Sashe 159
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lkci daya Abuturrab ya saketa ta dalilin hasken wuta da ya dawo kitchen din, ta rufe bakinta a rikice ta juya ta bude kofar kitchen din ta fice da gudu, Aneesah na tsaye parlor bayan ta kunna solan gidan, ta bi jiddah da kallon mamaki barin yanda taga ta rufe bakinta da hannu har ta wuce sama, can ta kalli kofar kitchen din, sai kuma ta tafi can da sauri ta tura kofar xata shiga suka kusa cin karo da Abuturrab xai fito, ya d'an buda ido kafin yace komai ya juya mata baya, walking toward the gas yace "Na xata kinyi bacci ai...." Daga sama har kasa ta dinga kallonsa, yana tsaye gaban gas din bai yarda ya juyo ba tace "Me kake yi a kitchen Captain?" Yace "Gyaran kitchen din da kika bari kaca kaca" Sai a sannan ta bi kitchen din da kallo taga sai walkiya yake, ko ina yayi fess, sake kallonsa tayi tace "Who just left the kitchen now?" Ya dau lighter kamar xai kunna gas din yace "The person that helped in transforming the kitchen back to it normal sef..." Tace "To wannan juya min bayan da kake na meye haka?" Wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke ya daga wayarsa da ya fara ring duk da Ahmad ne ke kiransa ya kai kunne still backing her, Aneesah ta gaji da tsayuwarta ganin ba gama wayar xai yi ba gashi yayi backing dinta ta juya ta fice daga kitchen din, sai a snn ya d'an waiga, ya dau mug ya bude flask ya xuba ruwan xafi ya saka Lipton, sannan ya dau lime din da yake siyowa a kitchen din ya yanka uku yayi squeezing a ruwan lipton din... Hajja ce tsaye kan Jiddah dake xaune kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, rai bace Hajja tace "Naga abinda ya fi karfina ni Dije, yanxu baxa ki bude baki ki gaya min me aka maki ba in san ta inda xan fara, matar gidan ce ta maki wani abun koko?" Jiddah taki dagowa hawaye sai sauka idonta yake duk jikinta yayi sanyi, Hajja bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin ta tafi can bangaren Abuturrab, da karfi ta kwankwasa kofar, Aneesah dake xaune saman kujera a parlon tana kokarin dialing number Aunty ta kalli kofar, jin an sake kwankwasa kofar kamar xa a cire ta mike a d'an fusace tace "Wai waye wannan" Tura kofar parlon Hajja tayi ta shigo ciki, tana huci tace "Ni dai kafin ince komai ina son sanin waye mai gidan nan tukun??" Aneesah tace "Haba dai.. ai ba girmanki bane shigowa wannan bangaren Hajja, duk abinda kike so da sai ki jira a fito....." Wani xagi Hajja ta mulmula mata tace "Ke har kin isa ki gaya min yanda xanyi a gidan jikana? Kaji min yar banxa, Ashe dama bayan bak'ar kazanta har da rashin kunya da fitsara kika iya ban sani ba? To wllh na fasa komawa wannan gantalallen Masar din dai tunda ba uban da na hada dasu, ina nan kasata Najeriya sai na nemo ma jikana auren tsaleliyar mata me bama tsafta hakkinsa, yar gayu me kamshi xan samar masa ba irinki kazama me wari ba, mata daga aure ko wata biyu ba ayi ba kin hallakar min gidan jika da kazanta ko ina banda tsutsa babu abinda yake fita, ko irin kamshin turaren nan na amare gidan nan bai samu gatan yi ba, to tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin mace kazama aminiyar dauda irin ki ba, amma duk ba wannan ya dameni ba, ya xan sa yarinya karama wanda kika kusa haifa ta tsaftace kitchen din da kika halaka yake fitar da tsutsa kuma ki saka min ita kuka babu gaira babu dalili??" Aneesah dai na tsaye sai kallon Hajja take baki bude with shock, Hajja tace "Ba kya kalleni kamar shashasha ba dama, wllh dole in nemar ma Aliyu mata me tsafta da son kamshi dai dai shi, ina ta kallonsa ganin ya d'an rame ashe kaxantar ki ne ke tsotse mana shi, to Allah ya isa wllh, mu kaf xuri'armu babu kazami...." A fusace Aneesah ta nufi kofa ta fice fuuuu, Hajja tace "Uwar kazaman Najeriya kawai, mata haka kazama na bugawa a jarida, dubi farin kafet din parlon nan fisabilillahi yanda ya fara fita hayyacinsa, parlon ma naji kamar karni yake wllh, ko da yake dai ba ruwana bari inyi shiru, ba abinda Usman ya aikoni inyi a gidan nan ba kenan, amma da yau kinji maganganu a kan kazantarki wllh" Aneesah na sauka downstairs ta tadda Abuturrab xaune ya gama shanye cup din Lipton da ya hada, tana shigowa parlon ta rushe masa da matsanancin kuka tace "Aliyu dama grandmum dinka xuwa tayi ta ci mun mutunci ta ci xarafina har gidana? Dama haka kuke ban sani ba?" Kallonta ya dinga yi don bai san me ya faru ba, sai ga Hajja tana sakkowa tana cewa "Wllh kinci albarkacin ba abinda Usman yace in xo inyi a gidan nan ba kenan, amma yau da na maki bankada iri iri, kuma gida muna nan babu yanda kika iya da mu tunda ba wani ya haifo min Usman din ba har Allah ya basa Aliyun" Da mamaki Abuturrab ke kallon Hajja yace "Me ya faru Hajja?" Tace "Me kuwa baxai faru ba Aliyu, daga na tura Jiddah ta farfado da kitchen din da ta fara hallakarwa kawai sai ta saka min ita kuka na rasa abinda tayi mata, yanxu haka yarinyar na can tana rusa kuka ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kuma taki gaya min menene, da kyar fa Ramlah ta amince ta biyoni, yanxu in maida mata yarinya idanuwa a kumbure me kake tunanin xai biyo baya matar da ba mutunci gareta ba kowa ya san da haka..." Abuturrab ya d'an saci kallon Aneesah, lkci daya ta sake fashewa da kuka tace "Wllh baxan kwana gidanka ba yau Aliyu, ni ai bansan bayan duk hakurin xama da nake da kai a yanda kake akwai wani kalubalen dake tunkaroni ba...." Tana fadin haka ta wuce sama kamar xata tashi sama, Hajja tace "Oho dai Allah ya ishi Jiddah, kai kuma kayi ta istigifari don wnn ba karamin laifi ka aikata ma mahaliccinka ba ya jarabe ka da mata kazama, ni wllh kawai nayi shiru ne amma tun daxu da na shigo parlon nan naji yana wari" Tana fadin haka ta juya ta koma sama, Abuturrab ya d'an yi murmushi, shi dai ya ki tashi har sannan, Aneesah na komawa sama ta saka kayanta ta dau kaya kala biyu a karamin akwatinta ta dau hand bag ta yafe gyalenta ta fito, tana saukowa downstairs bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi Kofa, ya bi ta da kallo yace "Ina xaki je Aneesah?" A mugun fusace tace "Wllh baxan kwana gidan nan da tsohuwar nan a ciki ba, baka ce min bayan hakurin da xanyi da kai har ita ma xanyi hakuri da ita ba, sannan ita wannan yar iskar mara asali da ta kawo min gida...." Dakatar da ita yayi yace "Tafi kije, Allah ya tsare" Bude baki tayi tana kallonsa, tace "Kace in tafi inje?" Fuska daure yace "Ehh, sai da safe" Kofa ta nufa fuu ta fice, ko kulle kofar bata yi ba ta nufi gate, ya mike ya karasa kofar ya kulle ya sa makulli. Hajja na komawa daki ta tadda Jiddah kwance ta takure waje daya, Hajja tace "Kiyi hakuri duk ni na ja maki don uwar rikon ki ma da kyar ta amince kika biyoni, ban san gidan er iska xa mu xo ba da ban fara xuwa da ke ba, amma kema wannan simi simin da kike baxai fissheki ba, gwara ki samu kiyi baki ki dinga kwatar kanki, naga kin cika wani sanyi kamar kankara, ai yanxu idan kace xaka yi sanyi sanyi a duniya kullum cikin cutarka ake, da kin gaggasa mata magana kin gaya mata irin kazantarta ai da ta kama kanta amma kin wani taho sama kina kuka kamar er yarinya, ni sai yanxu ma kika bani haushi wllh, da ba don Allah ya takaita aurenku da Aliyun ba ai kishiyarki fa xata xama, to a haka xa ki xauna kina mata kuka kullum??" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, har sannan xuciyarta bugawa yake, scene din abinda Abuturrab yayi mata ya ki daina dawo mata, ganin abun yake kamar afresh, Cike da damuwa Hajja tace "To ko dai wani mugun abun ta maki naga duk a firgice kike wllh, ki gaya min gaskiyar me ta maki Jiddah" Jiddah ta lumshe ido ta bude a karo na farko ta bude baki a hankali tace "Bata min komai ba" Hajja tace "Oho dai ita da Allah ni dai na gaya mata duk abinda ya kamata ta sani" Tana fadin haka ta sake fita daga dakin, Jiddah ta ji hawaye ya kawo idonta ta kai hannu bakinta da take jin kamar bai cire nasa ba har sannan, ita idan ba a tv ba bata ta6a sanin ana haka a reality ba ma, hancinta ta kai kayanta jin kamshin turarensa ya cikata, ta wani turo baki ta mike ta fara cire kayan, sai da ta cire tas sannan ta saka hijab ta kwanta tayi lamo saman gadon, scene din da bata so na sake dawo mata kamar a lkcn yake faruwa. Aneesah na xaune parlon kawarta Chef Salma, Salma tace "Kan bala'i!!! to ai ni duk a xancen ki babu abinda ya tsaya min irin yarinyar da kika ce ta biyo kakar tasa... Ita yar kauyen da ya saka ce ake miki sintirin xuwa gidan ki da ita? Sannan kuma ta bi ki da sharri haka? To me hakan ke nufi?" Aneesah ta fyace majina da handki din hannunta tace "Ai shine nake jiran kiran stepmom din tasa, wllh ni rabona da su gaba daya tun xuwansu da rana da nayi shigewata parlonsa, ban ganta ba balle har wani abu ya hadani da ita, amma ban san me taje ta gaya ma makirar tsohuwar ba ta shigo har bangaren mijina tayi min wankin babban bargo ta ci min mutunci" Salma tace "To kuma ai kinyi wauta barin gidan da kika yi, bar