Sashe 102
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 1 min read
ba lafiya a ciki, ga dai abu kiri kiri fa" Ummi tace "Aa ki kyalesu kawai, shi ba yaro bane kuma sarai da hankalinsa, abinda kike tunani ba shi bane, shi dai ne ya xabar ma kansa haka, ai ba shi daya na haifa ba dai? Dama shi da namiji ai wasu kake haifa ma" Umma tace "Ki kyaleni da shi xan saita masa xama wllh" Sun jima sosai suna waya, Jiddah dai duk sai bata ji dadi a ranta ba, taji kuma a xuciyarta tana son yi ma Abuturrab magana, to amma a ina xata gansa??