← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 205

Sashe 167

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

a airport din Abuja muka hadu taje gun uncle dinta, ni kuma mun sauke jirgi, and she requested my digit na bata kawai don ban iya walakanci ba, sai kuma coincidentally na dawo wani weekend na ganta a gidan nan ta xo gun Aunty da aunt dinta ashe Mum dinta close frnd din Aunty ce" Ummi dake ta kallonsa tace "Sai aka yi yaya? Sai aka ce ka so ta dole har ka aureta?" Yace "Aa Ummi but Aunty ce ai..." Sai kuma yayi shiru, Ummi ta tabe baki tace "Kaga Aliyu rabani da wannan labarin da na sani, yanxu dai kawai kayi hakuri ka nema mata house help, da xata dinga tsaftace maka gidan ka, sai kuma ka ci gaba da hakuri da sauran halayen nata tunda dai auren soyayya ku ka yi ba auren kiyayya ba" Bai iya yace komai ba, Ummi dai sai kallonsa take, amma can kasan xuciyarta tausayinsa take, she understands what he is going through, barin shi da yayi detesting kazanta with passion, ita har ta mance rabon da ya shigo dakinta balle har ya dade haka yana xance da ita kai tsaye, Ya d'an ja tsaki underneath his breathe yace "Karamar yarinya ma da ta kusa doubling age dinta warce ta tashi a ghetto bata irin abinda take yi na kazanta wllh, tun daga balcony nake jiyo kamshi lkcn da yarinyar ke gidan idan na dawo gida, for once ban ta6a shiga kitchen naga dirty utensils ko daya ba, ni har kunyar wani nawa nake ya xo gidana yanxu, dama a garin nake sai in dinga gyarawa ni kullum, kawai ita abinda ta sani sai tayi wanka ta fesa turare ta xauna tana danna waya, sai tara kawaye a gida" Ummi tace "Toh wai ita kuma wannan karamar yarinyar da kake sa wa a baki kake comparing da matarka meye hadinka da ita ne, why don't u face ur life ka daina mentioning dinta a lamarin ka, did she have anything to do with u again xaka sa ta a bakin duniya" Ya kalli Ummi amma bai ce komai ba, Ummi tace "Ni ka tashi kaje ka same matarka ka bata hakuri ka dauketa ku tafi gida, Allah ya ci gaba da daidaita ku, ba ruwana da matsalar cikin gidanku, it's something u should have known before marrying her" Abuturrab yace "But how mum, kullum fa fes fes xaka ganta a titi, waye xai san xata yi haka?" Ummi tace "Allah ya kyauta" Ya kwanta saman gadonta yace "Ni sai na ci abinci Ummi, kuma ba yanxu xan tafi ba sai after isha, kullum fa sai nayi takeaway din abinci bata girki" Sharesa Ummi tayi ta mike ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta kawo masa abinci dakin, tana ajiyewa ta juya ta fita, shi kam ko kallonta bai yi ba, can ya mike ya sauka kasa ya dau plate ya fara dibar abincin. Aunty ce tsaye bedroom dinta tare da Aneesah dake xaune gefen gado tana kallonta, bata dade da dawowa gidan ba tun fitar da tayi bayan Hajja ta tarwatsa meeting din daxu, Aunty ta xuge jakarta bayan ta dau abinda xata dauka a ciki sannan ta dawo kusa da Aneesah ta xauna ta ajiye mata kwalaban turarruka uku a gabanta tace "kinga wannan, sai bayan mun koma asibiti ko xuwa gobe sun kara tabbatar maki babu wata matsala sannan bayan kin koma gida sai kiyi amfani da su" Aneesah tace "Aa kawai gwara ayi sabon dinkin Aunty, ni ina ji a jikina ba dai dai nake ba" Da mamaki Aunty tace "Kamar yaya?" Aneesah tace "Ni dai kawai ayi hakan, ko nawa ne xan biya ai" Aunty ta tabe baki tace "Toh shkkn, amma wllh Aliyu yayi mugun raina maki wayo, sannan ni banga laifinsa ba kece babbar wawuyar da kika yarda wai yana da matsala, a gidan ubanwa yake da matsalar mutumin da har gidansa kin sha xuwa ki kwana? Ko ke duk xuwan da kike gidansa a Abuja kin ga alamar yana da matsala?" Aneesah ta tabe baki tace "Ban ta6a ganin haka ba wllh, kawai shi dai baxai yi intercourse ba sbda gudun sa6on Allah amma ba don bashi da lafiya ba ko wani abu, amma babu abinda baya min ai, ce min yayi of recent ya samu matsalar" Aunty tace "Wllh ni ban yarda da kanwar uwar nan tasa ba don ita ma waye bai san tana shige shige ba kilan taje ta hango aikinmu ne tasa aka lalata, shine yake ta maki hanya hanya..." Aneesah tace "Toh ai da kin tambaya inda kika je daxu" Aunty tace "Wllh na manta shaff ban tambayi mutumin ba, amma akwai wani da xan kira anjima a benue, xai sanar da ni komai, yanxu kuma sai ki kirgo dubu talatin na turaren nan ki bada" Aneesah tace "Ina na gansu Aunty, har yau fa nace maki kudin nan da kika ce in tambayesa sai min yawo da hankali yake, yace yau yace gobe" Aunty tace "Rabu da shi don ubansa, xa muyi maganinsa nan ba da dadewa ba, muna nan dake sai account dinsa ya dawo hannunki gaba daya" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty ta jawo pillow ta ture kananun kwalaban turaren a karkashi da sauri, Aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama kansa a kasa, Hade rai Aunty tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta shimfida darduma ta hau sallahn isha, Aneesah dai sai wani cika take tana batsewa tana danna waya, ya ja stool ya xauna ya fiddo nasa wayar yana dannawa, yana ta xaune har Aunty ta idar da sallah, sannan ya kalleta yace "Ina yini Aunty" a takaice Aunty tace "Lafiya lau, sai yanxu ka ga damar shigowa bayan ina ganin sanda ka shigo gidan tun kafin magrib?" Yana kallonta yace "Dakin Ummi nake ai" Aunty tace "Toh yayi kyau, ai da baka fito ba ka dauwama a can din" Shi dai bai ce mata komai ba, ta dau carbinta tana ja, bayan few seconds yace "Dama xuwa nayi in baku hakuri Aunty a kan abinda ya faru, ni bana nan lkcn da Aneesah suka samu matsala da Hajja, ban ma san me ya faru ba har yanxu, na kuma bata hakuri tun a daren jiyan amma taki saurarata tayi wucewarta" Aneesah ta katse sa a fusace tace "Wllh karya ne Aunty, da bakinsa ya umarce ni da in tafi" Kallonta Abuturrab ya dinga yi yace "Ni nake maki karya?" Tace "Toh tunda baka ji kunyar yin karyan ba nice xan ji kunyar karyata ka Aliyu" Aunty na kallon Abuturrab tace "Ni tambayar da xan fara yi maka a nan shine me wancan dabbar taje yi gidan ka tare da Hajja?" Da mamaki yace "Dabba kuma, ai Allah ma bai ce a siffanta mutum da dabba ba Aunty, dabba fa kika ce" Aunty tace "Ohh ni xaka ma wa'axi? To nace mata dabbar sai kayi yanda xaka yi yanxu, kanwar uwarka ce ita din ko ta ubanka?? Ko uban meye hadinka da ita xaka ce kar in kirata da dabba? Ka bani amsar tambayata uban me ya kaita gidanka Aliyu?" Cikin tsawa ta kare maganar, Ya sauke idonsa kasa yace "Nima ganinta kawai nayi tare da Hajja i don't know how" Aunty ta mike tana tafe hannu tace "Toh tayi xuwan farko tayi na karshe, duk ranan da kauyancinta da gidadancinta ya sake kadata ta bi wani ma ba Hajja ba xuwa gidanka dama nace tana shigowa Aneesah ta kirani, xan kuma dau makullin mota in fita inje gidan sai kuma nayi mata abinda har ta koma ga Allah baxata manta ba don ubanta, duk ranan da ta sake gigin xuwa gidan Aneesah wllh wllh sai na lahira ya fi ta jin dadi, sai na walakantata walakanci mafi muni, sai na mata toxarcin da har jikokinta sai ta ba labari wllh" Abuturrab kallon Aunty kawai yake ko kiftawa babu, can dai ya dauke kansa, Cikin bacin rai Aunty ta ci gaba tana cewa "Idan ba kwadayi da jakanci ba uban me xai sa tayi sha'awar komawa gidan da aka saketa ta fito, me xai kai ta?? To wllh ta kiyayeni bani da kyau, idan ta ci gaba da shiga gonata sai na sa ta bi duniya ni ba imani ne dani ba al-qur'an, su Ramlah yan iyayi da suka ga xa su iya riketa su ci gaba da riketa din, amma duk ranan da gidadancinta ya fada mata karya ya kaita gidanka to kuwa ranan xata yi da ta sanin haifota da matsiyatan iyayenta suka yi" mikewa Abuturrab yyi ya nufi kofa Aunty tace "Gidan ubanwa xaka ina magana Aliyu?? Aliyu ba da kai nake ba??" bude kofar yayi ya fice ya bar masu a bude ko kullewa bai yi ba, Aunty ta bi sa da kallo baki bude har ya fita kofar parlor gaba daya. Abuturrab na fita bangaren Ummi ya koma, Ummi na kallonsa tace "Kaje ka bata hakurin?" Kasa ce mata komai yayi saboda yanda xuciyarsa ke tafarfasa, Ummi ta lura da yanayinsa ta ci gaba da aikinta da take yi kawai, bayan kusan minti uku yace "Ummi ki kira Aneesah kice ta sameni a mota, idan kuwa bata fito ba xan yi wucewata" Ummi tace "Ka kira uwar dakin taka ka gaya mata mana, ba ita tafi kusa da Aneesar ba, sannan ina ce ma a bangarenta take" Abuturrab ya mike yace "Next weekend idan na dawo xan xo in dauketa in sha Allah, sai da safe" daga haka ya nufi kofa Ummi tace "Aliyu" tsayawa yayi, sai kuma ya juyo tace "Tell me what happened" Yace "Ummi kawai ni bana son abinda Aunty take yi ina raga mata ne kawai saboda Abba but idan ta ci gaba da shiga gonata i can go to d extent i am not suppose to, she is getting me pissed off" Ummi ta rike ha6a tana kallonsa da mamaki a ranta kuwa cewa tayi yau kuma?? Can ta d'an yi murmushi tace "Toh me ya hadaka da uwar dakin taka, dama ana jin kanku ashe" Abuturrab yace "She should just stay away from my personal life nd issues, that's all, xan jira a mota ki kira ki gaya masu idan kuma bata fito ba wucewata xanyi, sai da
Chapter 167 · 0% Book details