Sashe 26
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk ya rufesu yace "Ki dauka ki kai maku can ki ci" Da sauri ta kallesa tace "Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne" Ganin babu spoon a wajen tace "Bari in kawo maka cokali" Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din, sai kuma tace "In xuba maka?" Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika masa, calmly yace "Kwashe su nace baxan ci ba" Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace "Kee, ina xaki?" Ta juyo tace "Xan xauna a waje ne" Authoritatively yace "Dawo nan ki xauna" a hankali ta dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka ce "Captain da kansa barka da wuni..." Abuturrab yace "Ya kake Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Alhmdlh Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka jin dadi" Abuturrab yace "Ehh ina kaduna" Mu'axxam yace "Toh ya jikin Captain!" Abuturrab yace "Alhmdlh" Mu'axxam yace "To maa sha Allah ranka shi dade" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motarsa a hankali yace "Kana ji na Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Ina jin ka Oga" Abuturrab yace "Kana da mata ne?" Mu'axxam yayi dariya yace "Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba" Abuturrab ya gyara xamansa yace "Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?" Mu'axxam yace "Ikon Allah, Oga ai baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh" Abuturrab yace "To kar ka damu, in sha Allah xan maka duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae" Mu'axxam yace "Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye min kudi wllh...." Abuturrab yace "Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko Juma'ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi magana" Mu'axxam yace "In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga" Abuturrab yace "Maa sha Allah, xa mu yi magana" Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke... this is now almost settled saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace "Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun 'yan sandan nan maganar nan babba xata xama, Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar sannan na kawo ka wajen kawun nawa" Abuturrab yace "Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa aje police station din yanxu ba wani abu ba..." Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace "Ni da xa aji ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa shi sai mu koma gun 'yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d'an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban hukuma koko ya ku ka ga?" Hansai tace "Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna" Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace "Ko ya kace Alhaji??" D'an murmushi yayi yace "Ehh hakan yayi, aje wajen nasa" Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace "Ba sai mun sha wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu" Abuturrab bai ce komai ba ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace "Ita Jiddah ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai a gama da tantirin nan" Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace "Kinsan inda take kenan?" Da sauri Hansai tace "Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam" Abuturrab bai kuma cewa komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace "Toh gashi dai mun xo gareka mai unguwa...." Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa harara, ta marairaice tace "Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu da wani tsaro xaman mu a hayi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne Hansai?" Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace "Ikon Allah Iliya dai guda, d'an gidan Malam Kabiru?" Hansai na shessheka tace "Shi wllh" Yace "Toh yanxu ke kin tabbata yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu..." Hansai tayi saurin cewa "Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun" Mai Anguwa ya girgixa kai yace "Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan" Hansai ta xaro ido a mugun tsorace, Mai anguwan yace "Amma ke kika haifi yarinyar?" Hansai tace "Ehh 'ya ta ce" Yace "Yanxu ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba" Hansai ta fara matsar kwalla tace "Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire ran shiryuwar d'an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi, ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh" Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta, Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace "Amma tunda abu ya xo da haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don a gaskiya muna cikin hatsari" Ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta...." Hansai ta fashe da kuka tace "Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha'awar yi mata aure bayan abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na mata aure banda ta lalace" Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da yayi fice a gari, Abuturrab ya d'an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a ransa. Sai da suka yi la'asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen, Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace "Ku yi