← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 205

Sashe 4

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace "Look... I don't want to say anything about that.... idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa" Matashin na taunar apple yace "It's already late, tayi bacci..." Abuturrab yace "It's late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?" El-Basheer yace "Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan" Abuturrab yace "In dai Friday ne ina nan in sha Allah" El-Basheer ya daga kafada yace "Ohk then" Abuturrab yace "Let me pick a call, sai da safe" El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace "The lady u don't want to talk about?" Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa "How u babe?" Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano.... Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja... Tsayinta matsakaici ne.... ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace "Why ain't you picking my call Captain?" Ya gyara xamansa yace "It wasn't long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?" A hankali tace "I'm fine, ya gajiya?" Yace "Alhmdllh, where are u coming from?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Home... kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito" ya shafa beard dinsa yace "Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks" Ta langwabar da kai tace "Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow...." Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace "To ina jin ki yanxu, I'm sorry i forgot about that" Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Ina jin ki Aneesah" Tayi kasa da murya tace "Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?" Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace "To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan" Ta girgixa kai tace "Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don't u love me ne Aliyu?" Abuturrab ya xaro ido yace "Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki.... kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo..." Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace "Aa ni da motana na fito don't worry" Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace "I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba" Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace "Thank you my Captain" ya kashe mata ido yace "C'mon babe.... Nikab din kuma na meye yau kika sa?" Tace "I just felt like" ya daga kafada yace "Alright sai mun yi waya" ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace "Aa Abuturrab sannu da xuwa" ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace "Ka dawo weekend kenan" yace "Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?" Tace "Alhmdllh na ji sauki yanxu" yace "Allah ya kara lfya" tace "Ameen" ledan hannunsa ya ajiye yace "Ahmad yace in taho maki da wannan" Tace "Kun hadu a Abujan kenan" Yace "Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka" Amira tayi 'yar dariya tace "Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa" Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace "Ni dai Allah ya tsare min shi" a hankali yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace "Ameen Umma" Tace "Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko" Abuturrab ya d'an buda ido, sae kuma da sauri yace "Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai" Tace "Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae" Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace "Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa" Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace "Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated" tace "Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance" Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace "Ko kana da inda xaka je ne?" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Aa, bari in je in dawo" tace "To Allah yyi maka albarka" da kyar ya amsa da "Ameeen" snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace "Kee" bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace "Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne" Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana'arta, Yarinyar daxu tace "Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara" Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace "Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?" Tace "Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida...." Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace "Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d'an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba...." daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d'an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace "Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba...." Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam... Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace "Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu" Sai a sannan ta kallesa tace "Toh ai sai an soya ko baka
Chapter 4 · 0% Book details