kai tayi a hankali tana kallon Umma, Umma tace "Ina sauraronki, idan kika min karya kuma kar ki manta Allah na kallonki, kuma nasan kinsan makomar makaryaci" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Umma tace "Ina jin ki"