Sashe 107
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abuturrab bai ce komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa, Jiddah ta sunkuyar da kanta jin bai amsa ba, Umma tace "Amma you are getting much better now" Ya kalli Umma yace "Alhmdlh" Tace "Toh Allah ya kara afuwa..." Mikewa tayi tace "Allah ya sauwake" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ameen" Kofa ta nufa Jiddah ta bi ta da kallo sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, bata san sanda ta mike ba tana son fita dakin taji muryarsa a tsakiyar kanta, "Dauko min ruwan gora a kitchen" Kallonsa tayi don ta tabbatar da ita yake, ganin shi ma kallon nata yake tace "Toh" sannan ta juya ta fita dakin, Ya kalli su Maimoon da ke kallon tv dake aiki a dakin yace "Toh nagode" Kallonsa suka yi a tare da sauri, Maimoon ta wara ido tana kokarin mikewa tace "Allah ya sauwake Yaya" Yace "Ameen" Safiyya tace "Allah ya kara lafiya" a tare suka fita daga dakin suka kullo masa kofar, bayan few minutes Aunty ta shigo dakin rike da goran ruwa ta ajiye masa kan bedside drawer, ya dinga kallonta, can dai yace "Ke kika dauko da kanki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ehh, na sa ta wanke kwanukan da aka 6ata a kitchen din" Bai ce komai ba, ta dau magungunansa ta shiga buda masa yace "Aunty...." Ta dakatar da shi tace "Ehh ka hadiyesu yanxu" Bai kuma ce mata komai ba, ta mika masa tulin drugs din, ya sa hannu ya amsa, ta dau goran ruwan ta bude shi ma ta mika masa ya amsa ya hadiye maganin, kallon bowl din hannunsa tayi ganin ba wani shan pepper soup din yake ba tace "Bani in tafi da shi gun wanke wanke, dama nasan baxa ka sha ba ai" Ya girgixa kai da sauri yace "Aa gashi nan ina sha" Tace "To Allah ya sa" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Ahmad ne ya shigo dakin yana dubansa yace "How are you feeling now?" Abuturrab yace "I'm good" Ahmad ya karasa dakin yace "Allah ya kara lafiya" Ba tare da ya kallesa ba yace "Ameen" Ahmad yace "Bari in je masallaci in dawo" Daga haka ya fita. Bayan fitarsa da few minutes Abuturrab ya cire drip din hannunsa ya mike ya dau bowl din pepper soup da Aunty ta kawo masa ya bude kofa ya fita, sau daya ya saci kallon mutanen dake xaune parlor ya wuce kitchen, muryar Aunty yaji tace "Ina kuma xa ka" Ya ki juyowa balle ya tsaya, ta mike ta bi bayansa Umma ta bi ta da wani irin kallo, yana shiga kitchen din ya rufe kofar, Jiddah dake tsaye tana wanke wanke ta juyo tana kallonsa, sae ga Aunty ta shigo, amshe bowl din tayi tace "To sae ka wani fito? ko a waya baxa ka kirani ba in shigo in dauka" kallonta kawai yake, ta ajiye bowl din a gefen Jiddah tace "Mu je" Bai ce komai ba ya juya ya nufi kofa Jiddah ta bi su da kallo, sae da ya fita sannan Aunty ta fita ita ma ta kulle kofar... Umma na kallon Abuturrab tace "Do u need anything" ya kalli direction din parlon ganin Ummi na parlon ita ma, ya karasa can, Aunty tace "Wai kawai mutum ya fige drip da aka saka masa yayi ta yawo cikin gida, ta ya xa a gane treatment din da ake" Abuturrab na karasowa parlon ya xauna yana kallon Ummi a hankali yace "Ina yini Ummi" Ummi tace "Lafiya qlau" Bai kuma cewa komai ba kamar yanda ita ma tayi shiru, Aunty tace "Don Allah ka taso mu tafi ka maida ruwan nan da ka cire" Umma ta mike tace "Wai ke Hafsah wannan shisshigin da neman wajen xama da kike duk na menene ban gane ba? Ina ruwanki da wani drip da aka sa masa, ko ke kika sa masa?" Aunty ta bude baki ta rike ha6a tace "Shisshigi kuma Hajiya Ramlah? Ban gane Shisshigi ba" Umma tace "Sai ki je ki xauna kiyi naxari ki gane da kyau, duk kin bi kinyi kane kane a kan abinda bai shafeki ba a gidan nan, ke kin isa ki hanasa xuwa ya gaida mahaifiyarsa, wacece ke...." Katseta Aunty tayi tace "Aa kinga ni baxan biye maki ba Ramlah dama kina da wani kuduri can da ban sani ba a kaina dake cikin ranki, banda haka ina ruwanki da issue din gidan nan, ita mahaifiyar tasa ai ta san da cewa ya dawo bashi da lafiya amma ko bin ta kansa ta yi, Aa gaskiya ni ba ruwana baxa ayi tashin hankali da ni ba" Hajja ce ta leko daga dakinta tace "Me ke faruwa ne nake jin hayaniya ga dai mara lafiya kwance shememe a gida?" Aunty ta kalli Hajja tace "Kawai dai daga Aliyu ba shi da lafiya ina tsaye kansa sai Hajiya Ramlah ta xo tana gatsa min magana, da yau ace bani da 'ya yan nan da nayi kwanan takaici a gidan nan..." Hajja ta fito tayi kasa da murya tace "Atoh ae da gaskiyarta Hafsah, kin bi kinyi bake bake kan d'an mutane kamar ke kika haifosa duniya, duk shekaruna a Masar ban ta6a ganin haka ba wllh, don cewa ma xa suyi kin masa wani mugun abun ne, su basa haka abinda ya shafesu kawai suke, da ran Hauwa fa ba mutuwa tayi ba Hafsah, to ina ruwanki da d'an mutane" Aunty tayi wani murmushi tace "Toh ai shkkn, su ma sai su ja sa jiki kamar yanda nake masa su ga ko baxai yi masu biyayyan da yake min ba, ai ko dabba ma yasan me kyautata masa" Bata jira cewarsu ba ta bar wajen, Hajja tace "Kaji mayya, wani jikin xa mu ja sa bayan mu dai bamu san abinda kika masa ba har yau, yin abubuwansa kawai yake irin na en benue fah, da a masar ne idan hukuma basu garkameki ba shegiya nake, don ai ba a san abinda kika masa ba yake makale da ke" Shi dai Abuturrab kansa na kasa, Umma tace "Xan ga yau ko ita ta haifesa, bari Ahmad ya shigo su tafi can gida ya ci gaba da treatment dinsa idan ta isa ta wanke kafa taje gidana taga tsiya" Abuturrab ya daga kai ya kalli Umma, Hajja tace "Shikenan bakinmu alekum, ni ma sai in tafi da kayana kala hudu duk mu tafi can idan ta isa ta bi mu, wllh sai na nuna mata ni yar banxa ce" su Maimoon dai sai dariya suke kasa kasa, Ita dai Ummi girgixa kafa kawai take, Hajja tace "Abinda duk mun san kan iskanci mu da muka xauna a Masar..." tana fadin haka ta shiga daki ta hau hada kayanta, Ahmad na shigowa kuma Umma ta sanar masa can gidan xa su tafi tare da Abuturrab, sosai Ahmad yayi mamakib musun da Abuturrab bai yi ba, shi da yafi kowa sanin halinsa tafiya ayi masa treatment a can gidan isn't something easy amma sai gashi yaga bai ce komai ba, Hajja dai tuni ta hada kayanta ta fito da yar jaka tace "Wannan dai sai dai muyi mota biyu idan ana son mu tafi cikin walwala" Ahmad yace "Har ke xa aje Hajja" Hajja ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Dadina da Masar wllh Yaro bai isa ya raina babba ba, wani ta6aran ai sai a Najeriya, wai ku ji fa wata tambaya da Ahmad ko wa yake ke min, to ina ruwanka fisabilillahi, gidanka ko gidan Hajiya Ramlah, tun fa da mahaifinku ya rasu ita ke ta fadi tashi na ganin shegun danginsa basu kwace katon gidan nan da ku ke ciki ba, mace me kamar maxa kenan fa Ramlah, duk sai da ta bi ta kwatar ma kanta yanci shi yasa ban ga laifin kibar da ta narka ba wllh, gidajensa biyu da motoci da ya bari duk bata amince an cuceta ba, kun ga inda ta fi Hauwa kenan, tunda ita gashi ma mijin ba mutuwa yayi ba amma er benue ta kwace gida da 'ya ya tana xaune sandandan, ba a san gawar fari ba amma yau ace Usman rai yayi hali ko tsinke da kyar Hauwa ta tsira da shi a gidan nan, balle dama tsawon rai garesa idan Allah ya amince, toh kuma yaro sai ka wani ce da ni xa aje sai kace xanje gidanka, shi sa tunda ku ka yi aurenku da Ramlah sau biyar naje gidan don kada in ja ma kaina raini" Tana kai wa nan ta kalli Umma tace "Wani motar xa mu shiga Ramlah" Umma ta mike tace "Ku je a na Ahmad, ni sai in ja motar Yaya tunda driver baya nan" Hajja tace "Aa gwara in shiga naki mu tafi a nutse, su kuma yaran su shiga motar Ahmad din" tana kai wa nan ta fita gun mota, Ahmad ya bi bayanta yana murmushi don xuwa ya bude mata motar sannan ya dawo duba Ramlah, Umma ta mike tana kallon Ummi tace "Xa mu tafi can gidan yaya" Ummi tace "Toh Allah ya sawwake" Umma tace "Ramlah fa?" Ummi tace "Tana daki tana bacci" Umma tace "Toh bari dai in dubata" daga haka ta wuce bangaren Ummi, Abuturrab ya mike ba tare da ya yarda ya kalleta ba yayi hanyar bangaren stepmom dinsa, da gefen ido Ummi ta bi sa da kallo. Jiddah ta fito kitchen bayan ta gama wanke tulin kwanukan da Aunty ta ajiye mata, Ummi na kallonta tace "Sannu da aiki" Jiddah tayi murmushi ta karaso parlon tace "Umma fa" Ummi tace "Ta shiga daki yanxu" Jiddah bata ce komai ba ta xauna kasa, Ummi tace "Xauna saman kujera mana" Murmushi kawai tayi ta ki tashi, bayan some minutes Umma ta fito daga bangaren Ummi, tana kallon Jiddah tace "Ki je ku gaisa da Ramlah tana tambayarki" Tace "Toh" sannan ta mike ta wuce part din Ummi, Ramlah na xaune saman kujera tayi murmushi ganin Jiddah tace "Sannu da xuwa" Jiddah ta mayar mata murmushin tace "Ya jikin?" Ramlah tace "Da sauki, ya su Maman Abdallah" Jiddah tace "Suna gida" Ramlah tace "Toh ki gaida min su" Jiddah tace "Xa