← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 205

Sashe 38

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Abuturrab ya koma gida bai bari stepmom dinsa ta san ya dawo ba don bai ma dawo da motarsa ba a gidansu Ahmad ya barsa, Ahmad yayi dropping dinsa kofar gida a nasa motar ya koma, yana shiga bedroom dinsa ya sa makulli hade da sauke ajiyar xuciya, wanka yayi ya sauya xuwa pajamas dinsa ya xauna gefen gado, yana son shan shayi but baya son fita duk da ko ya fita din kanninsa xai saka still, wayarsa ya jawo ya shiga dialing number din Ramlah, tana dagawa yace "Make me a cup of tea, an omelette with just two eggs" Bai jira cewarta ba ya katse wayan, ba a dau lkci ba Ramlah tayi knocking bakin kofar dakinsa, ya mike ya isa kofan ya bude ya bata hanya ta shigo, ajiye plate din hannunta na kwai dake rufe tayi da cup din shayin tana kallonsa tace "Yaya...." yace "Goodnight Ramlah" Shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofa kafin ta fita yace "Thank you" Ta sake juyowa ta kallesa ta marairaice tace "Amma yaya me yasa....." Hade rai yayi yace "Fita!!" Fita tayi ta kulle masa kofar ya karasa ya sa key. Washegari Friday Abuturrab na dawowa masallaci da asuba ya shiga bangaren Umminsa, da da ne bangaren stepmom dinsa xai fara shiga, kansa a kasa ya gaida Ummi ta amsa, a hankali ya soma bata hakuri, tace "It's okay, ae kun gama magana da Hajiya Ramlah ko?" Ya gyada mata kai tace "Toh maa sha Allah" Yace "Amma Ummi don Allah kiyi ma Abba magana naji yana cewa baxan saketa ba..." Ummi tace "I don't know... But seriously he is not to decide that for you, you just ignore him" Abuturrab bai ce komai ba, can yace "Toh shkkn Ummi" mikewa yayi ya fita dakin ya koma nasa, a masallaci ma dodging din mahaifin nasa ya dinga yi har ya shigo gida basu hadu ba. As early as 10 Abuturrab ya bar gidan ya tafi gidansu Ahmad, bayan ya gaisa da Umma dake parlor ya tafi dakin Ahmad, Ahmad na shiryawa ya samesa, Ahmad na murmushi yace "Welcome latest ango" Abuturrab yayi still ya dinga masa wani kallo, Dariya Ahmad yayi yace "Yanxu dai cikin ruwan sanyin kullum sai ka xo gidan nan ko?" Abuturrab bai tanka sa ba ya tafi ya xauna, Ahmad ya gama shiryawa yace "She's getting better, jikin da sauki yau sosai" Nan ma Abuturrab ya sharesa, bai san shi abinda ya kawosa daban ba, Mikewa kawai yayi ya fita daki hoping Umma ta bar parlon yanxu, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, luckily ya tadda babu kowa a parlor ya karasa dakin da Jiddah take ya bude hade da sallama murya can ciki, tana xaune saman gado da wani drip din a hannunta ga pepper soup da Umma ta sa ayi mata, Huraira da Maman Abdallah ne dakin suna ta hira, ita dai sai dai tayi murmushi, ganin Abuturrab duk suka gaishesa, bai san suna ciki ba da baxai fara shigowa directly ba, ya amsa without looking at them, Jiddah ta kallesa tace "Ina yini?" Ita ma bai kalleta ba yace "Lafiya" Ahmad ne ya karaso dakin ya shiga ciki yana kallon jiddah yace "Alhmdlh jiki yayi kyau sosai ko Ummi?" Ta d'an yi murmushi amma bata ce komai ba, shi dai Abuturrab na tsaye, Ahmad ya kalli su Huraira da basu da niyyar fita a tunaninsu kawai dubata suka shigowa yi, yana murmushi yace "Maman Abdallah da Aunty Huraira a bamu waje mu duba patient pls" Duk suka mike, Huraira tace "Toh bari mu fita" Bayan sun fita dakin Abuturrab ya karasa gun window ya tsaya Ahmad dai sai kallonsa yake, Can yayi murmushi ya kalli Jiddah yace "Kin sha maganin ai ko?" Ta gyada masa kai tace "Eh" yace "Toh Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen" Ya juya yace "Bari in kawo maki na karshen.." Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita ya kulle kofar, sunkuyar da kanta tayi, Abuturrab ya d'an kalleta, he don't even know where to start from, hada ido suka yi ya rungume hannunsa yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki" Ya d'an yi jim kafin yace "Iyayenki sun daura maki aure..." Da sauri Jiddah ta daga kai ta kallesa, yaki yarda su hada ido ya ci gaba yace "Amma ba da mutumin nan ba" Kallonsa kawai Jiddah take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Amma shi wanda aka daura maki auren da shi xai sake ki, sai ki ci gaba da xama a nan wajen Umma ko gidanmu wajen Ummina, amma fa sai kin amince babu ke babu Baabar nan taku don ba sonki take ba, kuma baxata ta6a sonki ba, neman kudi take da ke" Cikin sanyin murya Jiddah tace "Toh da wa aka daura min auren??" Yace "Fada maki ba amfani xai yi gareki ba, kawai dai abinda na sani xai sake ki, sai kiyi xaman ki a nan ko kuma ki xauna gidanmu, ki fara karatu islamiyya da boko, kinsan wacece ke, kinsan daga inda kike, kawai na shiga rayuwarki ne ba don komai ba sai don in taimakeki in samar maki yan cin ki, idan ba don haka ba, ni bana shiga abinda bai shafeni ba...." Kallonsa kawai Jiddah dai take a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, a hankali tace "Jiya Umma da daddare ta shigo ta tambayeni in gaya mata gaskiyan wacece ni, kuma ya aka yi na xo gidan nan" Cikin rawar murya ta ci gaba tace "Ni kuma baxan iya mata karya ba" Abuturrab na kallonta yace "Kin dai gaya mata ko?" Ta gyada masa kai yace "Good, xuwa gobe duk inda kika ce xa ki xauna nan xa a kai ki, ko gidanmu ko nan" A hankali tace "Toh idan na xauna nan xaka dinga xuwa?" Kallonta yake da kyau, ya hade girar sama da ta kasa yace "In xo in yi maki me??" Kasa cewa komai tayi tana wasa da fingers dinta, yace "Ae ba lallai ki gan ni ba, ki ma daina min kallon sani daga yanxu, ki kama Umma da su Siyama ki rike sosai, they will like you, ni ba lallai a shekara ma kike ganina ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye cike idonta, yace "Sai ki tsaya kiyi karatu da kyau domin al'umma da wa enda suke tare dake suyi alfahari dake..." Nan ma ta gyada masa kai kawai, yace "Allah ya kara lafiya" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya dinga sauka idonta, Abuturrab ya amshi medical report dinsa wajen Ahmad kawai ya bar gidan coz baya tunanin har ya koma aiki da akwai abinda xai sake dawo da shi gidan, he now felt relieved, yaji baya tare da duk wani damuwa. Da yammacin ranan Abuturrab dake bedroom dinsa ya dau wayarsa dake ring, ganin number Abbansa yaji gabansa ya fadi sosai, dagawa yayi ya kai kunne hade da sallama, Daga daya bangaren Abba yace "Ka sameni parlona ynxu" Kafin yace komai Abba ya katse kiran, lumshe ido yayi ya bude, bayan few minutes ya mike a hankali still holding to his phone ya nufi kofa ya fita, a main parlor suka ci karo da Aunty, yayi kasa da kai yace "Ina yini Aunty" Ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa shi tayi wucewarta, ya bi ta da kallon gefen ido sannan ya ci gaba da tafiya xuwa parlon Abbansa cikin sanyin jiki, a hankali yayi sallama sannan ya shiga, sosai gabansa ya fadi ganin Abbansa da brothers dinsa biyu, a sanyaye ya karasa shiga cikin parlon ya xauna kasa sannan ya gaishesu, uncles din nasa suka amsa, ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Alhaji Lawal yayan Abbansa ne yace "Mun ji abinda ke faruwa Aliyu, ko kuma ince mun ji abinda ya faru" kasa cewa komai Abuturrab yayi, Alhaji Ibrahim kanin Abbansa yace "What u did is something very good but ba ta yanda ya kamata kayi ba kayi, kada ka manta ba kai ka haifi kanka ba, kana da iyaye, no matter what ya kamata ka nemi consent dinsu, ya kamata ka basu girmansu su san abinda kake ciki, ba sae da abu ya kwabe ba....." Daga kafada yayi yace "Anyway, wannan duk maida hannun agogo baya ne, tunda abinda ya faru ya riga da ya faru, sae dai a tari na gaba" Abuturrab bai iya yace masu komai ba, Alhaji Lawal yace "So what next now? Yarinyar tana ina?" A hankali yace "Tana gidan Umma" Alhaji Lawal yace "Wacece Umma?" Abba yace "Kanwar Hajiya Hauwa" Alhaji Lawal yace "Ohkk, am asking what ur next action is now" Abuturrab ya sunkuyar da kai yace "Abba sakinta xanyi sai ta yi xamanta tayi karatu that was my intention dama" Alhaji Lawal yace "Ka saketa a saboda me?" Abuturrab ya kallesa ya marairaice yace "Abba dama wllh niyyata kenan, ai baxai yiwu inyi aure iyayena basu sani ba, ni kawai na amince na aureta ne sbda kubutar da ita daga hannun matar babanta, amma ai ni baxan iya aurenta ba" Alhaji Lawal yace "Wannan ba magana bane Aliyu, ka aureta, ka aureta kenan, babu wani kwaskwarima, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya, kada ka sake tunanin sakinta, kaddararku da ita ne a haka" Bude baki Abuturrab yayi yana kallonsa without knowing cewar yayi hakan, Alhaji Ibrahim ya gyada kai yace "Hakuri xaka yi son, ka xauna tare da ita, ka cike ladanka, ai Allah ya ga xuciyarka, idan ka saketa baka kyauta mata ba, akwai hikima cikin auren nan...." Abuturrab ji yayi kamar ya fara masu kuka gaba daya, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Dama ni nace baxai saketa ba, cikin weekend din nan ya dauketa su tare, ai ba wani ya jawosa ya aura masa ita ba, sai yayi hakuri ya rungumi kaddara" Abuturrab was lost of words amma ganin musa masu baxai yi masa amfani ba yayi shiru duk yana sauraronsu, sai dai xufa kawai yake yi, to lkcn da ma xai saketa din sani xa su yi? Tunanin hakan ya saukar masa da relieve, Muryar Alhaji Lawal yaji yana cewa "Gobe asabar ka tare kawai
Chapter 38 · 0% Book details