Sashe 20
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 1 min read
shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace "Kina ina yanxu?" Ta bi inda take da kallo tace "Mai adaidaitan yace min kano road ne" Abuturrab yace "Ba sa wayar" Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace "Ehh a dai dai wajen muke ma" bayan few seconds mai adaidaitan yace "Toh shkkn xan jira in sha Allah" Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace "Abba xan d'an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it's urgent" Abba yace "Alright sai ka dawo" Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din.....