← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 205

Sashe 32

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 2 min read

murya yace "Abu me kyau kayi my son, and i am proud of you, Allah kadai ya san ladanka, kar ka damu it shall be well, Allah yayi maka albarka, and kada ka sake tunanin sakinta a ranka shine xai yi helping matters, ka xauna da ita tunda ka aureta, you won't regret it in sha Allah coz you've got a good heart, nasan wataran xaka yi alfahari da ita...." Da sauri Abuturrab ya dago ya kalli Abbansa da jajayen idonsa, ji yayi xaxxabi na neman kara rufesa, amma tunawa da yayi xai saketa ba tare da sanin kowa ba sai ya ji hankalinsa ya d'an kwanta, Abba yace "Xuwa yaushe xata tare din yanxu?" Abuturrab ya kalli Abbansa a sanyaye, Abba yace "Let me talk to ur mothers about it first, i hope they won't be disturb much..." Wayarsa ya dauka ya shiga kiran matan nasa, Abuturrab gabansa ya dinga faduwa don bai san yanda Umminsa da Aunty su kuma xa su dau lamarin nan ba, ba a dau lkci ba duk suka shigo, Abuturrab ya kalli Abbansa a hankali yace "Can i excuse my self sir..." Abba yace "Sure dear" Mikewa yayi ya nufi kofa walking slowly, Ummi ta bi sa da kallo, tun a shekaranjiya ta san abu na damunsa yana cin sa har cikin ransa, though tasan da kyar ya gaya mata koma meye da ya shafesa sai dai kishiyarta amma wannan karan ta lura ita din ma bai gaya ma ba, hakan yasa abun ya dameta sosai tun daga jiya bata da nutsuwa, don duk da baya gaya mata sabgarsa in dai xai gaya ma Auntyn da sauki, ko ba komai ita ma tana basa shawaran..... Aunty da ta bi sa da kallo tace "Alhaji ko ya gaya maka damuwarsa, tun safe nake fama da shi yace min ba komai, kuma nasan ba gaskiya bane, and this is so unlike him" Abba ya d'an sauke ajiyar xuciya yace "Kiran da nayi maku kenan yanxu" Duk suka maida hankali kan Abba don jin damuwar Abuturrab din.
Chapter 32 · 0% Book details