Sashe 191
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
su a cart din dai dai nan shi ma ya juyo rike da biscuits din da yake kallo suka kusa cin karo, juya masa baya tayi da sauri taji kamar ta nutse ta rufe ido, xata maida chocolates din taji ya fixgota, tayi narai narai da ido tana kallonsa da manyan idonta, ya amsa ya xuba su a cart din yana kallonta shi ma, ita ta fara sauke idonta, sauran siyayyan duk tana gefe har ya gama, suka tafi wajen biyan kudi, a booth duk aka xuba ledojin kayan siyayyan, eatry din mall din ya shiga ya siyi ice cream da pizza with shawarma sannan ya fito, ita dai tana tsaye bakin motarsa tana jiransa, bayan ya shiga ita ma shiga motar, cikin minti ashirin da biyar suka iso kofar gidan Ramlah. Jinginar da kansa yayi da kujeran motar ita dai jira kawai take taji ya bude lock din motar ta sauka, amma sai taga yaki budewa, bayan five minutes, taji muryarsa calmly yace "Xan mu fita Dubai gobe in sha Allah, from there xa mu tafi Uk..." Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya kalleta.... ta sunkuyar da kanta tace "Allah ya kiyaye" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Xan yi few months a can" Bata ce komai ba, yace "Kina da bukatar wani abu ne??" Ta girgixa masa kai tace "Wani abu kamar me bayan su Umma na yi min komai ni" Ya dinga kallonta yace "Wannan ne amsan tambayar da na maki?" Kin cewa komai tayi, yace "Bude baki kiyi min magana" Tace "Bana bukatar komai" shiru duk suka yi, ita dai wata magana ce ke cinta amma ta rasa ta ina xata fara masa, ji tayi yace "Do u have anything to say to me?" Ta kallesa da sauri, sai kuma tace "Ehh.." yace "Ina jin ki" cikin sanyin murya tace "Ranan Hajja tace wai kunje hayi an rusa gidanmu, ba kowa yanxu" Ya dinga kallonta yace "Sai aka yi yaya?" Ta fashe da kuka tace "Baabarmu da Bibalo fa?" Yace "Kina son xuwa wajensu ne yanxu??" Hawaye na sauka ido ta ta kallesa tace "Ehh ina so don Allah" Yace "Me xaki yi masu idan kinje" Cikin rawan murya tace "Ina son in gansu mana, saboda nayi kewarsu... Ban taso na gan ni da kowa ba sai su, and it's been long... Nayi kewarsu sosai" Tada motar yayi bai kuma ce mata komai ba yayi reverse suka bar layin. The journey was so silent, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso titin hayin rigasa, tunda suka shigo hayi Jiddah ta dinga bin anguwar tasu da kallo, ta rasa wani irin farin ciki xata yi a moment din, farin cikin nata bai bayyana a fili ba sai da ta gansu kan layin gidan Babaarta, ta kallesa da farin ciki amma ta rasa abinda xata ce masa, she looks so happy... shiga layin yyi da motarsa xuciyarta na bugawa tace "Don Allah ko xaka tsaya in fara shiga gidan Iyah in gaisheta???" Ya kalleta sannan yayi parking kofar gidan Iyah, sauka tayi daga motar da sauri ta shige gidan a guje, ya sauka ya jingina da motar tasa ya bi ta da kallo, Iyah na xaune tsakar gida da rediyonta a hannu, tana ma jikokinta dake kwance saman tabarma fifita sun yi bacci, Jiddah ta wara ido cike da murna tace "Iyah!!!" Fadawa jikinta tayi ta rungumeta, Iyah ta matsar da ita tana mata wani kallo daga sama har kasa, sai kuma tace "Jiddah????" Rungumeta Jiddahh ta kara yi lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "Nice Iyah, nayi kewarku wllh" Iyah ma ta fashe da kuka tace "Ashe rai kan ga rai Jiddah, ashe xan sake ganin ki a rayuwar nan?" Jiddah ta share idonta tana murmushi tace "Gashi kin gan ni Iyah" Iyah ta mike tsaye tana sake kare mata kallo don tabbatar da ita din ce kuwa, sai ta saki salati tace "Daga ina kike haka Jiddah?? Kece kika dawo haka kamar balarabiya Jiddah??" Jiddah tayi murmushi ta kasa ce mata komai tana kallonta, Iyah tace "Ke da waye yanxu haka? Daga ina kike?" Jiddah tace "Yana kofar gida, ince ya shigo?" Bata jira me Iyah xata ce ba ta tafi da sauri kofar gidan, har sannan Abuturrab na tsaye ya rungume hannunsa, tace "Wai tace ka shigo" kallonta ya dinga yi ta juya ta koma ciki da sauri, shafa kansa yyi ya bi bayanta... Har kasa Iyah ta durkusa tana gaishesa bayan ya shigo gidan, hakan yasa ya xauna saman darduma yana d'an murmushi calmly yace "Ina yini??" Iyah ta rushe da kuka tace "Wllh da kasan irin taimakon da Allah ya baka ikon yi da ladan da Allah xai baka da ba haka ba bawan Allah, ka taimaki rayuwar Jiddah a sanda take tsananin bukatar taimakon, ka cece Jiddah a dai dai lkcn da take bukatar ceto, Allah ubangiji ya sa ka samu me maka abinda kayi ma marainiyar Allahn nan duniya da lahira, Allah ya biyaka da aljanna, ya yalwata maka arxikin ka, Allah ya baka ikon ci gaba da riketa da amana, Allah kuma ya baku xaman lafiya tare na har abada ya bada xuri'a dayyaba" Kuka kawai Iyah take kamar jininta ce Jiddah, Jiddah dai duk jikinta yyi sanyi ta sunkuyar da kanta jin maganganun Iyah, shi ma kawai murmushin karfin hali yake yana kallon tsohuwar a hankali ya ce "Ameen nagode Mama" Iyah na kwalla tace "Wllh ki rikesa Jiddah, kaf duniya a yanxu dai baki da kamarsa, shine uwarki shine ubanki, ya maki abinda a cikin kashi dari na mutane baxa ki samu kashi biyu da xa su iya maki ba, ya fidda rayuwarki cikin kunci, maraici, tsanani, da bakar wahala, yayi maki duk wannan abun a lokacin da kike tsananin bukatarsu, to me xai janyo maki butulce masa a rayuwar nan, kiyi masa halacci yanda ya maki Jiddah, ga shi wai yau kece sai da na maki kallo kusan uku sannan na gane ki, ba don muryarki ba wlh baxan yarda ke din ce ba" Sosai jikin Jiddah yayi sanyi wanda bata san lkcn da hawaye ya dinga sauka idonta ba tana kallon Iyah, kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Iyah tace "Ki rikesa, kiyi masa biyayya, ki rike yan uwansa da duk wani nasa Jiddah, da abinda xaki iya biyansa kadai kenan ki ji in gaya maki, nace kiyi masa biyayya, wllh kiyi masa biyayya, Allah kadai yasan sadaukarwan da yayi sabida ke, Allah kuma ya baku xaman lafiya na har abada, nasan baku ma kai ga shiga gidan Hansai ba, amma idan xa ku ji ta nawa ba sai kun shiga ba kuyi tafiyarku kawai, Hansai bata canxa ba dai daga yanda kika santa... Sai ma dai abinda ya faru" Jiddah sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, Abuturrab ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye ma Iyah yace "Kiyi hakuri Mama babu yawa wannan, in sha Allah xan sake dawowa gaisheki, sannan xan daukeki in kai ki inda mu ke" Iyah tace "Wllh gaisuwan da kuka xo min ma ya isa ya wadatar ba sai ka bani kudi ba Yarona" mikewa yayi yana kallon jiddah da ta kasa daina kuka, a haka dai Iyah ta rakasu kofar gida tana cewa "Ba sai kun je gun Hansai ba, kuyi tafiyarku Allah yayi maku albarka ya baku xuri'a dayyaba..." Cikin sanyi Jiddah tace "Iyah baxan iya tafiya ban shiga na gaisheta ba" Iyah tace "Toh shkkn Jiddah, Allah ubangiji ya kareki daga duk sharrinta ku shiga kawai, akwai Allah" Abuturrab ma bai hana Jiddah ba suka karasa kofar gidan nasu da kafa, gabanta na faduwa ta shiga gidan ta ma kasa ko sallama saboda fargaba, Hansai na xaune tsakar gida tana fiffita ga kwanon abinci a gabanta tana cewa "Yo ba gwara ma ya mutun ba ko xa a rage mugun iri, duk fa da hadin bakinsa da uban kudi da aka dinga lafta masa aka siyar min da 'ya ban ji ba ban gani ba, yau wata dai dai kusan biyar kenan, kuma wllh gaya maki ne kawai banyi ba amma so nake na hada yan kudaden wankauna, na kai gidan malam Hamisu a sake danne tsinanne kada Allah ya mikar da shi, kaf bani da makiyi irinsa a duniya yanxu kam..." Zulai dake kwance tsakar gidan da daurin kirji tace "Ai ko dai ance yana can shika rai a hannun Allah baya gane duk wa enda ke kansa, aiki ma xa a masa sai kuma jikin ya dada sususcewa kinga bbu xancen aikin ai sai ya farfado kuma" Jiddah ta kasa shiga gidan gabanta sai faduwa yake ta dinga karanto addu'o'i a ranta, Zulai ce ta hango shadow tace "Waye tsaye nan, ko Bibalo ce" Hansai tace "Bibalo ai sai karfe sha biyu kila, wani shegen ne ya tsaya min bakin kofa yana min la6e?" Jiddah ta runtse ido ta karasa shiga tsakar gidan, duk suka tsaya kallonta don akwai hasken wata sosai tsakar gidan, Hansai ta ajiye maficin hannunta tana kallonta daga sama har kasa tace "Waye wannan?" Da kyar Jiddah tace "Ni ce Baabarmu" Zulai ta mike a gigice tana sake gyara daurin zanin kirjinta tace "Ke wa??" Hansai dai hangame baki tayi tana kallon Jiddah daga sama har kasa, can ita ma ta mike ta nufeta tana sake kare mata kallo kamar taga aljanna, Hawaye ya shiga sauka idon Jiddah ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace "Baabarmu" Hansai ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Toh Alhamdulillahi, yanxu saura in kai ma Badalan kan dutse cikon kudinsa, aiki kam ya ci Alhmdlh... Allah ya maido min ita gida da kafafuwanta" wani shewa Zulai ta saki da karfi tana gode ma Allah ita ma, Jiddah dai sai kallonsu take, Hansai na sharban majina tace "Tashi mu shiga ciki, tashi" Jiddah tayi karfin halin cewa "Ba ni kadai ba ce Baabarmu" Hansai ta kalli soro da sauri tace "Ke da uban waye??" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Ni da shi ne" Dai dai nan Abuturrab ya shigo cikin compound din don gaba daya hankalinsa ya ki nutsuwa shigan Jiddah gidan ita kadai, Hansai taji mugun faduwan gaba ganinsa tace "Ya xaka afko ma mutane gida haka kanka tsaye, kai waye??" Yana kallon Jiddah yace "Idan kun