Sashe 23
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 4 min read
da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan" Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa" Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito"