← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 205

Sashe 202

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk baka sani ba, to Hajja ta dage ita dole sai tayi ma Jiddah aure da Bashir, na kiraka ne kuma saboda naga kamar tana jin maganarka, i want u to put a stop to that, ko secondary bana fatan Jiddah ta gama ace xa a aurar da ita, don haka talk sense into Hajja" Abuturrab dai yyi shiru, ta hade rai tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Ina ji Umma, xan kirata in sha Allah, nobody told me about it, tace to wa xai gaya maka dama tunda cutar yarinyar ake son yi" a hankali Abuturrab yace "Shkkn, i will call her in sha Allah" Tace "Do so immediately" Daga haka ta katse wayar ta ajiye lamarin na kara kona mata rai, wai aure kamar xa a aurar da wata mara makabuli, to su yi ta gani. Hajja ta gama sauraron Abuturrab tsaff sannan tace "Toh ko ubanka Usman wanda shine lallai dole ne bai isa yace xai dakatar da ni kan abinda nayi niyya ba, kai kuma a wa Allah na tuba? Kai da ka walakanta yarinya ka cuceta ka mayar da ita baxawarar karfi da yaji sannan ka saketa? Kai fa ba wani abu ke damunka ba banda kishi, kuma sai dai ka hadiyesa don tayi maka nisa wllh, idan ma sa ka aka yi ka kirana ka koma ka fada ma wanda ya sa ka ai ba Hajjar da bace yanxu, bana nufin er yarinyar nan da sharri banda alkhairi, yanda ta taso cikin bakar talauci da rashin ga ta so nake ita ma ta ci arxiki ta bar sa a inda ta gansa, so nake ita ma ta shiga babban gida a dama da ita, to na meye kowa sai bakin ciki abinda ni Allah bai daura min ba kenan, to kowa dai ya ci kansa ya kurkure da bakin ruwa, kai kuma ina baka shawaran ka kauda idonka a kan duk wani abu da ya shafi yarinyar kayi mana me wuyar tunda ka kawota cikinmu" Tana kai wa nan ta katse wayar, Abuturrab murmushi kawai yake yi... Kawai bayan sati daya sai ga shi Aunty ta kira Umma wai an kawo kudin Jiddah daga masarautan bauchi... Ummi ta fi minti talatin rike da wayarta bayan aunty ta katse, Allah kadai yasan yanda take ji a xuciyarta a lkcn.... Sai yamma ta shirya ta tafi gidan don bata son xuwa ta tadda mutane, ai ko duk yan kawo kudin sun watse, parlon Abba ta shiga direct, yana xaune shi da duk brothers dinsa, Umma ta xauna bayan sun gaisa gaba daya tace "Alhaji Usman dama wajenka na xo" Abba na kallonta ya dau wayarsa yace "Toh Allah ya sa lafiya, in taso ne?" Tace "Ehh" tana fadin haka ta tashi ta fita, Abba ya mike ya bi bayanta, can kofar gida suka fita tana kallonsa tace "Yanxu Alhaji an xaunar da ita yarinyar an tambayeta ko tana son auren nan da ake shirin kulla mata? Domin bata da kowa ba yana nufin bata da gata Alhaji, this is wrong wllh" Abba yace "Domin bata da kowa mu ma ba yana nufin xa mu cutar da ita bane, did you know this is a great privilege to her also? Ki duba fa wanda ake son hadata aure da? Wa kike tunanin Hajja xata yi ma hakan banda ita din??" Umma tayi wani murmushi tace "Wato privilege? But she never begged for that privilege Alhaji, idan kuma xa ayi adalci kamata yyi a ji ta bakinta don a fita hakkinta, an ta6a yi ma mutum dole a aure? Shkkn sai aka ce ita bata da choice da dream dinta?" Abba ya duba wayarsa jin shigowar message yana dubawa yaga message din Abuturrab, and the content goes as thus "Kada ya kasance ana neman Aure ne a kan Aure Abba, that is highly prohibited in islam.... We plan but Allah plans best in sha Allah" Abba ya karanta text din ya fi sau uku, can ya mika ma Umma dake kallonsa, Umma ta amsa tana dubawa ita ma dai sau ukun ta karanta tana sake duba sender din, a ranta tace Aliyu?? A fili kuwa tana kallon Abba tace "Shashasha, to me yake nufi da text din? Wa ake nema ma aure a kan aure?" Abba yace "I am still trying to understand that too" Umma tace "Ka kirasa" Ba shiri Abba ya hau kiransa amma ya ji layin a kashe, ya kira sau uku duk a kashe, Umma tace "Wai wa yake nufi ne?? Wa ake nema ma aure kan aure?" Abba yace "Tare mu ka karanta text din nan yanxu Hajiya Ramlah" Umma tace "Toh ina jin shaye shaye ya fara a can din ko" Abba dai bai ce komai ba, Umma tace "Ni dai na gama magana, idan xa ayi mata adalci ayi mata, a tunaninku gata xa ayi mata tunda xa a aura mata d'an sarki, to amma kwanciyar hankalin xaman gidan auren fa, tunda naji ance uwar tasa ma ba so take ba, kuyi ma Allah a duba lamarin nan idan kuma shakkar yi ma Hajja magana ake ni sai inyi mata wllh" daga haka tayi ma Abba sai anjima ko gidan bata sake shiga ba ta bude motarta ta shiga, driving take amma tunanin solution da xata samar ma Jiddah take don in dai kuwa aka yi auren nan kilan bata doron kasa ne, samm baxata ta amince da auren ba, baxata ta6a bari a shiga hakkin yarinya ba. Abba na komawa cikin compound ya sa a kira masa Ummi, tana fitowa ya mika mata wayarsa yace "Ko xaki iya fahimtar wani abu a message din nan kiyi min bayani??" Ummi sai karanta message din take da surprise barin da ta ga cewar Aliyu ne sender din, can ta kalli mai gidan nata tace "What's the meaning of this?" Yace "Shine nake son ki min bayani" tace "Jiddar matar aure ce da xai ce kar a nemi aure kan aure?" Abba yace "Shine nake son fahimta Hauwa" Ummi tace "Ikon Allah, to ka kirasa" Abba na kokarin sake kiransa yace "A kashe wayar" sai gashi ance wayar a kashe, Ummi tace "Ji d'an rainin wayo, aurar da ita yayi ne ba a sani ba, ko ko?" Abba dai bai ce komai ba yayi shigewar sa ciki, Ummi ta bi sa da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunanin xata yi, anya kuwa Abuturrab na da kai? Menene manufar wnn text din wai kar a nemi aure kan aure, to ko aure yake nemar ma Jiddar basu sani ba ne. Abba na komawa gun brothers dinsa su ma ya basu wayar su duba message din, bayan sun duba da daddaya da daddaya, suka dinga kallon Abba, Alhaji Salmanu yace "Neman aure kan aure kuma? To ko dai bai saketa ba ne dama Alhaji Usman?" Abba yayi dariya yace "Ya fara hauka kenan, ai har yanxu takardan na nan bai je ko ina ba" Abba na fadin haka ya mike ya wuce daki sai gashi ya fito da takardan ya mika ma Alhaji Salmanu ya amsa ya karanta sannan ya ba duk sauran ma suka duba, Alhaji Salmanu yace "Ikon Allah, to me yake nufi da hakan? Is he even in his right senses?" Abba ya daga kafada yace "I thought as much" naxari duk suka yi shiru suna yi, Alhaji Umar yace "Try his line ko xai yi connecting" Abba ya sake kira yaji a kashe, Alhaji Lawal yace "Toh ko dai komawa yayi aka sake daura masa aure da yarinyar?" Kallonsa Abba yayi da sauri almost with shock, sai kuma yayi wani dariya yace "Aa he must be joking ashe, har ya isa ya sake yin hakan? Da kuwa nayi disowning dinsa wllh... Allah kuwa da ya ga the other side of me, wato ga yan iska ya ajiye, wllh in har hakan ne ya kasance Aliyu xai yi mamakina ainun" Alhaji Umar yace "Ikon Allah, that just dawn on me bayan Lawal ya fadi haka, in dai kuwa ba shi ya koma ya aureta ba to wani ya kai ya aureta, don babu yanda xai turo wannan message din idan ba dayan biyun abinda na fada ya kasance ba, but that's bad... Who does that, ya maida mutane kananun mutane kenan yake nufi ko me?" Abba dai da alama ransa idan yayi dubu ya baci, daukar wayarsa yayi ya tura ma Abuturrab text kamar haka, "call me immediately after switching on ur phone, i said immediately!!!" Alhaji Lawal yace "Lallai kuwa tunda har ya turo message din nan Komawa yaron nan yayi aka daura masa aure da yarinyar ba tare da sanin kowa ba, tunda ya san waliyanta sannan tun farko shi dama babu wanda yayi masa waliyyanci a cikinmu, don haka abu ne me sauki garesa" Abba dai baya cewa komai a parlon... Har bayan sati da text din nan wayar Abuturrab a kashe yake, Jiddah na xaune daki tare da Maimoon da daddare tana son mata magana amma ta kasa, don bata ma san ta ina xata fara maganar ba, tun 3 days ago maganar ke cin ta amma ta kasa yi mata shi, can dai ta dake a hankali tace "Maimoon ya jikin Ya Aliyu?" Maimoon ta kalleta tace "Wllh I don't know, I can't reach him for a week now" Jiddah tace "Both Whatsapp?" Maimoon tace "Baya hawa...." Jiddah bata kuma cewa komai, Maimoon dai sai kallonta take, mikewa tayi ta koma side din da take kwanciya tayi kwanciyarta.... Ranan Friday bayan an sauko sallan Juma'ah, Jiddah na xaune xaune bakin tap din compound din gidan tana wanke hijabs dinta biyu don Safiyya na wanki a washing machine aka bude gate din gidan, daga kai tayi a tunaninta Ahmad ne don in dai ya shigo kd ya kan fara xuwa ya gaida Umma kafin ya tafi gidansa, tun da ya shigo take kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, saukarsa kasar kenan kuma babu inda ya fara nufowa sai gidan Umma......
Chapter 202 · 0% Book details