Sashe 201
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
sosai, a hankali tace "Toh ai ba a unguwar nake ba yanxu..." Yace "Toh idan kika dawo anguwan fa?' ta xaro ido tace "Me xai maida ni?" Yace "Ni xan maida ki duk sanda kika shirya" Tayi wani murmushin bata ce komai ba, yace "Ko baki son komawa?" Tace "Wai in koma inyi mene??" Yace "Ki koma kiyi ibada" Ta xaro ido tace "Wani irin ibada?" Yace "Irin warce baki samu daman yi ba" Tayi shiru kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Ni ban gane ba" Yace "Irin warce Allah yace ayi" Tace "Ban san shi ba" Yace "Xaki san shi kwanan nan" Bata kuma cewa komai ba shi ma yayi shiru, a hankali tace "Allah ya kara lafiya" yace "Ameen, sai dai ban ta6a cin awaranki ba tun da can ma" Tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Yeahh" tace "Sai ayi maka" Yace "Irin na Baabarku?" Shiru tayi, ya shafa kansa yace "Sai anjima" daga haka ya katse wayar ta kalli screen din sannan ta ajiye a hankali... Abba ne xaune parlor da Hajja sae Aunty, Hajja na gyara daurin dankwalinta tace "Ae kaga saboda xuciyata me kyau ce bana riko duk da rashin kunyar da yarinyar nan ta min hakan bai hanani tsayawa har sae da na tika uwar Bashir da kasa ba, don da cewa tayi inaaa d'an ta baxae ta6a auran mara asali ba, to duk duniya banda shege waye bai da asali, da yake kabiru na jin maganata yana min biyayya don har ma ya fi ka, ba shiri ya taka mata birki ya dau maganata da muhimmancin gaske, to ba gashi komai na tafiya dai dai ba" Abba dai sae kallonta yake, Aunty dake ta boiling from inside sai kallon Hajja take amma ba daman cewa komai, kasa hakura tayi daga karshe ta dake tace "Toh shi Bashir din me yace Hajja?" Hajja tace "Aa baya ma kasar, yo shi Ina ruwansa, galallawa ne fa yaron nan da kuke gani, duk yanda nayi yace dai dai ne yasan baxan masa xa6in da xai cucesa ba, toh ni abinda yasa na makale ma yarinyar saboda tsaftarta ne baxan biye rashin kunyan da tayi min ba, duk da nasan wannan narkekiyar matar Ramlah ce xata koya mata ta min haka, amma da baxa ta min haka ba... Yanxu dai Kabiru yace kai sai ka xama madaurin aurenta wato waliyyinta, so nake kafin Bashir ya dawo an daura sai dai kawai a wanketa a kai masa dakinsa, uban ma ya amince da hakan...." Abba yace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Hajja tace "Cewa xaka yi Allah ya baki ladan wannan jihadi Hajja, ka ga ai da ni tsohuwar banxa ce baxan so in hada Jiddah da jinina ba don wllh gidan da Aliyu ya kai ni a hayin rigasa yace nasu ne, duk da a rushe gidan yake amma kana ganin gidan kasan na fakirai ne, su talaucin ma ba karamin kamu yyi masu ba, da kyar ake samun masu talauci irinsu, mu dai ba saboda Allah kawai muke abun mu ba dama, Allah dai kawai ya bamu lada" Mikewa Aunty tayi ta nufi kofa ta fice Hajja ta bi ta da wani kallo tace "Ae kaga da yake ta kaina nake, ni ko da wasa ban ta6a kawo d'an ta Salem a rai ba balle wataran ta zageni ko shi ya xageni, amma yanxu haka da xaka shiga xuciyarta xaka san hadin nan bai mata ba, na rasa abinda jiddah tayi mata da wannan tsana haka" Abba yace "Xan d'an fita Hajja, sae na dawo anjima" Tace "Toh Allah ya tsare, cikin satin nan Kabiru yace xa a kawo komai kilan har sadaki, wato shi ma xaman yaron a haka ya ishesa ashe, magana ce kawai baya yi, gashi sae yyi ta fita kasar waje an rasa uban me yake xuwa yi a can" Daga haka ta mike tace "To ba ruwana, ita warcan narkekiyar sae ka tafi har can gidanta ka yi mata bayanin komai don kar ta xo ta min rashin albarka ta cuce ku, ba karamin aikinta bane, don duk tayi bake bake kan lamarin yarinyar" shi dae bai ce mata komai ba har ta fita, girgixa kai kawai yake yana mamakin Hajja, ya dau wayarsa ya shiga kiran Ummi, tana shigowa ya tsara mata duk yanda suka yi da Hajja, Ummi ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Haka dama auren yake da sauki Yallabai, ina laifin ma ta kare secondary din tunda ta dauko hanya? Ita fa Hajja idan ta shirya abu a ranta babu me canxa ta, sannan tana ta nuna Bashir din ma yace ba ruwansa, tayi duk yanda tayi.. to an ta6a aure haka babu fahimtar juna tsakanin mata da mijin? Ko magana fa basu ta6a yi ba a waya" Abba yace "Ba dai tace shi Kabir ya amince ba ya bata goyon baya? To Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, ita ma yarinyar Allah ya sa hakan babban alkhairi ne a gareta" Ummi dai tayi shiru, can tace "Ba fa a tambayi yarinyar nan ko tayi na'am da hakan ba, it's more or less like auren dole xa ayi mata, gwara a fara jin ta bakinta Yallabai, kar a ga kamar don ba mu muka haifeta ba shi yasa ake juyata yanda ake so, hakan ba dai dai bane wllh" Abba yace "Wannan kuma ai aikin ke da Hajiya Ramlah ne, xuwa anjima sai kije can gidan kiyi mata bayani sannan a ji ta bakin ita yarinyar, don a yanda Hajja ta axalxali batun nan sai ta iya cewa cikin sati biyu ma take son ayi bikin" Ummi tace "Toh Allah ya kyauta, amma ya dace ka kira shi mai martaban kaji ta bakinsa, kilan ma shirinta ne ita kadai wa ya sani?" Abba yace "Ehh ina jiran nan da d'an anjima ne xan kirasa in sha Allah" Ummi tace "Toh Allah yayi mana me kyau" Abba ya amsa da "Ameen" mikewa tayi ta fita daga parlon. Umma ce xaune bedroom dinta tare da Ummi, ta jira har Ummi ta kai aya sannan tace "Kinga yanda baxan so ayi ma Maimoon ko Safiyya ko Siyama auren dole ba, to haka ita ma Jiddah baxan yarda da hakan ba Yaya, a ajiye batun ai ko bani na haifeta ba, wllh yanda xanyi ma 'ya yan cikina ita ma haka xan mata, ku yaya Hajja sai tayi ta wasu abubuwa kamar dai notiran kanta sun kwance amma ku dinga biye mata a rasa me gaya mata gaskiya? Meye amfanin hakan fisabilillah? Ni fa na xata tunda nace aa an bar xancen ne ashe abinda ya kai ta bauchi kenan ma? To ni dai sai dai a fadi duk abinda xa a fada amma Jiddah is too young for that marriage, sannan har take ikirarin uwar Bashir din bata so amma tayi ruwa da tsaki a kan lamarin har sai da ta sa kowa ya amince, wani xaman aure take son yarinyar taje tayi a wannan babban gidan Ummi, shikenan saboda bata da iyaye ita marainiya ce sai aka ce bata da gata? Aa wllh tana da gata don yanda na dau su Maimoon haka na dauketa, Hajja taje can ta samar ba Bashir wata matar amma ba Jiddah da ko secondary din ma bata kare ba" Ummi tace "Toh ina ga xai fi ki tashi kije ki samu Hajja kiyi mata duk bayanin nan, ke wani lkcn kina magana kamar baki san Hajja ba, kin gan ni nan duk fa abinda xai dameni ko ya bata min rai bana so yanxu, ta kaina kawai nake babu ruwana, In dai Bashir din da bakinsa yayi admitting yana son Jiddah kuma xai xauna da ita i see nothing wrong with that, domin kuwa shi din ba wani xama yake a kasar ba, bini bini ya fita, to ba sai ya tafi da matarsa ba, ina Jiddah xata ga uwarsa idan ba dawowa kasar suka yi ba, kinga wllh yanda kike hakikancewa a batun nan tsaf Hajja xata ce Hassada kike tunda ba er ki bace, don haka ina baki shawara ki bi komai saisa saisa babu ruwanki..." Umma tace "Aa kiyi hakuri yaya a gaskiya da ruwana, Hajja kuma ba tun yau na saba da tijararta ba, kuma ni kema kin san raga mata nake kawai sabida ke, banda haka ni baxan yi tolerating haka ba, kuma a gaskiya idan haka abubuwa xa su ci gaba da faruwa gwara ki tafi da Jiddah can gidan don ma kada taga kamar ban tsaya mata ba tunda ni ba uwarta bace.. ki tafi da ita kawai ku yi yanda ku ka ga ya dace da ita, dama ai Hajjar ta sha fada min ba don Aliyu ba a ina xa a santa, don haka ki tafi da ita ku yi mata bayani a can amma ba a nan ba" Ummi dai kallonta kawai take, Umma ta mike tace "Haka kawai ga gaskiya a dinga takesa kiri kiri, ita Hajjar Allah ce da dole sai an bi abinda tace mata gigin tsufa duk ya rikitata kuma ayi ta bin ta a haka, ba ga jikokinta sa'annin jiddar ba, tayi masu auren mana idan haka ne, kiyi hakuri fa kar kice rashin kunya nake maki Yaya, aa gaskiyata nake fadi, kawai don Jiddah bata da gata a duniya sai a tauyeta?? To dauketa ku tafi kuyi yanda ya dace da ita, babu ruwana" Mikewa Ummi tayi ta fita daga dakin tayi wucewarta... Bayan tafiyar Ummi da kusan awa daya su Maimoon suka dawo Islamiyya, bayan sun gaida Umma dake xaune parlor xa su wuce dakinsu Umma tace "Da wani number kike waya da Aliyu Maimuna?" Maimoon ta dawo, Jiddah ta d'an saci kallon Umma sannan ta wuce ciki, Maimoon tace "Da numbersa ne yana shiga" Umma tace "Toh" daga haka ta mike ta wuce dakinta ta hau kiran Abuturrab wayar bai yi connecting ba hakan yasa ta ajiye ta fito... Sai can da daddare Umma ta sake kiransa sai ya shiga, yana dagawa bayan sun gaisa tace "Kana ji na Aliyu?" Yace "Ina ji Umma" Tace "Ka dai ji abinda iyayenka ke shirin aikatawa ai ko?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Na me fa?" Tace "Ohh