← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 205

Sashe 182

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 7 min read

yace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" El-Basheer yace "Ameen" Ahmad yayi masa sai anjima sannan ya katse wayar... Abuturrab na xaune main parlor din gidansa tare da Ahmad, Ahmad yace "Magana xaka min ba shiru ba Captain" Abuturrab yace "Ni ban gane tambayar nan taka ba" Ahmad yace "Ohk haka kace?" Abuturrab ya gyara xama yace "But me yasa wnn thinking din ma ya xo maka at the first place Ahmad, u can see i am happily married with my wife, menene xai sa kayi tunanin i have anything to do with that girl? Da ina da ra'ayinta ai kome xai faru ni baxan amince in saketa ba lkcn da su Abba suka min umarnin yin hakan" Ahmad yace "Is that so?" Abuturrab yace "Yes" Ahmad yace "Ohk then, i was mistaken kenan, cause ni a nawa tunanin if u have nothing to do with something baxa ka dinga bibiyan abun blindly ba..." Abuturrab ya dakatar da shi yace "They are some kind of talks dake 6ata min rai.. what are u insinuating now?" Ahmad yace "Nothing!!" Abuturrab ya ja tsaki yace "Da ina da intention din xama da ita babu wanda ya isa ya sa in saketa.... Balle ma duk su gama haukansu" Ahmad yace "I am glad i cleared this now" Mikewa yyi yace "Sae mun yi magana" daga haka ya nufi kofa, Abuturrab ya jinginar da kansa jikin kujera ya bi sa da ido. Da daddare Jiddah ta fito wanka kenan tana shiryawa Maimoon ta shigo dakin rike da wayarta tana xaro ido ta mika ma Jiddah wayar murya can kasa tace "Ya Aliyu" Da mamaki Jiddah ke kallon wayar, can ta amsa ta kai kunne jin shiru tayi sallama murya can kasa, daga daya bangaren taji yace "Kina jina?" Tace "Eh" yace "Duk wanda xai ce ki kai sa can gidanku a hayi kice baki san hanyar gidan ba" Tayi shiru tana sauraronsa, calmly yace "Kin ji abinda nace maki" Tace "To saboda me?" A takaice yace "Saboda haka nace maki" kasa ce masa komai tayi, taji ya katse wayar, tana kallon Maimoon ta mika mata wayarta, Maimoon ta amsa tace "Me yace maki?" Girgixa kai tayi tace "Abu yayi misplacing a hospital yake tambayata ko na gani" Maimoon dau ta juya ta fita bayan ta ta6e baki. Xaunawa Jiddah tayi gefen gado ta kasa ci gaba da abinda take tana tunanin to wa xai tambayeta gidansu a hayi. Washegari Asabar tun safe Abba ke kiran Abuturrab wayarsa a kashe, Hajja sai cewa take "Yau naga bala'i.. to wai baku san gidansa bane Usman, ko kuma mu tafi a dau yarinyar ai baxata rasa sanin hanyar gidansu ba tunda ba kwakwalwar kaza ce ita ba da xata mance gidansu, amma kun tsaya kuna ta kiran mutumi dake can yana bacci tare da matarsa, ranan ma fa da muka je gidan da Jiddah suna can suna ta bacci da rana tsaka har da garkame kofa" Abba yace "Toh sae a je da yarinyar ta nuna unguwar nasu" Aunty ce tsaye dakinta tana waya duk abun duniya ya isheta, Godiya tace "To ai duk laifinki ne Hafcy, da tun farko kin fito min da haka ai ni da tuni naje anyi abinda xa ayi an gama" Aunty tace "Ni kinga abinda yasa ban ce maki komai ba naga suna yawan waya har ma da chatting sai na fara tunanin ko abinda nake so ya kasance ne ke son kasancewa a raina, ashe ba haka bane" Godiya tace "Yanxu shi yariman da bakinsa yace yana son shegiyar yarinyar?" Aunty tace "Ji wata magana, da bai ce yana sonta ba neman auren me xa aje yi kuma, bbu wanda xai masa dole, da yardansa shi sa kika ga abun ke son yi nisa, wai yau fa xa aje can gidansu yarinyar" Godiya tace "Toh bari dai xan kira ki xuwa anjima" Daga haka ta katse wayar, Aunty ta xauna gefen gado tayi tagumi, Yarima da take ma Aisha sha'awa ne xa a nemi a makala ma wata can mara asali da dangi da kaf duniya bbu wanda take jin tsana irin ita, sake kiran Number mum din El-Basheer tayi amma har ya katse ba'a dauka ba, ta ja tsaki tace "Ko ina ta jefar da waya haka nake ta kira tun daxu" Kusan a guje Aneesah ta nufo Abuturrab ganin ya dau wayarta ta kwace tace "Wayana ne ai captain, naka na parlor" Ya dinga kallonta, sai kuma yace "Kira xan yi" tace "Naka fa?" Yace "A kashe yake" Tace "A kashe kuma, to me yasa baka sa a caji ba" Yace "I switched it off ba wai bani da caji ba" Tace "Toh bari in baka karamin wayana wnn ba credit" Bai ce mata komai ba ta karasa ta dau karamar wayar sai da tayi deleting duk out going da incoming sms snn ta kai masa wayar, amsa yayi ya fita parlor, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, downstairs Abuturrab ya sauka yayi dialing number El-Basheer dake kansa, yana fara ring ya daga, Abuturrab yace "How are you doing?" El-Basheer yace "Alhmdlh, ya aka yi wayarka a kashe?" Abuturrab yace "Na shiga bathroom da shi ya fada cikin ruwa" El-Basheer yace "Hard luck, grandma tace ana ta kiranka ka kashe waya" Abuturrab yace "Saboda me xan kashe waya" El-Basheer yace "Ai ban sani ba" Abuturrab ya shafa beard dinsa yace "Jiya na samu labarin matar da aka samar maka" El-Basheer yace "Ashe baka samu labarin da wuri ba kenan" Abuturrab yace "Amma nayi mamaki" El-Basheer yace "Mamakin me" Abuturrab yace "Warce Prince ke da niyyar aure" El-Basheer yyi murmushi yace "Sai dai kuma kasan ba prince din yayi ma kansa xabin ba" Abuturrab yace "A seventeen year old girl? Sai kace ka auri me kenan?" El-Basheer yace "Hajja xa mu yi ma wannan tambayar" Abuturrab yace "Kuma ka bani mamaki" El-Basheer yace "Na me fa?" Abuturrab yace "Ban yi tunanin xan rabu da abu ka dawo ka nuna kana son abun ba, in saki mata kace xaka aura" El-Basheer yace "Saboda hakan haramun ne?" Abuturrab yace "Whatever, amma it's more a less of abun kunya hakan da kayi, Allah ka bani mamaki" El-Basheer yace "From the beginning i was never serious with Hajja saboda ina ga kamar abinda baxai ta6a faruwa bane, amma wannan words din da ka fada min yanxu ya sa naji dole ma sai na auri Jiddah, kuma ka xuba ido ka gani... Till then" daga haka ya Katse wayar, Abuturrab ya dinga kallon screen din.... Ummi da wata frnd dinta tare da Aunty suka tafi can gidan Umma don nufin tafiya gidansu Jiddah tare da Jiddar, bayan Umma da Ummi sun kebe a daki Umma tace "Yanxu yaya menene amfanin wannan abun da Hajja ke shirin yi, duka duka shekarun yarinyar nan nawa, ko secondary din ma baxa a bari ta gama ba, yaushe ta samu yancin kanta har xa a fito da wani xancen aure a kanta? Don Allah ni dai a san yanda xa ayi a janye maganan nan wllh banyi farin ciki da shi ba, ina ita ina family dinsu El-Basheer? Yarinyar da har yanxu bata samu karatun kirki ba, takaicin da ta sha a gidan Aliyu ai kadan ne da wanda xata je gidan sarautan nan ta fuskanta... " Ummi tace "Kar ki yarda Hajja ta ji wannan abinda kike gaya min, nima na fara kawo mata hakan tace bakin ciki nake ma yarinyar saboda Bashir bai ce yana son Nafisah ba... Tun daga sannan na ja bakina nayi shiru, mu dai namu kawai fatan alkhairi" Umma tace "Aa wllh idan tsoron gaya mata gaskiya kuke sai ni in buda baki in gaya mata abinda ke raina, ya muna xaune lafiya xata dawo daga Masar duk ta bi ta daga mana hankali haka, ba fa Bashir din yace yana so da kansa ba, duk hade hadenta ne da rikicin tsufa irin nata, ni baxan amince da hakan ba gaskiya, yarinyar da nake so har university sai ta fara kafin aure... Sannan ni akwai d'an aminiyata ma a kasa" Ummi ta juya ta fita daga dakin kawai, Umma dai sai tafarfasa xuciyarta ke yi, Aunty kuwa na xaune parlor bakin ciki na ta cinta ita ma, Jiddah ta fito dag dakinsu ta durkusa ta gaida Ummi, sannan ta gaida frnd din Ummi da Aunty, Ummi tace "Xa ki gane anguwar ku Jiddah?" Jiddah tayi shiru tana kallonta, Can ta girgixa kai a hankali tace "Aa" Ummi tace "Baxa ki gane ba??" Jiddah ta gyada mata kai, Umma dake tsaye parlon taji dadi har ranta da Jiddah tace baxata gane gidansu ba...
Chapter 182 · 0% Book details