← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 205

Sashe 11

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace "Tashi ki fita ki ban waje" Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace "Wllh baka gansa ba Captain, ni dai ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??" Abuturrab na cin Apple din hannunsa yace "Meye da shi wai Aunty?" Cike da takaici Aunty tace "Don dai sai da yamma ka dawo jiya da ka gane ma idonka...." Yace "Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma'ah, private jet muka biyo daga kano, sha biyu da rabi ina kaduna..." tace "To a ina ka tsaya sai bayan la'asar ka dawo gida?" Yace "Muna tare da wasu abokanmu" Aunty tace "Shi yasa, ai da ka gansa wllh... Muna xaune fa jiya da safe kamar abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma'ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana..." Abuturrab dake ta kallonta yace "Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu" Tace "Toh kaga Captain tun daga bakin titi da kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan arxiki, kana ganinsa dai kaga 'ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba" Abuturrab yyi murmushi ya kai Apple dinsa baki yace "Wani sana'a yake yi?" Wani kallo ta jefa masa tace "Sana'a, wa ke ta wani sana'arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus... The way u dress will be the way u will be addressed??" Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace "Wllh na sake ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki..." Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta...." Tace "Ameen sai ka kirata and talk sense into her head... Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba" Mikewa yayi, tayi saurin cewa "Captain ban kai ka kaje kaga filin da na siya ba ae" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" tace "Lahadin xaka koma aikin?" Yace "Idan Allah ya yarda" Tace "Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba..." Ya shafa kansa yace "Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi, wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week" Tace "Gashi ko ka xo kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba" yyi murmushi kawai, tace "Sai kaji an sa ranan Ahmad da Ramlatu" Yace "So Abba told me" Tace "Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya ku bayin garin nan, Ahmad ai d'an gayu ne d'an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan" Abuturrab ya nufi kofa yace "To Allah ya kyauta" Tace "Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?" Murmushi yyi yace "Allah ya kai mu lokaci" Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa, ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace "Don't tell me har kin sauka?" Tace "God!!! Nima Don't tell me baka fito ba Captain" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ban dade da shigowa gida ba... But in few mins time xan karaso I'm sorry" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa.... Tafiyar minti ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace "Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima...." Cike da shagwaba tace "Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu" Yace "Sai kika basu kenan" Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake driving din Aneesah dake gefensa tace "I learnt about Ahmad's engagement with Ramlah" idonsa na kan titi yace "So i heard also" Tayi kasa da murya tace "To mu kuma namu fa?" Still bai kalleta ba yace "Xa ayi" Tace "Yaushe??" yace "Am trying to put things in order first, i don't get why u are in a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace "Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata wuce shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki" Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da
Chapter 11 · 0% Book details