Sashe 138
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sauka ta bi sa da ido ya shiga driver seat ya tada motar ya bar layin, a hanya aka yi ta kiran wayarsa, ya daga daga karshe, calmly yace "Kun ga Ahmad ni ba yaro bane da xa a wani jera dani kafin in shiga gidana, this isn't my first marriage, my first marriage ma babu wanda yayi min haka, i went home my self, don haka duk sanda nayi niyyar shiga gida xan shiga, yanxu ina wani sabgar ne..." Ahmad yace "Ohh really?" Abuturrab yace "Yes Ahmad, bana anguwan ma ni" Ahmad yace "To idan kaje gidan sai ka sallami kawayenta..." Abuturrab yace "Sun wahala in dai sallamata suke jira... xa mu yi magana good night" daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gidan Umma yayi parking ya kashe motar, Jiddah da taji wani relieve ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace "Sai da safe" Daga haka ta shiga gate din gidan ya bi ta da kallo. Gidansa ya wuce daga nan, Aneesah da kawayenta na daki banda complain babu abinda take, Fauziyya tace "Nima ban ta6a ganin haka ba wai kannin ango su wani xo gidan amarya suce xa su kwana ranan da aka kawota, wllh sai kinyi da gaske wajen tattaro hankalin mijinki gaba daya gareki ya share kowa ya daina ganin kowa sai ke, don wnn dangin nasa baxa su bari kiji dadin rayuwar aurenku ba" Aneesah tace "Baxa su bari in ji dadin rayuwar aurena ba??" Wani dariya tayi tace "Lokacin da shigowa gidan nan xae fara gagaransu xan kira in sanar maku, ni fa Captain da ku ke gani nawa ne ni kadai wllh, haka plan din yake dama" Naja tace "Atoh, dama wa xai xauna ya xuba ido, barin ma miji irin naki, wllh kar kiyi sanya Aneesah... Kowa tashi tsaye yake" Aneesah tace "Ni nasan bani da matsala da yan mata tunda nasan wanene captain, nasan root din matsalata a aurenmu kuma magancesa ba wani big deal bane wllh" Jin an bude kofar parlon duk suka yi tsit, Maimoon ta shigo cikin dakin tana wani cika tana batsewa tana kallonsu Fauziyya tace "Ya Aliyu yace idan kun gama xaman ku fito xa a maida ku can gida" Aneesah ta cire gyalen kanta da sauri tace "A maida su gida?? Budar kan fa??" Maimoon bata ko kalleta ba ta juya ta fice, Mikewa Aneesah tayi ta fice daga dakin bayan ta daura mayafi a kanta ta sauko downstairs, tsaye ta gansa a parlor, da mamaki tace "My Captain kace xa a maida su Fauziyya gida? As in how?" Yace "Ehh" ta daure fuska tace "Toh wai budan kan fa?" Calmly yace "Duk budewar nan da kika yi ma kan bai yi ba sai wani special one kike jira" Da mamaki take kallonsa, yace "Pls Aneesah I'm tired and i need rest now... idan xa su sakko in ajiyesu tare da su Maimoon su sakko, or i leave the house duk sanda suka tafi in dawo" Kallonsa kawai Aneesah take, sai ga su Maimoon da Aisha da Nafisa ko warce da jakarta a hannu tana cika tana batsewa suka sakko suka ma Aneesah sai da safe suka fita waje, juyawa yayi ya bi bayansu, ya fi minti goma xaune a mota yana jiran fitowar kawayen Aneesah uku amma shiru shiru, su Maimoon dai na xaune bayan mota, daga karshe ya tada motar ya maida su gida, ko sai da safen kirki Maimoon bata yi masa ba ta shige gate tare da su Aisha, sai a sannan tace "Da nace masa xamu kwana fa daxu bai ce komai ba don har cewa yayi in kai ma Jiddah wayar ita ma ta dawo ta kwana I don't know what made him Change his mind all of a sudden" Aisha dai sai ta6a bake take tace "To ba gashi dai mun dawo gidan ubanmu ba" Direct hotel Abuturrab ya wuce yyi lodging daki, sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kashe wayarsa. Har karfe biyun dare Aneesah bata yi bacci ba, bata ta6a xaton haka nata first night din xai kasance ba, yanxu duk abubuwan da aka ce tayi a wannan daren baxata yi ba kenan ya tashi a banxa, gashi tayi ta kiran layukansa duk a kashe, dama rashin mutuncin Aliyu ya kai haka bata sani ba, lallai kamar yanda aka ce mata xama ba nata bane, xaman kuwa ba nata bane, she needs to bring down Aliyu to d level she wants him to be for her, kawayenta uku na kwance saman gadon sun yi bacci abunsu hankali kwance, mikewa xaune tayi daga karshe ta fita parlor ta xauna tayi tagumi, duk irin burikan da ta ci ma daren nan ya tashi a banxa kenan?? a takaice sai wajen karfe hudu bacci barawo ya sace Aneesah, Washegari da safe aka kawo abinci daga can gidansu Abuturrab, Fauziyya ce ta bude kofar parlon ta amshi abincin a hannun su Safiyya ta kai masu can sama, bayan sun hada shayi me kauri ga uban kwai da dankali a gabansu Fauziyya tace "Wllh ki nuna ma Captain din nan bacin ranki, wacce amarya ce aka ta6a yi ma wnn walakancin da yayi maki, ni ko a tarihi wllh ban ta6a jin haka ba, kar ki kuskura ki amince masa duk dadin bakinsa sai kin gwara kansa shi ma kin rama... Wannan ai walakanci ne wllh, duk wani ango na xumudi a ranan da aka kai masa amarya amma banda naki angon...." Aneesah dai bata cewa komai amma gaba daya ranta a dagule yake, daga karshe ta mike ta dau wayarta ta fita, wani dakin ta shiga ta kulle ta yi dialing number Aunty, yana fara ringing Aunty ta daga tace "Amarya bakya laifi, har kun tashi? Fatan dai komai normal?" Aneesah ta fashe da kuka, Aunty ta xaro ido ta mike tsaye ta fita daga dakinta don akwai wasu baki, murya can kasa tace "Lafiya Aneesah me ya faru? Da matsala ne?" Cikin kuka Aneesah ta shiga ba Aunty labarin abinda Abuturrab yayi jiya, Aunty ta saki baki har Aneesah ta kai aya, can tace "Abinda ya maku kenan Aliyun?" Cikin kuka Aneesah tace "Wllh kuwa Aunty, ni da babu kawayena ma da baxan ji wnn kunyan da nake ji ba ynxu, duk fa sun san komai kar suje su yada ni a Abuja, har cewa suke ko a tarihi basu ta6a jin amaryar da aka yi ma wnn rashin mutuncin ba" Aunty da ranta ya dau tafarfasa tace "Shikenan, share hawayenki Aneesah, xan kiraki nan da anjima kadan, kiyi hakuri ko su Mumy kar ki sanar ma kinji!" Aneesah na shessheka tace "Toh" daga haka Aunty ta katse wayar tana wani huci ta hau dialing number Abuturrab taji a katse, rike baki tayi tana naxarin walakancin da xata masa, can tayi wani murmushi hade da kwafa ta koma daki xuciyarta na ci gaba da 6ararraka.... Karfe tara da yan mintuna Jiddah ta fito daga dakinsu sanye da kayan bacci dogo har kasa sai hula a kanta xata shiga kitchen, ita kadai ce a gidan sai Umma da Aunty Nafisah, su ma kuma basu tashi ba, Huraira na can gidansu Ummi bata dawo ba sbda aiki, tun asuba ta tashi ta gyara gidan gaba daya tayi wanke wanke ta share har balcony, ta tafasa ruwan Lipton da ta cika ma kayan kamshi ta juye a flask snn ta koma daki wajen karfe takwas amma bata yi bacci ba, yanxun ma yunwan da take ji ya sa ta fito xata hada shayi, bude kofar parlon taji anyi ta juya da sauri don tun da ta share waje ta shigo bata kulle kofar ba, da d'an mamaki take kallonsa, ya shigo parlon ya kulle kofar, sai da taga ya karaso cikin parlon ya xauna snn ta duka nan kasan carpet tana kallonsa tace "Ina kwana" har lkcn kayan jiya ne a jikinsa, ta mike don bata san ko ya amsa gaisuwar ko bai amsa ba ta koma daki ta saka hijab dinta snn ta fito ta wuce kitchen, mamakin abinda ya kawosa da sassafe ta dinga yi, ta dai hada shayi ta dau bread slice uku a kan glass plate snn ta fito har xata wuce dakinsu ta juyo taga kallonta yake, ta d'an tsaya tace "Xa a kawo maka shayi ne? Su Umma basu tashi ba" Maimakon ya bata amsa sai taga ya tashi yayi hanyar dakin Ahmad, ita kuma ta wuce dakinsu ta kulle kofar. Aunty ta rasa me ke mata dadi, ta rasa wanda xata kira tace ga abinda Abuturrab yayi, gashi El-Basheer ma wayarsa a kashe, to ko dai suna tare ne, ita Ahmad ba shiri take da shi ba balle ta kirasa, can dai daga karshe ganin har kusan goma wayar Abuturrab a kashe Kuma bata son Aneesah ta kira mutan gidansu tace xata sanar masu yasa ta yanke shawaran kiran Ahmad, luckily nasa ya shiga, sai da ya kusa katsewa Ahmad ya mike xaune daga kwancen da yake ya dau wayar mamaki ya kamasa ganin wai Aunty ke kiransa ya daga ya kai kunne, Aunty tace "Ahmad ya gajiya?" Yace "Ina kwana?" Tace "Lafiya lau, Aliyu fa?" Ahmad yace "Aliyu kuma? Ba yana can gidansa ba" Aunty tace "Bai can, kuma ba can ya kwana ba" Bude baki Ahmad yayi, Aunty tace "Kar ka min karya Ahmad, yanxu da gaske bakwa tare?" Ahmad yace "Wllh ni ina gidana, jiya tun karfe takwas muka rabu da shi ina jin" Aunty tace "Toh Shikenan" daga haka ta katse wayar, Ramlah dake gefensa ta kallesa tace "Me ya Aliyun yayi" Ahmad ya daga kafada yace "Ban san meke damunsa ba, wai bai kwana gidansa ba jiya" Ramlah ta xaro ido tace "Aneesar fa?" Ahmad yace "Tana can gidan i guess" Ramlah ta ma rasa abun cewa, Ahmad yace "Ko aurensa na farko da yaje yayi bai k'i kwana a gidan ba ranan da suka tare balle wannan" Ramlah tace "Toh ko dai Aneesan sun masa wani abu ne" Ahmad yyi dariya bai ce komai ba yana kokarin kiran layin Abuturrab shi ma ya ji a kashe. Karfe goma Jiddah ta fito ta ajiye cup da ta sha shayi a kitchen sannan ta dau wani cup din ta hada wani shayin, ta