Sashe 49
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
xan siyo kayan abinci da komai da xa ki bukata a kitchen, don haka duk abinda na gaya maki yanxu baki da wani da xai sake gaya maki a gidan nan, it's better ki tabbatar kin gane komai...." Kallonsa kawai take tana jin wani kuka xai taho mata, ya ki yrda ya hada ido da ita, ya daga kafada kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta sauke idonta a hankali wani hawaye me xafi ya shiga sakko mata. Abuturrab na dawowa daga masallaci da magrib ya shigo da abinci, sama ya haura ya kwankwasa kofar sannan ya bude, tana xaune saman darduma, ya ajiye mata abincin bakin kofar, ya d'an tsaya wanting to ask what she is even reciting in her prayers, sai kuma kawai ya fasa, ya ta6e baki yayi wucewarsa, karfe tara da rabi ta gama saka kayan da ya nuna mata yace ire irensu xata dinga sa wa da daddare, wando ne dogo da riga, sosai kayan ya mata kyau tana tsaye gaban madubi ta saka daya daga hulunan da ya siyo mata, har makogwaro ta dinga jin turarrukan da ta fesa abin ka da bata saba ba, ta nufi saman gado ta takure waje daya ta kwanta ta lumshe ido... Abuturrab ya fito daga bangarensa rike da lallausan duvet, kana ganin duvet din kasan me tsada ne sosai, kamshin turarruka ne ya gauraye ko ina na upstairs din, ya isa kofar dakin, ya fi second biyar a tsaye kafin ya bude, ko motsi bata yi ba alamar ta fara bacci, ya karasa ciki ya bude duvet din ya rufeta da shi, da sauri ta bude ido, yana kallonta yace "Daga yanxu idan xa ki kwanta ki dinga kashe wuta" Ta gyada masa kai, gun switch din ya nufa ya kashe wutan dakin sannan ya fita ya kulle kofar dakin, Jiddah ta lumshe ido gabanta na faduwa don bata saba kwana ita kadai ba. Washegari Abuturrab ya tabbatar duk wani abinda Jiddah xata bukata a kitchen ya siya, tare da Ramlah suka tafi siyayyen, duk ita ke fada masa abinda xa su siya na foodstuffs, har da filling din gas sun yi, kitchen din ya dawo well stocked up with foodstuffs, few pots, and some kitchen utensils, Jiddah dai na xaune parlon tun bayan dawowarsa da Ramlah, shi ma ya aika Ramlan taje ta kirata ne, yana tsaye kitchen din Ramlah ta jera komai, yana kallonta yace "Ahmad ya koma Abuja ne?" Ta gyada masa kai, ko ranan ma Ahmad ya kirasa amma yaki dagawa kamar dai shi ya aura masa jiddah, Ramlah na gamawa Abuturrab ya bata 2k transport ta fito daga kitchen din tana kallon Jiddah dake ta xaune, da murmushi fuskarta tace "Aunty amarya xan koma" ko lura da kallon da Abuturrab ke mata bata yi ba don jiddah kawai take kallo, Jiddah kam ta ga kallon da yake ma kanwartasa, cikin sanyi tace "To sai anjima" Ramlah ta nufi kofa.... bayan ta fita, Jiddah ta d'an kallesa suka hada ido, daure fuska yayi yace "In rokeki ki taso?" A hankali ta mike ta nufesa, komai na kitchen din ya shiga nuna mata da inda suke ajiye, ya koya mata kunna gas ya tabbatar ta iya kashewa ta iya kunnawa, yana kallonta da kyau yace "Anjima kafin in tafi xaki kunna min in gani" Tace "Toh" fita yyi daga kitchen din ya bar ta tsaye, ta bi sa da ido sannan ta bi bayansa. Abuturrab na komawa bangarensa ya ga calls din Umma har biyu, kiranta ya shiga yi bayan ta daga ya gaisheta, ta amsa tana tambayarsa ya gida, ya amsa mata, tace "Jiya naji ka je kun yi siyayya da Jiddah ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh Allah ya saka da alkhairi" Ya amsa da "Ameen" tace "Yanxu meye babu cikin kayan, don xan taho anjima ne, sai in ga ko xa a iya tahowa da su" Ya d'an shafa kansa yace "Kawai Hijabs, bayan shi babu wani abu" Tace "Toh xuwa wani satin sai a dinka mata su" Yace "To Allah ya kai mu" Tace "Shi kenan dai ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh sai na iso" Yace "Kamar yaushe xa ki taho Umma?" Tace "Xaku fita ne?" Ya girgixa kai yace "Xan koma aiki ne yau" Da mamaki tace "Xaka koma aiki kuma? ni na xata tunda ansan baka ji dadi ba xaka dau wani satin off?" Yace "Aa ni naji sauki, yau xan koma" Sake baki tayi, can tace "To ita Jiddar fa? Ko tare xa ku tafi?" Ya xaro ido kamar warce ta fado masa wani mugun abu yace "Aa" Tace "To ina xaka barta?" Yace "Nan gidan" Umma tace "Ita kadai?" Yace "Ehh babu komai" ta xaro ido tace "Aa gaskiya ka kawota nan kawai" Abuturrab yace "Aa xata xauna nan Umma" Umma tace "A kan me xaka bar yar mutane ita kadai a wannan gidan, ae baxai yiwu ba Abuturrab" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Umma tace fa xata iya xama, kuma ma xa a kawo mata mai aiki, ni nafi son ta xauna nan din kawai, and ranan laraba da safe xan dawo ai" Umma tace "Yaushe xa a kawo me aikin??" Da sauri yace "Ermm yau, in sha Allah" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ni dai na fi gane ka kawota nan gida Abuturrab, ina ga xai fi wllh, it's not advisable to leave her all alone a gidan nan, she is too young for that, beside bata saba xama ita kadai ba" Trying all he xan to convince her yace "Umma xafa ta iya xama wllh, u shouldn't worry pls..." Umma tace "Toh amma is there anything wrong idan ka dawo da ita nan din, idan ka dawo weekend ba sai ka xo ka dauketa ba" Yace "Umma makaranta fa xata fara soon, plss u need not to worry" A hankali Umma tace "Toh shkkn wai dama don in dinga nuna mata wasu abubuwan ne, yasa nayi insisting" Ya girgixa kai yace "Ai bata da wani lkcn Umma, xata fara boko sannan islamiyya" Umma tace "Toh shkkn" ya d'an sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh sai kin xo Umma" Tace "Kai xan ba Maimuna sakon kawai ta kawo, next week din xan shigo in sha Allah" Yace "Umma me yasa kika fasa kuma, ko fushi kika yi" Tace "Not at all, let me leave it next week kawai" A hankali yace "Toh shkkn Umma" Sallama tayi masa ta katse wayar tana mamakin irin taurin kan Abuturrab, wanda tasan da Aunty ce tayi masa wannan maganan baxai mata musu ba xai yi yanda tace, girgixa kai kawai tayi don kwata kwata bata ji dadin haka ba, Abuturrab ya sauke wani ajiyar xuciyar ya ajiye wayar. Bayan la'asar ya gama shirinsa don driving xai yi xuwa kanon, komai da yasan ya kamata jiddah ta sani ko ta iya amfani da shi a gidan sai da ya tabbatar ya nuna mata a gidan nan, abinda ya kara bata masa lkci kenan, xaune yake parlor waiting for Maimuna don baya son sai ya tafi ta xo, tana ring din bell ya mike ya bude kofar, gaishesa tayi da fara'a, ya amsa yace "Ya gida" Tace "Alhmdlh yaya, ina Aunty Amarya" Babu yabo bbu fallasa ya amshi ledan hannunta, sannan ya ciro dubu daya ya mika mata yace "Ki yi transport" tace "Tare da driver muke" Yace "Ohk" dubu daya ya kara xarowa aljihunsa ya hada ya mika mata yace "Ki saka kati" Tana murmushi tace "Aa ka bari nagode yaya" Ya hade rai yace "Amsa ki tafi" Amsa tayi yace "Sai anjima" Tayi masa godiya sannan ta juya a hankali, amma duk jikinta yyi sanyi don bai bari ta ga Jiddah ba, ya kulle kofar, kujera ya koma ya xauna yana duba abinda ta kawo, turarrukan wuta ne a kwalbansu kusan kala hudu sai burner, da wasu turarrukan na jiki, tabe baki yyi ya mike ya wuce sama, dakin jiddah ya bude ya ganta xaune duk ta dawo wani iri, tana ganinsa ta sauke kanta kasa, ya ajiye ledan yace "Umma ta bada a kawo maki" ta bi sa da kallo har ya jona burner din a socket, sannan ya bude turaren wutan guda daya ya diba ya xuba yana kallonta, bayan d'an lkci kamshi ya fara tashi, yace "Safe da yamma xaki tabbatar kin ma dakinki da parlor haka" Ta gyada masa kai kawai, waya karama ya ciro aljihunsa yana kallonta ya mika mata, ta mike ta isa inda yake ta risina ta amsa, yana kallonta yace "Number da xaki dinga samuna ne kadai a ciki, sai ki koyi yanda xaki yi amfani da shi ke kadai" cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Sannan ba ace ki xauna ke daya kiyi wani shiru kamar me xaman makoki ba, ga kayan kallo duk na koya maki yanda xaki kunna" Ta sunkuyar da kanta, kofa ya nufa yace "Na tafi" Ta kallesa da sauri tace "Ina xaka je" Yace "Garin da nake aiki" bude kofar yyi ta bi sa da ido, sai da taga ya fita kafin ya kulle kofar cikin sanyin murya tace "Allah ya tsare" Ya amsa da Ameen a takaice, da sauri tace "Yaushe xaka dawo?" Yana kallonta yace "Wannan bai shafeki ba, ko da wani abu da xaki bukata bayan duk wanda na maki??" Daga haka ya kulle kofar hawayen dake makale idonta ya silalo a hankali, ta fi minti goma tsaye yanda ya bar ta, jin an tada mota ta kalli window da sauri sannan ta karasa window din ta d'an bude labule tana lekan waje, tana ganinsa ya fita da motar, a hankali ta fara kuka ta xauna nan kasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar ana dada tunxurata, Abuturrab ya sauka motar yana kallon gate din gidan, he just dont have any option then to close the gate from outside, don bai ma son ya gwada mata yanda ake kullewa daga ciki balle ya sa ta kulle ta ciki, yasan probably kafin ya dawo weekend an samar masa mai gadi kamar yanda yayi requesting ayi, ya kulle gidan ya koma ya shiga motarsa yana karasa addu'o'in da yake yi tun daga compound a ransa ya bar layin.....