← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 205

Sashe 168

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 4 min read

safe" Daga haka ya fice daga dakin Ummi ta bi sa da kallo, daukar wayarta tayi ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace "Hafsah ki turo min Aneesah" Aunty ta wani kyabe baki tace "Aneesah kuma?" Ummi tayi shiru bata ce komai ba, Can Aunty tace "Toh dama sallah take bari ta idar" Ummi ta katse wayarta, sai bayan minti shidda Aneesah ta shigo parlon Ummi ta xauna saman kujera ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Ki je ki saka hijab dinki ki dau jakarki mijinki na jiranki a mota, sai kuma ayi ta hakuri, shi dama xaman aure d'an hakuri ne, kowa hakuri yake, ke kuma sai ki gyara duk abinda baya so, shima xai gyara in sha Allah, Hajja kuma ba lallai xaki sake ganinta a gidan ba ma, kiyi hakuri ki bi mijinki ku tafi kin ji" Aneesah tayi kasa da kanta, bayan wani d'an lokaci tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kofa, Ummi ta bi ta da kallo har ta fita, tana komawa ta sanar ma Aunty yanda suka yi da Ummi tana tabe baki, Aunty ta ja wani dogon tsaki tace "Toh baxa ki je ba wllh, ita a wa xata tsomo baki cikin lamarin nan? Ina ruwanta! A cikin kayan miya wacece ita a lamarin Aliyu??" Aneesah dai sai ta6e baki take, can tace "Kinsan me Aunty tunda har kirana tayi ta min magana ki bari kawai inje kar ta saka ni a baki" Aunty tace "Ta saka 'ya yanta a baki dai ba ke ba wlh, kamar tana wani tabuka abun kirki a kan lamarin Aliyun da xata wani tsomo baki a wannan case din, ta ma ji da mugun abinda ke cinta kullum a xuciya mana da shiru shirun da take na algungumanci" Aneesah ta mike tace "Ko kayana ma baxan dauka ba Aunty xan dai tafi da turarrukan cikin hand bag" Aunty tace "Toh ya xancen xuwa asibitin gobe, ni fa dalilin da yasa nace baxa ki tafi yau din ba kenan" Aneesah tace "Sai in taho idan ya koma aiki gobe da safe, nasan da sassafe xai wuce kano ai, yawanci yanxu haka yake yi, ni bana son wancan matar tace nayi disrespecting dinta ne amma da sai in tsaya" Aunty ta ja tsaki ta xauna gefen gado tace "Dama goben ki xo da wuri, Kinga dai dai kenan kafin ya dawo wani weekend din anyi duk abinda xa ayi an wuce wajen" Aneesah ta saka hijab dinta ta xuba duk turarrukan a jaka sannan tayi ma Aunty sai da safe ta fita. Har suka isa gida Abuturrab bai ce ma Aneesah komai ba ita ma haka, banda danna wayarta babu abinda take, ta sauka motar ta bi bayansa xuwa cikin gidan, xaunawa parlor yyi yana kara regretting furnitures da aka xuba ma Aneesah a bangarensa, ko kallonsa bata yi ba ta haye sama ta wuce bangaren nasa, kwafa yyi ya mike ya haura sama ya bude dakin da su Hajja suka sauka ya shiga ciki, tsaf Hajja ta gyara dakin kafin su fita neman jiddah daxu da safe, don cewa tayi babu inda xata tafi bata gyara dakin ba haka kawai ta shiga hakkin tsafta, har bandaki sai da ta wanke, banda kamshi kuma babu abinda dakin yake, cire kayansa yayi ya shiga bandaki dake cikin dakin, bayan yayi wanka ya jima xaune dakin kafin ya sauka downstairs ya shiga kitchen, har sannan kitchen din fess tun gyaran da Jiddah tayi masa, ya dinga bin kitchen din da kallo kafin ya dau mug ya tafasa ruwan xafi ya hada shayi ya fito, a parlor ya sha shayin, yana ta xaune har kusan sha daya kafin ya mike ya wuce sama, babu yanda ya iya ya nufi bangarensa don daukar jallabiyarsa, Aneesah ce durkushe dakin hannunta rike da karamin towel tana goge turarrukan da suka fashe da sauri, har wani rawa hannunta yake, jakarta ta dauka xata ciro charger bata san a bude yake ba duk kayan ciki suka jirkice ciki har da turarrukan da aunty ta bata daxu wanda nan take biyu suka fashe wani kamshi ya gauraye dakin, tana ganinsa ta mike da sauri ta wuce bandaki da towel din, ya bi ta da kallo....
Chapter 168 · 0% Book details