← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 205

Sashe 14

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa, bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne, wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi Aunty" ta hade rai tace "Shine ni baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata, Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace "Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune, Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye, kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan, Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai maki sauki ba?" hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da xuwa Alhaji.... Ae da ta fito maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare" Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?" Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai" Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace "Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida, Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?" Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace "Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba" kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama da abincin
Chapter 14 · 0% Book details