← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 205

Sashe 31

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma dole nan da lkci ba mai tsayi ba in auri Aneesah" Ahmad yace "Sai ka ajiye su gida daya kenan?" Abuturrab yace "Yes, kaga Aneesah ta samu me taimakonta aikace aikace kenan" Ahmad yace "Gaskiya ne wannan, to yanxu abinda nake son sani shine, idan ka rubuta takardan ba yarinyar xaka yi kenan ko ko ya xaka yi?" Abuturrab yace "I will do the rightful thing, giving her or not giving her" Ahmad yace "To su kuma can iyayen nata xaka bari su san tana wajenka?" Abuturrab yace "There is no need, idan ta samu 'yan cin kanta xata je garesu watarana" Ahmad ya sauke ajiyar xuciya. Karasawa Abuturrab yyi jikin window yana kallon waje, Ahmad dai sae kallonsa yake, shi har sannan ganin lamarin yake kamar a film, abinda ya fi daure masa kai yanda Abuturrab ya boye masa komai from beginning sae ynxu da abu ya baci, murmushi yyi yana gyada kai yana tunanin irin dariya da tsokanar da xae fara yi ma Abuturrab idan hankalinsa ya kwanta, sae dae deep down him he is so Happy for this young girl don yasan Abuturrab baxae ta6a cutarta ba, with him her future is super bright, komai na rayuwa baxai ji kyashin yi mata ba, maganar sakin da Abuturrab yyi ne kadai bai ji dadi ba har cikin ransa. Ana kiran magrib suka fita tare xuwa masallaci bayan sun yi alwala, Jiddah ce kadai xaune tsakar gida da buta a gabanta, tunda ta hangosu daga nisa tayi kasa da kanta tana alwalanta,, Kallonta kawai Ahmad ke yi yana mamakin yanda ita da gogan suka iya pretending, ko da wasa bata ta6a nuna masa ta san sa ba, murmushi kawai yake yi yana kara jinjina wannan lamari me abun mamaki, Abuturrab dai ko kallon inda take bai yi ba har ya fita gate din, Ahmad yyi murmushi ya bi bayansa, shi dai ya san ko giyar wake Abuturrab ya sha baxai yi accepting yarinyar nan matsayin matarsa ba, bayan an idar da sallah sun fito masallaci Ahmad na kallon Abuturrab yace "She isn't comfortable staying with the gate man and his wife, may be because daki daya ne, kaga baxai yiwu suna ciki tana ciki ba shi yasa take yawan xaman waje, na lura da hakan" Abuturrab bai ce masa komai ba har suka shiga compound din, sae a sannan yace "Idan na gaida Umma xaka saukeni gida yanxu" Suna bude kofar parlon Abuturrab yyi ido hudu da jiddah tana tsaye daga kusa da kofan parlon, sunkuyar da kanta tayi ta koma gefe cikin sanyin murya tace "Ina yini" Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon, Ahmad ya sakar mata murmushi yace "Ki karasa ciki mana, kin tsaya a bakin kofa" Tana jan yatsunta tace "Abinci xan amsa inji Maman Abdallah" Ahmad yace "Toh ki karasa ciki" Ta d'an karasa amma ba can cikin parlon ba tace "Na gaya ma Aunty Huraira tace toh" Umma ce ta fito kitchen ganin jiddah tace "Yau ma jikin kofar kika makale Jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Ma su sunan ki kuwa suna da sakin jiki ke ban san ya haka ba" Ahmad yace "Bakuwa ku ka yi gidan Umma" Umma tace "Ehh bakuwar Amina ce, gashi har yau taki sakewa" Ahmad ya kalleta yana murmushi yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" tausayinta Ahmad ya ji har cikin ransa, without allowing that to show... ya buda ido yace "Lahh Ummin Captain ce ashe" Umma tayi murmushi tace "Kai ba Umminka bace kenan?" Ahmad ya shafa kansa yana murmushi ya kalli Abuturrab da ya hade rai kamar bai ta6a dariya ba yana kallon TV, yace "Captain ga mai sunan Ummin mu fa" Umma na kallon Jiddah tace "Karasa kitchen din ki ga ko ta gama xuba maki, kinji" Kitchen din Jiddah ta nufa ta shiga ciki, Abuturrab ya gaida Umma a hankali, amsawa tayi da murmushi tace "Alhmdlh jiki yayi sauki kenan, ai daxu da muka je kana bacci" D'an murmushin karfin hali yayi yace "Naji sauki Umma" Tace "Toh Allah ya kara lafiya Son, bari a kawo maku abinci yanxu" A nan parlon ta barsa shi da Ahmad, Jiddah ta fito rike da abinci, bata yadda ta kallesu ba ta nufi kofa kamar mara gaskiya ta fita... Washegari Thursday karfe tara da yan mintuna Abuturrab ya fito daga bedroom dinsa, Bangaren Abbansa ya nufa, sai da ya bude kofar parlon Abbansa yace "Alhmdlh.... Much better now" sisters dinsa ne xaune parlon suna masa ya jiki kamar baxai amsa ba kuma bayan ya isa bakin kofar parlon Abbansu ya amsa sannan ya shiga parlon da sallama, Aunty ce tare da Abba a parlon, tun da ya shigo Abbansa ke kallonsa, ya xauna kasan carpet yace "Sannu da dawowa Abba" Abba yace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdlh na ji sauki" Abba yace "Allah ya kara lafiya" Aunty tace "Jiki kam Alhmdlh, kamar ba shi ba shekaranjiya" Abba na kallonsa yace "Kana stressing kanka da yawa ko, you look stressed out" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba" Aunty tace "Kamata yayi ka dau hutun ko da sati biyu ne ka huta har ka murmure gaba daya, you look so lean" Shi dai Abuturrab murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Aunty ta mike ta nufi kofa bayan ta dau tray din da ta kawo ma Abba shayi ta fita, Abba na kallon Abuturrab yace "Hope babu damuwa Aliyu?" A hankali Abuturrab yace "Akwai Abba" Da mamaki Abba ke kallonsa, kafin yace "Talk to me, meye damuwar" Abuturrab ya kallesa lkci daya jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya yace "Abba i did something...." Sai kuma yayi shiru, Abba ya ajiye cup din hannunsa yana kallonsa da kyau yace "Feel free son, tell me what happened" Abuturrab ya sunkuyar da kansa nan ya sanar ma Abbansa komai tun daga farko, bai boye masa komai ba, Abba couldn't stop looking at him da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, Abuturrab ya xauna kan kneels dinsa a hankali feeling so remorseful yace "Kayi hakuri Abba, i neva thought things will turn out that way da ban yi komai gaban kaina ba, ban san haka lamarin xai kasance ba, i am sorry father, I don't know if this means failing you, kayi hakuri Abba..." Abba ya dafa shoulder dinsa ya sauke ajiyar xuciya amma kuma ya rasa ma abinda xai ce masa, da alama ya girgixa sosai da batun shi ma, Abuturrab yace "Xan iya kai ka gun mai anguwan ma so u can believe me 100%, ban ta6a xaton haka abubuwan xa su tafi ba da ban yi ba" Abba ya kara sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ka Aliyu, but this is astounding..." Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya dinga pondering kan lamarin, sai yake ganin abun kamar a mafarki, his son getting married babu shi, babu yan uwansa, infact unprepared marriage, hakan bai ta6a faruwa a xuri'arsu ba kaf" Abuturrab ya katse ma Abba tunaninsa ta hanyar cewa "Amma xan saketa Abba" Da sauri Abba ya kallesa yace "Why? Ba saboda ka taimaketa ka aikata hakan ba, xaka saketa saboda me kuma?" Da mamaki Abuturrab ke kallon Abbansa, can yace "Abba amma ai ni baxan iya xama da ita as a wife ba, i just can't Abba, she is not my class" Abba ya dinga kallonsa, Can ya girgixa kai yace "Dole hakan xaka xauna da ita kuwa, before making the decision of marrying her ai ya kamata ka fara naxarin ko xaka iya xama da ita din as wife or not, ka saki yarinya for what reason, i thought it's ur decision? Ko ka dau aure abun wasa ne, ka xata film ku ka yi acting a wajen ranan, ko kuma wasan yara ku ka yi?" Abuturrab ya marairaice hankalinsa a mugun tashe yace "Abba wllh kawai don in taimaketa a wannan moment din ne yasa na amince da auren ba wani abu ba, naga xa ayi ruining rayuwarta ne yasa na amince Abba, amma kuma nayi niyyar sakinta ai bayan daura auren" Abba na masa wani kallo on a serious note yace "Erase that harebrained idea right away, babu wani sakinta da xaka yi, tunda har aka daura auren shaidu duk sun shaida ka bada sadaki, babu wani abinda ya rage illa kayi accepting fact din ka tare da matarka, kada in sake jin ka yi xancen saki, ba drama ko film din Hausa kuka yi acting ba a wajen" Da mugun mamaki Abuturrab ke kallon Abban nasa baki bude, sanin arguing further won't favor him yasa yayi shiru, but deep down him yasan in har yana son ci gaba da rayuwarsa yanda yake yi a da to sai ya datse igiyar yarinyar nan a kansa, idan bai saketa ba he will never have peace of mind, he might even turn a Sadist, sakinta kuma da xai yi babu wanda xai bari ya sani, they will stay in the same roof but not as husband and wife, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Sai ka karasa gyara gidanka na nan garin ku tare, i will call all my brothers and inform them what happened, since u chose this for ur self" Abuturrab ya ji kamar yayi kuka sanin in har cousins da frnds dinsa suka ga cewar wannan yarinyar ce matarsa ai tasa ta kare kuma, he don't even want to imagine how they will make jest of him and even laugh at him, yayi narai narai da ido ya marairaice yace "Abba don girman Allah ba sai ka gaya ma kowa wannan abun ba pls I'm begging you Dad" Dariya ya kusa ba ma Abban nasa ganin yanda ya marairaice, wanda he couldn't help it but laugh, duk da kasancewarsa musulmin kwarai sannan dattijon kwarai ne kadai ya sa ya saduda yayi give up da wannan auren na d'an sa, amma banda haka shi da kansa xai iya sa Abuturrab ya saketa don har cikin ransa bai ji dadin wannan lamarin ba, Lkci daya idanuwan Abuturrab suka kada sosai ya kife kansa da kujera, Abbansa yaji tausayinsa ba kadan ba yana murmushi yyi patting shoulder dinsa cikin kwantar da
Chapter 31 · 0% Book details