← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 205

Sashe 73

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 6 min read

yi baccin ba, hotel din da ya ke sauka ya tafi yayi lodging yayi ordering abinci, bin sa kawai take yana tafiya har suka isa dakin da aka basa, tana shiga dakin ta jingina da bango ya kulle kofar ta dinga bin dakin da kallo, ya ajiye makullin motarsa da wayoyinsa gefen gado ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, ita dai tana ta tsaye, ya shimfida darduma yayi sllhn isha, bayan ya idar da sllh aka yi knocking kofar, mikewa yayi ya isa kofar ya bude, ya amshi abincin da aka kawo sannan ya kulle kofar, shayi ya sha, sai pepper soup din hanta bai bude takeaway din shinkafar ba ya mike ya dau wayarsa yayi dialing number Aneesah don tun yana hanya take ta kiransa, fita yyi dakin ya kulle daga waje, Jiddah ta bi sa da kallo, xaunawa kasa tayi hawaye na taruwa idonta bayan kusan minti sha biyar ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito tayi magrib da isha, kwanciya tayi kan darduman nan da nan bacci ya dauketa. Karfe sha biyu da mintuna Abuturrab ya shigo dakin abincin ya fara dubawa ko ta ci ya ga bata ci ba, ya xauna gefen gado ya sa hannu ya buga gefen kafarta bude ido tayi ganinsa ta mike xaune da sauri, babu yabo bbu fallasa yace "Dauki abincin ki ci" Tace "Ni na koshi" wani kallo ya mata, ta jawo abincin ta bude ta fara turawa, bai takurata sai ta ci da yawa ba, bayan ta rufe sauran yace "Tafi ki wanke bakin ki kiyi wanka" Bata iya ta ce masa komai ba amma ji tayi kamar ta fashe da kuka, ta mike ta cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta bude jakarta ta ciro sabulu da sponge, toothpaste da toothbrush, xata wuce bandakin yace "Tawul din fa?" Dawowa tayi a hankali ta kara bude jakar ta dau towel dinta ta wuce bandakin, ta kusa minti biyar tsaye bayan ta gama wankan ta rasa yanda xata fito daure da towel, gashi bata shigo da hijab ba, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofar a hankali tana lekan dakin, bata gansa a dakin ba, ta fito da sauri, ta fiddo kayan da xata sa da turarruka da mai, tana rufe jakar ya shigo dakin, kasa dago kanta tayi ya rufe kofar, bata yarda ta kallesa ba ta mike ta dau kayan nata ta shiga bandaki, sai da ta gama sakawa sannan ta fito ta mayar da turare da cream din cikin jaka ta tafi kan darduma ta xauna, yana xaune can gefen gado ya kalleta yace "Tashi ki kwanta" sunkuyar da kanta tayi, sai kuma ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta, ba a dau lkci ba kuma bacci ya dauketa, karfe daya nayi ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya dau pillow ya ajiye a kasa ya kwanta. Da asuba ana idar da sllh Abuturrab yyi wanka ya shirya, tun ana sllh Jiddah ta tashi amma bata juya ba balle ya san idonta biyu, tana jinsa yana shiryawa har ya gama, kallonta yayi ya buga gadon yace "Ke baki sallan asuba ne dama?" Mikewa xaune tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta wuce bandaki, kwance ta gansa da ta fito idonsa a lumshe ta tada sllh bayan ta idar ta kwanta kan darduma, karfe bakwai da few minutes Abuturrab ya tashi, tashinta yyi ta mike xaune da sauri, yace "Anjima idan anyi knocking ki bude kofa ki karbi abinda aka kawo, apart from that ban ce ko bakin kofar ki je ba, kin ji me nace maki??" A hankali tace "Toh" Sai da ya fara kunna TV dake dakin ya kai tashar hausa sannan ya dau jakarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har xai fita ya juyo, da sauri ta dauke idonta daga kallonsa, yace "Saura ki bude kofar a haka baki sa hijab ba idan aka kwankwasa" bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, mikewa tayi ta hau saman gado ta ci gaba da baccinta. Karfe takwas taji an kwankwasa kofa, mikewa tayi har ta nufi kofar haka ta dawo da sauri ta dau hijab da ta daura kan riga da wandon jikinta na bacci, sannan ta nufi kofar ta bude, abinci aka kawo mata ta amsa tare da godiya ta juya ta koma cikin dakin, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta yi breakfast din da aka kawo mata. Throughout ranan haka ta yini ita kadai dakin sai dai tayi kallo idan ta gaji tayi bacci, tana farkawa ta ci gaba da kallon, abincin lunch da aka kawo mata ma sai kusan la'asar ta ci, karfe biyar da rabi tana tsaye bakin window taji an bude kofar, da sauri ta juyo, shigowa dakin yyi, ya ajiye ledan hannunsa,duk da wayar da ta gani kare a kunnensa hakan bai hanata ce masa Ina yini ba, ya xauna gefen gado ya ci gaba da wayarsa, bayan ya gama ya tashi ya fita ta bi sa da kallo, sannan ta kalli ledan da ya ajiye. Sai bayan magrib ya shigo tana xaune saman darduma ta bi sa da kallo har ya xauna ya bude ledan da ya shigo da shi ya fara cin naman tsiren dake ciki, dauke idonta tayi bayan few minutes tace "Kace min gidanmu xaka kai ni, baka kaini ba shine xaka kawo ni nan, ni wllh ka maidani wajen Babarmu" Bai tanka ta ba, hakan bai hanata maimaita abinda ta fada ba, ya juya ya kalleta yace "In maida ke wajen Baabarku?" Tayi shiru bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma gefen gadon ya xauna yana facing dinta yace "Tambayarki nake?" Ta sunkuyar da kanta tace "Ehh kai kaini wajenta" Yace "Ohkk... amma bari in tambaye ki" Ta dago idanuwanta ta kallesa yace "Kina tunanin xamana da ke ba burden da damuwa bane a gareni?? Ina nufin baki san cewar rayuwar ki tare da ni nauyi babba na daura ma kai na ba da rashin kwanciyar hankali? Do you think ko matata ba iyakar abinda xan mata nake maki ba? What's so important about staying under same roof with you? Kina tunanin ni ajin ki ne da nake kula ki nake kula al'amuranki? Toh bari ki ji, ni din nan da kike gani ba ajin ki bane, ina taimakon ki ne saboda Allah ba don komai ba, gidan naku da kike cewa in mayar da ke an gaya maki baxan iya daukan ki in maida ke ba duk abinda xai faru dake ya faru? Toh bari ki ji, sau da yawa tausayi kan canxa mutum, banda haka bani da abinda xan yi dake a waje daya, and i mean it, ni ba ajinki bane" Yana fadin haka ya mike ya fice daga dakin, ta bi sa da ido kafin ta sunkuyar da kanta.
Chapter 73 · 0% Book details